Yawan yin fitsari alamace da kada kayi wasa da ita

Feb 13, 2025 - 22:21
 0
Yawan yin fitsari alamace da kada kayi wasa da ita

Yawan yin fitsari,alamace da kada kayi wasa da ita

Yawan fitsari alamane na cututtuka dayawa musamman na mafitsara.

Mutun mai lafiya bayayin fitsari sama da sau 6-8 a rana.idan yawuce haka,ko mutun yana tashi sama sau 3 da daddare toh yazama matsala Kuma alamane na rashin lafiya

Yawan Shan ruwa,nescafe ko barasa kan janyo wannan matsala,Kuma hakan bazai zamanto abun damuwa ba,Shan ruwa abune mai kyau ga lafiyarka da jikinka,saidai giya da nescafe Wanda Basu da wani amfani ga lafiya.

Daga cikin abubuwan dake kawo Yawan fitsari sune:

1.Sanyin mafitsara

sanyine dake shafar mafitsara,alokacin daka kamu da wannan sanyi zaka runka fitsari ne sosai ba dare ba Rana, wani sa'in zakanajin zafi lokacin fitsari ko ganin jini acikin fitsarin.

2.Ciwon siga:

ciwon siga na dagacikin cututtukan dake janyo yawan fitsari,mutun na kamuwa da wannan ciwo ne alokacin da siga acikin jikinsa ta hau hawa sosai.bayan yawan fitsari mutun kan fuskanci Jin kishirwa sosai,yawan shan ruwa da rama.ciwon siga nada matukar illa ga jiki,Yana janyo ciwon zuciya,shanyewar barin jiki, cututtuka na magudanar jini,makanta da dai sauransu

3.Juna biyu

yawan fitsari nadaga cikin alamomin juna biyu a mata.Alokacin da kikayi batan wata sannan Kuma kina yawan fitsari toh kifara tunanin ciki

4.Ciwon BPH

 kowanne da na miji yana da 'prostrate' acijikinsa wanda yake taimakawa wajen samar wa "sperm cells" sinadaran da suke bukata domin yin aikinsu.

alokacin da shi prostate yafara kumbura,mutun kan fuskanci wannan matsala ta yawan yin fitsari.Amafi yawancin mutane shi wannan prostrate din nafara kumburane alokacin da mutun yawuce shekaru 40.Abubuwa dayawa kan janyo shi Wanda zamuyi bayaninsu a wani rubutun namu.

5.prostatitis

Prostatitis sanyi ne na shi prostrate,yakanzo da zafin fitsari,ciwon dubura bayan yawan fitsari

6.Ciwon shanyewar barin jiki

Ciwon shanyewar barin jiki nadaga cikin abubuwan dake kawo Yawan fitsari,a masu wannan ciwo marar su da duburar su kan saki sukasa rike fitsari ko kashi,Wanda hakan zaisa fitsari ko kashi yarunka fitowa dakansa.

7.Daukewar al'ada ta manyanta

Alokacin da mace tawuce shekaru 50,zata iya fuskantar wannan matsala ta yawan fitsari, watoh alokacin da al'adar ta ta manyanta ta dauke

8.Fibroid

Fibroid ko tsiro acikin mahaifa nadaga cikin abubuwan dake iya kawo Yawan fitsari,yakanzo da azababban ciwon mara da zubar jini sosai.

9.kansar prostrate 

Kansar prostate daji ne da prostrate,yakan kama mutun alokacin dayakainahekaru samanda 70,daga cikin alamominsa shine yawan fitsari,yawan Jin matsin fitsari,rashin iya rike fitsari,ciwon baya da dai sauransu.

10.Kansar mara

Kansar mara ko daji na mara daga cikin abubuwan dake kawo Yawan fitsari,mutanen dasukafi kamuwa da wannan matsalar sune masu aiki a kampaninnika na kemicals,ko Wanda suke yawan samun sanyi na fitsara.

13.Magunguna

Shan magunguna irinsu magungunan hawan jini kan janyo wannan matsala ta yawan fitsari

Meyakamata mutun yayi

Idan kana fama da wannan matsala yanada kyau kaje asibiti a gano meke kawo maka wannan matsala da wuri domin magance ta,rashin magance wannan matsala na iya janyo wa mutun wadansu cututtuka daban Wanda maganinsu nada matukar wahala(misali sanyin fitsari na janyo ciwon Koda)

Likita zai iya baka wadannan gwaje gwajen:

  • 1.Gwajin siga
  • 2.Gwajin mafitsara
  • 3.Gwajin ciki 
  • 4.Hotan ciki

Magani yadanganta da abunda yake kawoshi Kuma asibiti ake bayarwa bayan likita yamaka tamboyi da gwaje gwaje 

DR. RABIU RABIU I'm DR. RABIU RABIU, a dedicated and passionate healthcare professional with a strong background in community health. As a licensed practitioner and registered with the Community Health Practitioners Board of Nigeria, my mission is to promote wellness and provide quality care to individuals and communities.