Cutar Yawan fargaba da Tsoro

Cutar Yawan fargaba da Tsoro
Cutace dake sa mutun yawan fargaba akan abun da zai faru anan gaba.Mutun yakan tsinci kansa acikin matsanancin zullumi da fargaba.
A kalla 40% na masu ganin likitan kwakwalwa suna dauke da cutar. Bincike ya nuna a kalla 50% na yan shekara 11 suna iya samunta wanda 80% na masu shekara 20 zuwa sama suna iya kamuwa da ita.
Anfi ganin wannnan cuta a mata akan maza.
Abun dake kawo ta
Babu takamaimai abinda yake kawo ta sai dai tana sababai wanda suka hada da:
- Takurarriyar yarinta
- Karancin arziki
- Samun me irin cutar a dangi
Ana samun wannan matsalar ne alokacin da sinadaran kwakwalwa irinsu norepinephrine,serotonine,gaba,glutamate suka samu matsala.matsaloli a caudate nucleus,amygdala,da hippocampus kan janyo wannan matsala.
Ire Iren wannan ciwon
1.faduwar gaba.
wannan Yana zuwa acikin kankanin lokaci alokacin da mutum yana cikin bacin rai ko ma yana cikin kwanciyar hankali wani sa'in,mutun zai fuskanci alamomi kamar haka:
- bugun zuciya da karfi
- yawan gumi
- bari da kakkarwa
- ciwon kirji ko shakewa
- ciwon ciki da amai
- jin jiri
- jin kamar
- jin kamar komai ba gaske bane ko jin kamar mutun ba ajikinsa yakeba.
- tsoron mutuwa.
2.Fargaba alokacin da mutun ya shiga taron jama'a.
Mutanen da ke fama da wannan nau'in ciwo na fargaba ne tsoron shiga taron jama'a.
Aduk lokacin da mutun yashiga jamaa yakan rasa samun sukuni da nutsuwa,hakan kansa mutun kin shiga cikin jama'a.
3.fargaba na abubuwan dake muhalli.
wannan yana da alaka da tsananin fargaba ga wasu abubuwa da suke kusa da mutum a muhalli wanda yakan iya ganin su lokaci bayan lokaci.wadannan abubuwan sun hada da dabbobi,jini da sauransu.Mutanen dake fama da wannan nau'in sukan shiga zulummi alokacin da suka ga daya daga cikin wadannan abubuwan.
misali matsanancin tsoro alokacin da mutun yaga kadangare,miciji ko yayin da mutun yahau gada ko bene.
Alamomin sa sun kunshi;
- matsanancin tsoro alokacin da mutun yaga wani abu.
- shiga cikin zullumi ta yadda wani sa'in mutun yarasa dailin haka
- tsoron yakan hanashi gudanar da alamuran rayuwarsa.
4.fargaba da Damuwa sabida abinda mutane zasuce:
Mutun yakan shiga damuwa da fargaba sabida abunda mutane zasu fada idan ya aikata wani abu.wannan zaisa mutum yakiyin abin saboda kar ya jamasa kunya(misali tsoron yin magana a bainar jama'a)
5.Fargaba da tsoro akan duk wasu alamura na rayuwa.
mutanen dake fama da wannnan nau'in kan shiga cikin zullumi akan kusan komai na rayuwarsu kama daga aiki,auratayya,iyali,lafiya da sauransu.
Me yakamata mutun yayi?
Idan kana fama da wannan matsala,kasani cewa ba Kai kadai bane Kuma ana maganin ta a asibiti.
Akwai magunguna na tsoro da Wanda zasu cire maka damuwa da likita zai baka bayan ya tabbatar kana dauke da Wannan ciwo na fargaba.