YADDA ZAKA GANE KO KANA DA SANYIN MAFITSARA CIKIN SAUKI
Mutane dayawa suna suffering na cututtuka daban daban, amma kuma suna treating dinsu da wasu magungunan na daban, a wannan rubutun munyi muku cikakken bayanin yadda zakayi diagnosis idan kana fama da sanyin mafitsara da kuma matakin da yakamata ka dauka

Sanyin mafitsara sanyi ne dake shafar mafitsara.kwayoyin cuta na bacteria ne ke Kawo wannan cuta.
A hakikanin gaskia wannan cuta anfi samunta a mata da Mutanen da mafitsarar su ta Toshe.
,Yin amfani da robar fitsari ( catheter ),wanke wajen Kashi kafin na fitsari,Saduwa da mutane daban daban duk Kan iya janyo wannan ciwo.
Hakazalikaa ana yawan samun wannan ciwon a matan da al'adar su tadauke,mutanen dake da Matsalar mafitsara tun lokacin haihuwa ( congenital ) da Wadanda ke fama da cututtuka masu karya garkuwar jiki Kamar ciwon kanjamau,siga,tarin fuka da yawan amfani da magunguna Kamar irinsu antibiotics.
YADDA ZAKA GANE KO KANA DASHI:
Idan har kana da wadannan Alamomin toh kana wannan cuta:
- 1.Yawan fita fitsari musamman da daddare(tashi sama da sau biyu acikin dare)
- 2.Jin Zafi yayin fitsari
- 3.Rashin iya rike fitsari idan ya matseka
- 4.Ganin jini a cikin fitsari
- 5.Ciwon ciki ko mara
- 6.Amai da tashin zuciya
- 7.Zazzabi
- 8.Ciwon kugu da baya da sauransu.
IllOLLIN DA SANYIN MAFITSARA ZAI IYA JANYO MAKA
- 1. Ciwon koda : Ciwon Koda nadaga cikin manyan matsalolin da sanyin mafitsara ke kawowa musamman Wanda baisamu isasshen kulawaba.
- Yana da kyau idan anga wadannan alamomin ayi gaggawar neman magani.
- 2. Rubewar wani bangare na koda
- 3.Duwatsun Koda
- 4.karancin ruwa da jini a jiki
- 5.Zazzabi mara tafiya
Da zarar kaji alamomin cutar, a tuntubi likita
MAGANI
Maganin sanyin mafitsara a asibiti akeyinsa.likita zaibaka gwaje gwaje Wanda zasu tàimaka wajen magance wannan matsala cikin sauki kamar haka:
- 1.Gwajin fitsari na mcs
- 2.Gwajin fitsari na urinalysis
- 3.FBC
- 4.E/U/CR
Likita zai Dora ka akan magunguna na tsawon sati biyu.
Shawarwari dazasu tàimaka maka
- 1. Yawan shan ruwa akalla Lita 2 ko sama da haka arana
- 2. Yin bawali kafin kwanciya ko da za rar an sadu da iyali
- 3. Tsaftar muhalli ( musamman bandaki )
- 4. Ka da mutum ya na rike Kaashi ko fitsari cikin mara, da zarar anji fitsari a je a yi
- 5.Wanke wajen fitsari kafin wajen Kaashi