Yara Meke kawo Nimoniya a yara?

Meke kawo Nimoniya a yara?
Nimoniya cutace datake shafar Huhu. Acikin huhu akwai wasu 'yan jakka da ake kira dasuna "alveoli"inda nanne iska ke zuwa alokacin da muke numfashi. Wadannan alveoli, suna cikene da iska. Alokacin da Kwayar cuta tashiga cikin huhun,takan janyo kumburin wadannan "alveoli" din tare da rage yawan iskar dake ciki, hakanne yakesa yaro daya kamuda nimoniyar yariqa jin zafi yayinda yake nunfashi yakuma hanashi shaqar iskar oxygen ishashshe.
Kungiyar lafiya ta duniya wato WHO, ta bayyana Nimoniya na yara kamar haka " Wata matsalace ga lafiya, wacce take tafeda tari ko nunfashi dakyar-dakyar. Ana iya ganetane ta hanyar bincikar numfashin yaro ko yananan dai-dai ko akasin hakan yayinda aka duba kasan kirjin yaron ko yana fadawa batareda yaron yafice daga hayyacin saba.
Meke kawo wannan ciwo?
Kwayoyin cuta irinsu bakteriya, bairos, fungai ( bacteria, virus, and fungi) sune ke kawo wannan cuta alokacin dasuka shiga cikin Huhu.
Atakaice dai yayinda, daya daga cikin kwayoyin cutar yasamu damar isa zuwa Huhu shike haddasa ta. Wanda sukafi kawowa sune Kwayar cutar bacteria maisuna striptokokkus nimoniya ( streptococcus pneumonia) dakuma Hemopilos influanza taib bi ( Hemophilus influenza type b. [Hib])
Yadda cutar ke yaduwa
Nimoniya tana yaduwa ta hanyoyi dadama:
- Kwayar cutar bairos da bakteriya wadanda ake yawan samunsu a hancin yara ko makogwaro sukan isa sushafi Huhun yaron yayinda yaro ya shaqesu
- Hakazalika cutar tana yaduwa tahanyar zubarda kaki(majina) lokacin yin tari ko attishawa.
- Sanannan takan yadu ta jini musamman lokacin haihuwa.
- Ta kan yadu ta hayaqin da yake zagayawa cikin gidaje yayin dafa abinci kodai kona wani abu
- Takan yadu a inda babu ishashshen iska misali a daki dan karami ko marasa winduna , yana karawa yaro barazanar kamuwa da nimoniya.Haka zalika cikin taron al'umma.
Alamomin nimoniya a yara
- Tari
- Nunfashi dasauri-dasauri ko ahankali-ahankali ko Nunfashi dakyar-dakyar
- Wani sauti daga kirji kamar ana sace balonbalon
- Zazza6i
- Ciwon makogwaro
- Ciwon kai
- Rashin son cin abinci
Dazaran wadannan alamomin sun bayyana ayi gaggawar kai yaro asibiti.
Sauda yawa yara suna rasa ransu akan Nimoniya ne, saboda masu kula dasu ko iyayensu basu iya gane alamomintaba.
Hanyoyin kariya daga Nimoniya
Akwai hanyoyi dadama dazamu kare kanmu da yaranmu daga wannan cutar.
Amma ga muhimman kamar haka:
• Rigakafi
Rigakafi hanyace ingantacciya ta kare yara daga cutar NIMONIYA. Anayin wannan Rigakafin a asibiti bayan sati hudu da haihuwar yara dakuma bayan sati shida sannan kuma bayan sati goma. Yanada kyau yara susami wadannan Rigakafin.
• Ishashshun abinci masu qara lafiya:
Ishashshen abinci masu qara lafiya wa yara, yana farawane daga shayar dasu ruwan nono zalla na tsawon wata shida ( exclusive breastfeeding for the first six months). Yin hakan yana karawa yara karfin garkuwar jiki dakuma kariya daga nimoniya kokuma yahana cutar tsawaita ajikin yara.
• Tsabtar muhalli:
Tsabtar muhalli yana taimakawa wajen bada kariya daga cututtuka dayawa, saboda kana kokarin fitar da wasu kayan dattine dakan iya 6oye kwayoyin cuta.
Domin nimoniya yadace makaucewa taron al'umma misali kauracewa tara yara fiye da hudu ko biyar a daki daya ko wajen biki kodai duk wani wurin taronda nunfashin mutane yana gaurayuwa dana juna, ta yadda dazaran wani yayi tari ko attishawa akwai barazanar kamuwa da cutar. Sannan kuma da kauracewa duk wani mulallinda Hayaqi yake.
Saikuma akara da wadannan hanyoyin
- Wanke hannaye da ruwa da sabulu
- Sanya takunkumi
- Motsa jiki
- Ziyartar asibiti akan lokaci
Mungode.