Illolin dake tattare da yawan cin gasasshen nama

Nama na daga cikin nauin abinci mai gina jiki da Kara lafiya. Yana daga cikin abinci dake dauke da sinadarin protein mai yawa.
Yanada kyau inzaka ci shi ka dafa shi.
Cin soyayye ko gasasshe bashi da wani amfani ga lafiya.
Gasasshen nama na dauke da sinadarai masu cutarwa waɗanda zasu iya ƙara haɗarin kamuwa da cututtukan daji watoh kansa.
Bincike na likitanci yanuna cewa mutanen dake yawan cin abincin da aka gasa ko aka Sarrafa shi da hayaki na iya janyo cututtuka dayawa.
Illolin shin gasasshen mana
Daga cikin illolinsa akwai cututtuka na daji,ciwon siga,shanyewar barin jiki,olsa da dai sauransu.
- Ciwon kansar hanji da ciki : Yawan cin gasasshen nama nada alaka ga saurin kamuwa da kansar hanji musamman babban hanji da ciki abunda Bincike ya nuna. Kansar ciki nadaga cikin cututtukan daji dasukafi kashe mutane a duniya.
- Ciwon olsa : Daga cikin abubuwan da Ke kawo olsa shine cin abunda aka fada ko aka Babb aka shi da hayaki. Hayaki nadaga cikin abubuwan dake yawan samar da acid acikin ciki. Idan kana da olsa yawan cin Abu mai hayaki na iya tada maka da ita.
- Shanyewar barin jiki da ciwon siga: Yawan cin gasasshen Nama na iya janyo wadannan cututtuka na shanyewar barin jiki da ciwon siga da wasu cututtuka ma dayawa.
Yawan Cin Jan nama kadai shima nada nasa illolin,masana sundangantashi da cututtuka na zuciya,shanyewar barin jiki,kansar ‘prostrate’ a maza da dai sauransu.
Yakamata mu runka lura da abubuwan damukeci domin samun zama da jikin mu lafiya