Alamomin cututtika na mafitsara

Jan 16, 2025 - 20:30
 2
Alamomin cututtika na mafitsara

ALAMOMIN CUTUTTUKA NA MAFITSARA 

3.ZAFIN FITSARI

Zafin fitsari ko Jin ciwo lokacin yin fitsari alamace dake nuni da cututtuka dayawa musamman ma na mafitsara,mahaifa(a mata) da Koda.

Meke kawoshi

1.Sanyin mafitsara

sanyin mafitsara sanyi ne dake shafar mafitsararka,idan kana dashi,toh zaka runka yawan fita fitsari akoda yaushe musamman da daddare(sau biyu zuwa uku).alamominsa sun hada da:

 Yawan fitsari

Tashi da daddare yin fitsari(tashi cikin dare sama da sau biyu)

Jin zafi lokacin yin fitsari

Ganin jini acikin fitsari

Ciwon gefen ciki bayan ciwon mara

mutun na kamuwa da sanyin mafitsara alokacin da aka samu kumburi ko kwayar cuta tashiga cikin mafitsara.

mata sunfi saurin kamuwa da wannan ciwo akan maza.

Hakazalika masu ciki da Wanda al'adar su ta dauke suna da saurin yiwuwar kamuwa da wannan ciwo

2.Sanyin da ake dauka ta hanyar saduwa:

Zaka iya Jin zafi alokacin dakake fitsari idan kana da sanyi wanda ake dauka ta hanyar saduwa.

Daga cikin sanyin da ake dauka ta hanyar saduwa dake kawo zafin fitsari sunkunshi herpes, gonorrhea, da Chlamydia.

Alamomin sa sune:

Jin zafi lokacin saduwa musamman amata

Fitar ruwa ta gaba

Yawan fitsari

Ganin jini acikin fitsari

Kurajen gaba

3.Sanyin prostrate(Prostatitis):

Daga cikin cututtukan dake kawo zafin fitsari akwai prostititis, wato kumburin prostrate,ana samun prostrate ne a maza kadai.Amfanin 'prostate' ajiki shine karawa "sperm cells(maniyyi)" sinadaran dasuke bukata,wanda rashin hakan kan iya janyo "Rashin haihuwa a maza".

Alamomin sa sune:

Fitsarin jini

Ganin jini a cikin maniyyi na maza

Jin zafi lokacin saduwa a Maza

4.Sanyin mara(cystitis):

Cikin abubuwan dake kawo zafin fitsari shine kumburin mara(bladder). 

Alamomin kumburi ko sanyin mara sun kunshi :

yawan fita fitsari  

ciwon mara musamman idan antaba marar da hannu.

Mutun na kamuwa da wannan ciwon ne alokacin da Kwayar cuta tashiga cikin mara.

5.Sanyin tantanin mafitsara(Urethritis):

urethritis yana nufin sanyi ko kumburin makwaroron fitsari, urethritis na janyo zafin fitsari da yawan Jin San fita yin fitsari.

Mutun na kamuwa da wannan sanyin ne alokacin da Kwayar cuta tashiga cikin tantanin mafitsara

6.Sanyin Epididymis:

Jin zafi lokacin fitsari zai iya kasancewa sabida wannan ciwo, wanda sanyi ne dake shafar mazaunin "sperm cells(maniyyi) acikin marena(epididymitis) yake kawoshi.

Alamomin sa sune:

Ciwon marena

Jin zafi lokacin saduwa a maza

7.Sanyin mahaifa:

sanyin mahaifa watoh "pid" na shafar duk wani bangare na mahaifa tundaga kan bakin mahaifa,cikin mahaifa,hannun mahaifa da Kwan mahaifa.

Alamominsa sunkunshi:

ciwon mara

Kaikayin gaba

Fitar da ruwa ta gaba

jin zafi lokacin saduwa

zafin fitsari 

8.Toshewar mafitsara (Obstructive uropathy):

Wannan ciwo ne da yake faruwa alokacin da aka samu wani abu ya toshe magudanar fitsari acikin mafitsara . abubuwan dake kawo wannan matsala suna da yawa.

Alamomin sa sunkunshi:

Rashin iya yin fitsari

Yawan fita fitsari

Rashin iya rike fitsari

Kumburin kafa da fuska

9.Duwatsun koda:

Mutun kan iya fuskantar wahalar yin fitsari idan yana da duwatsun koda.duwatsun Koda wadansu duwatsu ne dake fitowa a Koda daga daskarewar datti da gishiri dake cikin Koda.

Alamomin sa sun kunshi:

Yawan fitsari

Azababban ciwon mara

Ciwo a gefen mara Wanda yake zuwa har cinya

Rashin iyayin fitsari

10.Magunguna:

Shan Magunguna kamar su estrogen, magungunan ciwon damuwa, magunguna na ciwon jiki da dai sauransu kan iya janyo zafin fitsari.

YAUSHE YAKAMATA KAGA LIKITA?

1.idan zafin fitsarin yaki tafiya 

2.idan mace nadauke da juna biyu 

3.Idan zafin fitsarin yazo tare da zazzabi 

4.Idan yazo tare da fitar ruwa daga al'aura 

5.Idan fitsarin ya canza kala ya koma ja ko baki ko Kuma fitsarin na wari. 

6.Idan zafin fitsarin yazo tare da ciwon ciki 

7.Idan dawatsu sun fito acikin fitsarin 

MAGANIN ZAFIN FITSARI 

Abu mafi muhimmanci shine afara sanin me ke kawomaka wannan matsala,idan har angano inda matslar take toh komai zaizo da sauki.

Za a iya baka wadannan gwaje gwajen a asibiti domin gano meke kawo wannan matsala kamar haka:

1.Test din fitsari 

2.Test din jini 

3.Hoton mafitsara da hoton mara

4.Test din Koda 

Likita zai iya baka "magungunan sanyi"(antibiotics) sabida sanyi,sannan zai iya baka magunguna daza su rage maka radadin ciwon mara. 

SHAWARWARI

1 Yawan Shan ruwa na tàimakawa kwarai wajen rage zafin.

2.Rage cin abinci masu tsami sosai,Kofi da barasa 

3.Amfani da matakan kariya kamar "condom" lokacin saduwa 

4.Rage amfani da sabulu,Omo ko man shafawa masu kamshi sosai .

DR. RABIU RABIU I'm DR. RABIU RABIU, a dedicated and passionate healthcare professional with a strong background in community health. As a licensed practitioner and registered with the Community Health Practitioners Board of Nigeria, my mission is to promote wellness and provide quality care to individuals and communities.