Domin gudanar da aikinsa na yau da kullun yadda yakamata,jiki na bukatar wasu sinadarai daga abinci dazaiyi amfani dasu

Alokacin da baya samun wadannan sinadaran yakan fuskanci wasu matsaloli daka iya janyo wata cuta ko ciwo kamar:
- 1.Rashin girma da saurin tsufa
- 2.zubar gashi da saurin furfura
- 3.karancin jini ajiki
- 4.Raguwar Gani
- 5.Raguwar kaifin basira
- 6.Matsaloli na fata
- 7.Yawan kasala da ciwon jiki da dai sauransu
Abincin dazasu taimaka
Cin abinci kamar wake,waken suya,shinkafa,dankali,doya da dai sauransu,kwai,nama
Kayan Miya kamar timatir,kubewa,kabewa,citta,tafarnuwa,kuka da dai sauransu
Mai kamar man ja,man zaitun, man kwakwa.
Kayan itace kamar lemon tsaki,cocumber,Karas,ayaba,abarba,mangwaro,dabino da dai sauransu.
Wadannan abubuwa duk zaa iya samu cikin sauki