Gurbacewar ciki bayan cin abinci(food poisoning)

Gurbacewar ciki bayan cin abinci(food poisoning)
Gurbacewar ciki na faruwa sakamakon cin abinci Wanda ke Dauke da kwayoyin chuta ko Kuma cin abinda Wanda ke Dauke da sinadarai Wanda kwayoyin chuta suka samar. Gurbacewar ciki Abu ne Wanda ke illar ta da mutane musamman ma yara, masu ciki, da tsofaffin, wasu lokutan gurbacewar ciki na iya Barazana ga rayuwar mutum.
Alamomin ta sun HaDa da;
- Gudawa
- amai
- ciwon ciki
- zaxxabi.
Akwai rashin lafiyoyi da dama wanda ke da irin wannan alamomin. yadda ake Gane ce wannan alamomin sun faru ne sakamakon cin abinci shine.
Faruwar wannan alamomi lokaci kadan bayan Gama cin abinci.
Wasu Wanda suka ci wannan abincin suma susami kalar wannan alamomin.
Shidai abinci Wanda ke Dauke da kwayoyin chuta ba Gane shi ake ta ido ko DanDano ba Dan Haka Abu Mai mahimmanci shi ne a Guji abubuwa Wanda ka iya kawo kwayan cutan cikin abinci.
Yadda zaa kare kai
- Ayi kokari wajen wanke duk wani abu da aka San za ai amfani dashi gun cin abincin kamar hannu, kwanuka da sauransu.
- Duk abunda za aci atabbatar ya Dahu sosai.
- Duk abincin da aka San za aDau lokaci kafin acishi ayi kokari wajen sashi cikin fridge Wanda aka San Yana aiki
- Akwai wani abu da alikitance muke chema cross contamination Wanda ke nufin misali ayi amfani da wuka wajen yanka Danyar Doya Sannan ayi amfani da wannan wukar wajen yanka doyar bayan ta Dahu, ana so ya zamto duk abunda akai amfani da shi aDanye bashi za ai amfani dashi ba bayan abun ya Dawu.
Abunda mutum zai yi inya kamu ko wani nashi ya kamu shine, babban abunda ke illatar da mutane shine wannan ruwan da mutum ke rasa ajikin sa sakamakon amai da gudawan, don haka abun da yafi mahimmanci shine duk amai ko Gudawa Guda Daya in mutum yayi ayi kokari ahaDamasa ruwan gishiri da siga abashi yasha yadda zai koshi, Haka za atayi har akai shi zuwa ga asibiti. Daya wa mutane kafin akawo su asibiti sun galabaita wasu ma sun Fi ta daga hayyacin su sakamakon ruwan da suke rasa wa Kuma ba amayr musu dashi ta hanyar ruwan gishiri da sigan.