Irin ciwon jikin da be kamata ayi wasa dasu ba

Jan 16, 2025 - 20:36
 0
Irin ciwon jikin da be kamata ayi wasa dasu ba

IRIN CIWON JIKIN DA BAI KAMATA KAYI WASA DASU BA 

Ciwon jiki alamane na ciwuka da yawa,wani sa'in ma har cututtukan da za su iya yin ajalin mutun in ba a dau kwakkwaran mataki da wuri ba.

Ire Iren wadannan ciwukan jikin da Bai kamata kayi wasa da su ba sun kunshi:

✅1.Ciwon kirji mai yawo.

Irin wannan ciwon kirjin alamane na cututtuka na zuciya masu hatsari (kamar su ischemic heart diseases).

Alokacin da kaji kamar ana matse maka kirji ko kamar an Dora maka Abu mai nauyi akan kirjin,sannan bai tsaya iya Nan ba,Yana zuwa har gefen kafadunka da wuya,toh kayi kokarin daukan kwakkwaran mataki akanshi ta hanyar ziyartar likita,likitan ma kwararre.

✅2.Ciwon Kai mai farawa lokaci daya.

Alokacin da kaji kafara ciwon Kai lokaci guda mai matsanancin ciwo da radadi toh kasan cewa wannan alamane dake nuni da fashewar magudanar jini acikin kanka.

Rashin daukan mataki da wuri zai iya sa Taruwar jini acikin kwakwalwa da mutuwa lokaci daya.

✅3.Ciwon hakori.

Alokacin dakake fama da matsanan cin ciwon hakori,Yana da kyau da kaje kaga likitan hakori watoh"dentist" a asibiti domin Neman magani.wasa da irin wannan ciwo ka iya sa ka kamu da ciwon zuciya agaba.

✅4.Mata masu Jin zafi ko ciwo lokacin saduwa.

Wannan alamane na Kansar bakin mahaifa

Musamman inkina fitar da jini bayan saduwar.

✅5.Azababban Ciwon ciki a dan kankanin lokaci.

Wannan alamane na cututtuka masu hadari kamar fashewar hanji,Duwatsun Koda,fashewar appendix,fashewar mahaifa da dai sauransu.rashin daukar mataki da wuri zai iya sa mutun ya rasa rayuwarsa.

✅6.Ciwon kafafu.

Ciwon kafafu musamman tare da kumburi alamane na cutar magudanar jini watoh"DVT" wannan ciwo na da matukar hatsari.

Alokacin dakake fama da ciwon kafa bayan kayi doguwar tafiya,ko bayan anyi maka tiyata,ko bayan kayi doguwar jinya,sannan a mata Kuma inkina Shan maganin tsarin iyali toh afara tunanin wannan ciwo.

DR. RABIU RABIU I'm DR. RABIU RABIU, a dedicated and passionate healthcare professional with a strong background in community health. As a licensed practitioner and registered with the Community Health Practitioners Board of Nigeria, my mission is to promote wellness and provide quality care to individuals and communities.