Alamomi dake nuna jikinka na fuskantar karancin sinadarai

Alamomi dake nuna jikinka na fuskantar karancin sinadarai
Domin gudanar da aikinsa na yau da kullun yadda yakamata cikin lafiya,jiki na bukatar wasu sinadarai daga abinci dazai yi amfani dasu wajen gudanar da wadannan ayyukan.
Alokacin da baya samun wadannan sinadaran yakan fuskanci wasu matsaloli daka iya janyo wata cuta ko ciwo.
Daga cikin alamomin karancin sinadarai sunkunshi:
1.Alamomi a Gashin kai.
karancin sinadarai kamar su vitamin B12,B complex na iya sa tsistsinkewa da zubar gashi,furfura da wuri da dai wasu matsaloli na gashi.
2.Alamomi a ido
Idan idonka na yawan yin ja,ciwo,kwantsa,ko ganinka na raguwa,toh akwai yiwuwar kana fuskantar karancin sinadarai irin su vitamin A.akwai cututtuka na ido dayawa daka iya kawo maka wadannan alamomin,Dan haka ba karancin sinadarai ne kadai mai Saka wadannan abubuwa ba.
Cin Karas akai akai,kabewa,timatir,kwai,kifi,dankalin turawa,hanta da dai sauransu zai iya magance maka wannan matsala.
3.Alamomi A baki
gyanbon Baki da tsagewar Baki alamomune dake nuna cewa jikinka na fuskantar karancin sinadarai.
Gyanbo ko kurarrajin Baki na iya yiwuwa kana fuskantar karancin sinadarai kamar su vitamin c.
Abubuwan dazasu iya kawo maka wannan matsala bayan karancin sinadarai sunkunshi:Ciwon candidiasis,ciwon siga,ciwon hiv,yawan Shan magunguna na Sha ka fashe.
Zaka iya magance wannan matsala ta hanyar Shan kayan itace masu dauke da sinadarin vitamin c kamar lemon Zaki ko na tsami
4.Dashewar fuska.
Karancin sinadarai ajiki kamar su folic acid da vitamin B12 Wanda Ake amfani dasu wajen Samar da kwayoyin halitta na jini ka iyasa fuskanka ta dashe.dashewar fuska alamane na karancin jini ajiki.
5.Yawan kasala da ciwon jiki.
Hakan na iya nuni da cewa kana fuskantar karancin jini da sinadarai kamar su sodium,potassium,chloride da dai sauransu ajiki.
Zaka iya magance wannan matsala ta hanyar cin abubuwa kamar ayaba,kankana,kwai,Madara,nama,waken suya,shinkafa da dai sauransu.
6.Yawan ciwo ko zafi a kashin jiki
Yawan zafin Kashi na iya yiwuwa jikinka na fuskantar karancin sinadarai na calcium.
Zaka iya magance wannan matsalane ta hanyar cin abinci masu dauke da shi sinadarin kamar su Madara,awara,lemon Zaki,wake,wajen suya,kobewa,kwai da dai sauransu.
7.Raguwar kaifin basira
Alokacin dakake fama da karancin sinadarai,basirarka na iya raguwa.
Abincin dazasu tàimaka maka wajen Kara basira sunkunshi:kwai,kifi,kabewa,coffee,kayan Miya,man kwakwa,lemo,dark chocolate da dai sauransu.
8.Matsaloli na fata
Yaushi,bushewa da rashin kyan fata nada alaka da karancin sinadarai ajiki.
Cin abubuwa kamar kifi,kwai,man kwakwa,man zaitun,lemon Zaki,Karas,green tea duk na tàimakawa wajen gyaran fata.
9.Rashin girma
Rashin girma na daga cikin alamomin karancin sinadarai,alokacin dabakasamun isassun sinadarai da zasu Gina maka jiki toh ba makawa jikinka zai zauna inda yake ba cigaba