SIFFOFIN MASU JIN TSORAN ALLAH(005)

005 SIFFOFIN MASU JIN TSORAN ALLAH
*_BASA ROQON KOWA SE ALLAH_*
*_masu jin tsoran Allah_* _Basa roqon kowa sai Allah, ba wani mala’ika makusanci ga Allah, ko wani Annabi mursali, ko wani waliyyi nagartacce, Allah kawai suke roqa, domin Allah yace_
(وَلَا تَدْعُ مِنْ دُونِ اللَّهِ مَا لَا يَنْفَعُكَ وَلَا يَضُرُّكَ فَإِنْ فَعَلْتَ فَإِنَّكَ إِذًا مِنَ الظَّالِمِينَ106) [يونس: 106]
*(Kada ka kirawo wani ba Allah ba, wanda ba zai amfaneka ba, kuma ba zai cutar da kai ba, idan kuwa ka aikata haka, to lallai kai kana cikin azzalumai).*
_*masu jin tsoran Allah* Basa roqan kowa se Allah domin haqiqa yin addu’a shi ne tsananta kwadayi ga Allah Ta’ala wajen neman biyan buqatun duniya da na lahira da yaye baqin ciki da kade sharri, da bala’i na duniya da lahira. Saboda haka agurin Allah kawai suke qasqantar dakai wajen roqon Allah domin Allah yace_
(وَقَالَ رَبُّكُمُ ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ60) [غافر: 60]
*(Kuma Ubangijinka ya ce, ku roqe ni, na amsa muku. Haqiqa wadanda suke girman kai ga barin bautata za su shiga wutar Jahannama suna qasqantattu).*
_*masu jin tsoran Allah* Dukkanin wata matsala idan ta taso Allah kawai suke roqa domin an rawaito daga Abu Huraira (R.A) daga Annabi (ﷺ) ya ce: *“Ku roqi Allah, kuna masu sakankancewa da amsawa, kuma ku sani cewa Allah baya qarbar addu’a daga zuciya gafalalliya mai wasa”.* Tirmizi ne ya rawaito shi._
Daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi, daga Annabi (ﷺ) ya ce, *“Lokacin da bawa ya fi kusa da Ubangijinsa, shi ne lokacin da yake sujjada. Don haka, ku yawaita addu’a a cikinta.”* Muslim ne ya rawaito shi.
_Kuma an karbo daga Ibn Abbas (R.A.), ya ce: MAnzon Allah (ﷺ) ya ce: *“Lalle haqiqa ni an hana ni in karanta Alqur’ani a cikin ruku’u ko sujjada. Amma ruku’u to ku girmama Ubanjigi a cikinsa. Ita kuma sujjada, to ku yi matuqar qoqari wajen addu’a a cikinta, lallai ya dace amsa muku.”* Muslim ne ya rawaito shi._
Daga ciki: akwai tsakanin kiran sallah da iqama. Domin an rawaito daga Anas (R.A) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: *“Ba a mayar da addu’a a tsakanin kiran sallah da iqama.”* Tirmizi ne ya fitar da shi, kuma ya ce, hadisi ne kyakkyawa ingantacce.
_Manzon Allah, tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ce: “Ubangijinmu kan sauka (irin saukar da ta dace da shi), kowane dare zuwa saman duniya yayin da sulusin dare na qarshe ya rage, sai ya ce *“Wane ne zai kira ni na amsa masa? Wane ne zai nemi gafara ta na gafarta masa?”.*_
_Daga ciki: akwai qarshen sa'a bayan sallar La’asar ranar juma’a. An rawaito daga Abi Huraira (R.A) cewa Manzon Allah (ﷺ) ya ambaci ranar Juma’a sai ya ce *“A cikinta akwai wata sa'a babu wani bawa Musulmi da zai dace da ita a tsaye yana sallah, yana roqon Allah wani abu face ya ba shi. Ya yi nuni da hannunsa yana qarantata.”* Bukhtari da Muslim ne suka rawaito shi._
_Yana daga guraren amsa addu’a da shari’a ta zo da su: *Daren Lailatul Qadari, da ranar Arafa, da gurin Hajarul Aswad, da yayin saukar ruwan sama, da bayan sallolin farilla, da lokacin shan ruwa a yayin azumi.*_
Yaku bayin Allah kuji tsoran Allah kada ku bari zuciyarku ta mutu imaninku yayi rauni saboda kowa ya dogara ga Allah ya nema daga falalar.
Ina roqon Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai iko ne a bisa kowane abu. Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji na Alqur’ani ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin qai
*الله تعالى أعلم*
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ اليه
Join our telegram channel:
https://t.me/paymentchannel013