SIFFOFIN MASU JIN TSORAN ALLAH(001)

SIFFOFIN MASU JIN TSORAN ALLAH {1}
*BASA YIN SHIRKA*????
_*masu jin tsoran* basa yin shirka basa hada Allah da wani wajen bauta domin Shirka itace mafi girman abinda Allah ya haramta a bayan kasa, Saboda Hadisin da Abi Bakrata ya ruwaito Yace manzon Allah (SAW) yace *"Shin bana baku labarin mafi girman manyan laifuka ba, har sau uku Se Sahabbai sukace bamu ya manzan Allah , se manzan Allah Yace: Shine Yin Shirka da Allah…"*_
*masu jin tsoran Allah* basa shirka ga Allah domin kowani laifi Allah ze iya gafartawa me shi in banda Shirka domin ita se anyi mata tuba kebantatta Allah madaukakin Sarki Yace:
إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَن يُشْرَكَ بِهِۦ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُ
*( Lallai Allah madaukakin Sarki baya gafartawa ga wanda yayi Shirka dashi, amma yana yin gafara ga abinda ba Shirka ba ga wanda yaso )*
*masu jin tsoran Allah* basa yin shirka domin manzon Allah (ﷺ) yace, *“Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa.”* Sai aka ce, “Wadanne ne, ya Ma’aikin Allah?” Sai ya ce, *“Hada Allah da wani, da tsafi, da kisan kan da Allah ya haramta, sai da gaskiya, da cin dukiyar maraya, da cin riba, da tserewa daga fagen yaqi, da yin qazafi ga tsararrun mata, gafalallu, muminai.”* [Bukhari da Muslim].
*masu jin tsoran Allah* basa zuwa gurin boka ko matsafi ko dan duba domin Allah madaukakin sarki yace
(وَلَا يُفْلِحُ السَّاحِرُ حَيْثُ أَتَى69) [طه: ٦٩].
*(Kuma mai sihiri ba zai rabauta ba, ko ta ina ya zo).*
Imran ibn Husain ya rawaito manzon Allah(SAW) yace *“Wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi, ba ya tare da mu; ko ya yi bokanci, ko aka yi masa bokanci, ko ya yi tsafi, ko aka yi masa tsafi. Duk wanda ya je wajen boka, ya gaskata shi da abin da yake fada, haqiqa ya kafirta daga abin da aka saukar wa Muhammad.”* [Bazzar ya rawaito shi, da salsala ingantacciyya].
_*masu jin tsoran Allah* sune masu kiyaye dokokin Allah basa yin shirka ga Allah basa zuwa gurin dan duba ko matsafi, basa bautawa kowa se Allah_
Ina roqon Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai iko ne a bisa kowane abu. Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji na Alqur’ani ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin qai
*الله تعالى أعلم*
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_
Join our telegram channel:
https://t.me/paymentchannel013