Olsa ga mai azimi

Mar 11, 2025 - 19:25
 0
Olsa ga mai azimi

Olsa ga mai Azumi.

Manyan Hanyoyin Kaucewa Matsalar Da Olsa wadda Ke Iya Haifar da hana azumi.

1. Amfani da maganin da zai hana wannan sinadarin asid ɗin sauka da yawa balle ma har yaje ya haifar ma mutum da matsala (watau, ya tada mishi da olsa ɗin). Cikin magungunan akwai OMEPRAZOLE, RABEPRAZOLE, ESOMEPRAZOLE. 

In OLSA ɗin mutum mai sa TASHIN ZUCIYA/KO JIN AMAI ne, sai ya samu PERBLOC-DSR ko ESOFAG-D

Wannan magungunan ana shan su ne kafin aci abinci, watau sai mutum yasha KAFIN YACI ABINCIN SAHUR. Ɗaya daga cikin su kawai mutum zai sha.

2. Gujewa abinci ko abun sha masu iya uzzula ma olsa lokacin SAHUR ko BUDA BAKI. Misalin wannan abincin ko abun sha su ne, abinci mai ɗauke da yaji sosai, abin sha mai ɗauke da sinadarin asid irin su lemun tsami da lemu, lifton da neskef (lipton & nescafe), lemun kwalba/roba irin su C0câ-C0lā, sai abubuwan da suka soyu sosai).

3. Yawaita shan ruwa lokacin sahur da buda baki duka.

4. Mutum na iya samun gishirin Andrew (Andrew Liver Salt) ya zuba kulli biyu a cikin kofi yasha bayan ya gama sahur.

Bi'iznillah za ka yi azumin ka lami Lafiya duk da kana da olsa.