NASIHA ZUWA GA MAI AZUMI

ZUWA GA MAI AZUMI
Nasihantarwa
Ya kai bawan Allah mai azumi! Ka daure ya kasance cewa Alƙur'ani yana da kaso mafi tsoka a cikin lokutanka na yinin Ramadana mai albarka, kada ya kasance cewa baka da tsari ko lokacin karanta Alƙur'ani ko yawaita ambaton Allah
-
Kada ka ƙarar da gwala-gwalen lokutanka a shirme da bankaura da hawa social media kana aikin da bashi da muhimmanci, kada ka mayar da hankalinka wajen yin gulma ko tsugudidi da faɗi ba'a tambayeka ba, ka dawo ka rungumi Alƙur'ani mai tsarki
-
Haƙiƙa kuskure ne babba a matsayinka na mai yin azumi amma ace har rana ta fito kuma ta faɗi ba tare da ka karanta Alƙur'ani mai girma ba, lallai ne wannan babbar asara ce
-
Allah ta'ala yasa mu dace Amin Ya Rabb