YAUSHE NE AKE DAURA NIYYAR AZUMI

Feb 28, 2025 - 21:28
 0
YAUSHE NE AKE DAURA NIYYAR AZUMI

YAUSHE AKE DAURA NIYYAR AZUMI???

Ana daukar niyyar Azumine cikin dare kafin fitowar alfijir na biyu,dukkan wanda bai dauki niyyar Azumi ba kafin fitowar alfijir ba,baya da Azumi.

Manzon Allah SAW yana cewa;-

*(Dukkan wanda bai dauki niyyar Azumi ba kafin fitowar alfijir ba,baya da Azumi)*

 @رواه الترمذي (730) 

A lafazin Imam Nisa'i yana cewa:-

*(Dukkan wanda bai dauki niyyar Azumi ba acikin dare to baya da Azumi)*

@صححه الألباني في صحيح الترمذي (583) 

Ma'ana shine:-

*_Dukkan wanda bai dauki niyyar Azumi ba cikin dare ba har alfijir ya fito,to baya da Azumi_*

Niyya Gurbinta shine a zuciya,dan haka mutum zai yi himma da kuduri a zuciyarsa cewa zai azumi gobe wannan shine niyya sannan niyyar tana kara tabbata ne lokacin da ya fara shan sahur,furta niyyar azumi da sauran niyyar ibada yin hakan bidi'ane kuma baya da asali.

Niyya ingantacciya shine mutum ya qudurta a ransa gobe zaiyi Azumi, yin niyyar Azumi bata da wani wahala abune mai sauki ka kudurta a rai cewa zakiyi azumi gobe ba tare da furta komai ba.

ابن تيميةرحمه الله:

Yana cewa:-

*_Dukkan wanda ya san cewa gobe watan Ramadhana ne kuma yana nufin yin Azumi gobe,to yayi niyyar Azumi kenan_*

@مجموع الفتاوى ٢٥/٢١٥ 

        Allah ne mafi sani