BUSHARA DA ZUWAN WATAN RAMADAN

Mar 1, 2025 - 23:08
 0
BUSHARA DA ZUWAN WATAN RAMADAN

BUSHARA DA ZUWAN WATAN RAMADAN:

:

????????????????????????????❓

:

Assalamu alaikum warahmatullah. Wane irin albishir Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yake yiwa al`ummarsa kafin watan Ramadan ya kama?

:

????????????????❗️

:

Wa alaikumus Salam Warahmatallahi Wabarakatuh 

Watan Ramadan wata ne mai girma, Wata ne da aka Saukar Da Alqur'ani A Cikinsa. wata ne mai albarka, Musulmai suna farin ciki da zuwansa. Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) da Sahabbansa sun kasance suna farin ciki da zuwansa, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana yima Sahabbansa bushara da zuwan watan Ramadan.

Daga Abi Huraira (Allah ya ƙara Mashi yadda) yace: "Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance yana yiwa Sahabban shi bushara da zuwan watan Ramadan, yana cewa: Lallai wata mai albarka ya zo maku, Allah ya wajabta maku azumtar shi, a cikin shi ake buɗe ƙofofin Aljanna, ake rufe ƙofofin wuta, ake ɗaure shaiɗanu, a cikin shine wani dare yake wanda yafi wata dubu Alkhairi, Duk wanda aka haramta ma wannan wata Lallai yayi Hasara." Sahihut - Targeeb [1/490]

Al-Hafiz ibn Rajab (Rahimahullah) yace: Wasu daga cikin Malamai suka ce: Wannan hadisi asali ne Babba dake nuni akan cewa mutane suna iya yiwa junansu murna da shigowar Ramadan, ta ya ya mumini ba zai yi bushara da buɗe ƙofofin Aljanna ba? Ta yaya mai aikata zunubi ba zai yi farin ciki da rufe ƙofofin wuta ba? Ta yaya mutum mai hankali ba zai yi bushara da lokacin da an ɗaure shaiɗanu ba?

Dan Haka Musulmi Yana Farinciki Da Gabatowar Watan Radaman,Yana Bushara Da Shi Kuma Yana Fuskantarsa Da Farinciki, Yana Robautarsa Ta Hanyar Tsayuwar Dare, Da Azumtarsa Da Rana, Da Tilawar Alqur'ani, Da Zikiri Domin Cim Ganimarsa.

Wajibine Akan Musulmi Ya Roqi Allah S.W.T Dan Ya Nuna Masa Lokacin Wannan watan, Kuma Ya Taimake Shi Akan Azumtar Watan Da Tsayuwa A Cikinsa Da Aiki A Cikinsa, Domin Wata Dama Ce Ga Musulmi cewa: Duk Wanda Ya Azumci Watan Ramadan Yana Mai Imani Da Neman Lada, Za'a Gafarta Masa Abinda Ya Gabata Na Zunubansa.

Ya Allah kasa mu risƙe watan Ramadan da lafiya da aminci da yalwar arziƙi, ka datar da mu falala da alkairan da ke cikinsa. Ameen ????

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ