Saqo mai muhimmanci ga masu jiran cin Gajiyar shirin CCT, RRR, PVHH, NCTO | Latsa Nan Domin karanta sakon

Mutane sunani babu Maganar Replacement ko sake cike daya daga cikin wadan nan Programs din, kuyi Hattara da masu cewa kuzo Zasuyi muku Replacement ko sake yi muku apply karya ne!
A halin yanzu babu wani Program acikin guda hudun nan da ake cikewa, idan kuma mutum ya kuskura yaje ya basu bayanansa To ka sani lalle macuta zasu cuceka ne.
Har yanzu ana Tantancewa da kuma karbar ATM Card a Qananan Hukumomin Kowacce Jiha a Fadin Najeriya musamman Jihohin Kano da sauran jihohin arewacin Kasar nan.
Wanda a halin yanzu a Jihar Kano Ana Bayar da ATM Ne a Manyan Santocin da aka Karbi bayanan mutane,
Abinda ya kamata kuyi:
Ma'aikatan Nakiran Mutane ne a Waya kosu Tura sakon SMS domin zuwa Gidan Magajin gari, Mai unguwa, da dai sauran wuraren da aka cike Shirin tun a Tsohuwar Gwamnatin data Gabata.
Ana zuwa ne da Katin Shaidar zama Ɗan Ƙasa National Identity Card (NIN)
Ayi share Domin taimakawa wasu