Illolin da ciwon sikila ke janyowa da kuma hanyoyin da za'a iya kare kai

Feb 16, 2025 - 22:07
Feb 16, 2025 - 22:08
 0
Illolin da ciwon sikila ke janyowa da kuma hanyoyin da za'a iya kare kai

Cutar sikila cuta ce ta cikin "jini"wadda ake gadon ta daga wajen iyaye,ta yarda za’a samu karancin jini masu nagarta da za su iya daukar iskar oxygen zuwa sassa na jiki baki daya.

Wannan cuta dai gadon ta akeyi. Yayin da iyaye masu dauke da cutar sikila sukayi aure ma’ana idan mahaifi (SS) da mahaifiya (SS) su kai aure,toh ba makawa akwai tabbacin zasu iya haifar me cutar sikila. 

Haka zalika idan mahaifi (AS) da mahaifiya (AS) sukai aure, akwai yuwar za’a iya samun yara masu dauke da cutar sikila. Atakai ce, ana haifar me sikila ne idan daya daga cikin iyayen yana / suna dauke da wannan cuta. 

Alamomin ciwon sikila

Alamomin wannan cuta sukan bayyana da wuri. Su kan bayyana ne tun yaro yana wajen wata shida a duniya. 

Daga cikin alamomin ta akwai:

1. Yawan Karancin jini ajikin mutum.

Hakan Kan faru ne sabida kwayar halittar jininsu Kan rasa kwari da karfi sannan ranakun su ajiki Kan ragu sosai.

A mutun Mai lafiya Wanda bashi da wannan cuta ta sikila,kwayar halittar jinin sa kanyi kwana 120 kafin su mutu,amma amasu sikila kwanakinsu baya wuce 10-20 suke mutuwa,hakan kansa karancin kwayar halittar jini ajikinsu,tadalilin haka ne suke samun karancin jini gabadaya,wannan dalila ma shiyakesa masu Cutar faama da shawara(jaundice).

Dalili nabiyu da yasa masu Cutar Kan fuskanci karancin jini kuwa shine 'matsalar da ke faruwa a inda jiki ke saamar da jini wato aplastic crisis",hakan Kan faru ne yayin da kwayar Cutar parvovirus tashiga "bone marrow" din.

2. Yawan gajiya da kasala.

Masu sikila kanyi fama da yawan  

gajiya da kasala sabida matsalar karancin jini ajikinsu dasuke fama dashi.

3. Ciwon jiki me tsanani ( musamman a cikin kasusuwa da ga‘bo’bi ).

Masu sikila kanyi fama da azababban ciwon jiki sabida toshewar magudanar jini da kwayar halittar jini Mai dauke da sickla keyi!

Ayaayin da aka Samu toshiya a magudanar jini,Sai yakasance isasshen jini baya zuwa sassa daban daban najiki,

 kamar(Kashi,gabobi,kirji,kwakwalwa,Koda da sauransu).Aduk lokacin da isasshen jini baya zuwa wani bangare na jiki,hakan Kan haifar da azababban ciwo a wannan bangaren.shiyasa kodayaushe masu wannan cuta kanyi fama da ciwon jiki sosai musamman acikin kasusuwansu da kirjinsu.

4. Kumburin hannaye da kafafuwa.

Hakan nafaruwa ne sabida toshewar Magudanar jini a masu sickla.wannan anfi samunshi a yara kananu.

5. Yawan yin laulayi ( rashin lafiya ).

Masu sikila kanyi fama da yawan laulayi da Rashin lafiya sabida matsalar karancin jini dasuke dashi ajiki.ayayin da jini yayi karanci ajiki,karfin garkuwar jikima Kan ragu,hakan zaibawa kwayoyin cuta damar shigowa cikin jiki su haddasa ciwo.

masu wannan ciwo kanfuskanci matsala a saifar su"spleen",wadda ba karamin taka rawa take ba awajen kare mutun daga cututtuka.

Wannan dalili yasa kodayaushe suke cikin Rashin lafiya.

Dan haka ne likitoci kanyiwa Yara masu Cutar rigaakafi tare da dorasu akan magunguna(antibiotics) da zai karesu daga cututtukan da za su iyayimusu barazana ga rayuwarsu(Kamar nimoniya).

6. Rashin girma / balaga da wuri

A lafiyyayyen mutun aikin kwayar halittar jini ne Kai iska da sinadaran Gina jiki zuwa sassa daban daban najiki,Dan haka alokacin da mutun ke fama da karancin jini a jiki akansamu tawaya wajen Kai wadannan sinadarai sassa daban daban na jikin,hakan kansa masu sickla Rashin girma.

7. Matsalar idanu ( rashin gani da kyau)

Akansamu wannan matsala ne sabida toshewar Magudanar jini dake Kai jini da sinadarai zuwa Ido a masu Cutar sickla.wannan dalili kansa su Samu matsalar gani.

8.Kumburin ciki

Hakan nafaruwa ne sabida kumburin hanta da saifa"spleen" dake faaruwa amasu Cutar.

Abubuwan dake tada ciwon sikila(crises)

Abubuwan dakan iya janyo masu Cutar su Samu "crisis" sunkunshi;

  • Shiga cikin sanyi
  • Rashin shan ruwa akai akai
  • Damuwa
  • Aikin wahala
  • Cuta musamman sanyi ko malaria.

Yana da kyau da duk me wannan cuta yayi kokari yakiyaye kansa daga wadannan abubuwan.

Yaushe yakamata kaga likita?

Ziyartar likita yazamanto anayinshi akai akai,sannan alokacin da aka ga daya daga cikin alamomin nan to maza a garzayo asibiti domin tallafin gaggawa.

Daga ciki akwai: zazzabi, tsananin ciwon kashi da gabbai, kumburin hannu da kafa, ciwon ciki, kumburin ciki, dashewar fatar jiki, daukewar magana, ko tsananin ciwon kai, dashewar saman farce, rashin kwari a wani bangare na jiki.

Illolin da ciwon sikila ke janyowa

1. Mutuwar barin jiki

Daga cikin manyan illolin da ciwon sikila ke janyowa shine mutuwar barin jiki.musamman idan ba a kula dashi sosai yadda yakamata

2.Matsaloli a kirji

Ta kan iya haifar da matsala a kirji ( chiwon kirji(acute chest syndrome), nimoniya tare da zazzabi da kuma daukewar numfashi ).

3.Makanta

 Cutar sikila takan iya jawo makanta, mutun ya rasa ida nun sa gaba daya.

4. Gyan bon kafa

Ciwon sikila na iya janyo gyanbon kafa da lalacewar kafa Baki daya in ba a kula dashi yadda yakamata

6.Matsala a mata

Ga mata masu juna biyu, takan haddasa hawan jini, bari ko ahaifo yaro bakwai ni.

7.Matsaloli a koda

 Cutar sikila kan iya janyo sanyin mafitsara,zubar jini acikin fitsari,ciwon Koda maza, ta kan janyo sandarewar mazakuta ta ki kwanciya, wanda hakan zai iya janyo rashin haihuwa.

8.Matsaloli a Kashi

Cutar sikila Kan iya janyo sanyin Kashi(osteomyelitis) da saurin karayar kashi.

9.Matsaloli a zuciya

Cutar sikila Kan iya janyo cuttuka na zuciya Kamar cardiomyopathy,ishchaemic heart dz,corpulmonale da ciwon zuciya(ccf).

Shawarwari dazasu taimaka

1.Hanya daya da za’a magance yaduwar wannan ciwo shi ne, yin gwaji na cutar sikila kafin ayi aure.

2.Duk mutumin dake dauke da wannan cuta yaakamace shi dayayi kokarin Kare kansa daga yanayi na sanyi ,yawan Tara gajiya, cututtuka, ko Hawa guri Mai tsayi sosai.

3.Yana da kyau agareshi da ya runka Shan ruwa sosai,yazamanto yana zuwa ganin likitaa akai akai tare da Shan magunguna na Karin jini(folic da hydroxyurea),magungunan Kara karfin garkuwar jiki(Kamar vitamin c),hakazalika yana da kyau da ya dage wajen Shan magungunan da zasu Kare shi daga malaria(watoh proguanil) da nimoniya(ta hanyar karban rigaakafi na 

pentavalent da pneumococcal vaccines),abun lura anan shine wadannan magungunan suzamanto anashansu akarkashin kulawar likita.

4.Karin jini akai akai(chronic blood transfusion with hbAA blood) bayan kowanne sati shida zaitaimaka sosai wajen bada kariya ga kamuwa da Cutar paralisis(stroke) musamman a Yara.

DR. RABIU RABIU I'm DR. RABIU RABIU, a dedicated and passionate healthcare professional with a strong background in community health. As a licensed practitioner and registered with the Community Health Practitioners Board of Nigeria, my mission is to promote wellness and provide quality care to individuals and communities.