Hanyoyi 5 dazakabi Dan samun lafiyayyan bacci
Wasu mutanen sukan bata lokuta masu tsayi suna sharar bacci a banza, wanda basusan cewa wannan baccin bashida wani alfani da ga lafiyarsu ba, a wannan rubutun munyi cikakken bayani yadda zaka samu lafiyayyen bacci wanda ze amfani ga Lafiyar ka da kuma sauran sassan jikinka

Rashin samun bacci na da matukar illa ga lafiya,yakan iya janyo cututtuka na jiki Dana kwakwalwa.
Domin samun lafiyyayan bacci,kayi wadannan Abubuwa:
1.Tsaida lokacin bacci da tashi.
Idan kana San samun lafiyyayan bacci,Yana da kyau ka Saka tsayayyan lokacin bacci da tashi akullun.idan kana kwanciya karfe Tara na dare sannan kana tashi 5 na safe,toh yazamanto kullun kanayin haka.
2.Samun bacci na akalla away shida
Akullun ana bukatar kasamu bacci na akalla awa 6,Rashin yin hakan na iyayiwa jikinka illoli daban daban
3.Kashe haske lokacin da zaka kwanta bacci
Kwanciya da haske na iya janyo maka rashin samun wadataccen bacci Wanda zaisa jikinka ya huta kafin safiya,akalla ana so ka kashe wutar dakinka ko kayi nesa da wayar ka awa daya kafin kayi bacci.
4.Kada kasha nescafe ko coffee
Nescafe da coffee na dauke da sinadarin caffeine wanda ke Hana bacci,Dan haka ba abune mai kyau ba inza ka kwanta kasha wadannan abubuwa.
5.Banda motsa jiki
Motsa jiki abune mai kyau ga lafiyar ka,Amma anfiso ayishi alokacin da yadace kamar da safe ko yamma.motsa jiki dad da zaayi bacci bashida wani amfani Kuma zai iya Hana ka samun lafiyyayan bacci.