Abubuwan dazasu sa kakamu da Farfadiya

Abubuwan dazasu sa kakamu da Farfadiya
Cutar farfadiya cutace da ta ke sa mutun jijjiga, tana zuwa tare da yin wasu dabiu na daban da fita daga hayyaci.
abubuwan da ke kawo wannan cuta ta farfadiya su ne kamar haka:
1.Gado
Ana iya samun Cutar farfadiya ta hanyar gadonta daga dangi watoh alokacin da wani acikin iyayen ko dangi yake fama da wannan ciwo
2. Matsalar cikin kwakwalwa.
Matsalolin cikin kwakwalwa kamar su kansa ko tsiro acikin kwakwalwa da cutar shanyewar barin jiki kan iya jawo wannan cuta ta farfadiya.
3. Buguwa a kai
Buguwa a kai sanadiyar hadari ko wani abun kan iya kawo cutar
4. Cututtuka na infection
Cututtuka kamar irinsu sankarau,Kanjamau dasauransu kan iya haifar da wannan cuta.
5. Matsaloli lokacin haihuwa.
Jariran da suka Sha wahala wajen haihuwa,ko suka sha ruwan nakuda,da Wanda basuyi kuka ba lokacin da aka haifesu,ko Wanda sukayi zazzabi, idansu yayi ruwan dorawa ko wata cuta ta shigesu.
Hakazalika wadanda akasamu taruwar jini da ruwa a cikin kwakwalwarsu ko kuma yaro aji masa ciwo a kai yayin fito da shi duk kan iya haddasa wannan cuta.
Alamomin cutar farfadiya.
- 1. Rikicewa
- 2. Kafewar idanuwa su kalli sama
- 3. Jijjiga (musamman kafa da hannu).
- 4. Fita daga cikin haiyaci.
- 5. Alamomin firgici da tsoro yayin fara farfadiya
- 6. Ganin walkiya ko haske yayin far farfadiya.
- 7. Yin amai, gudawa ko fitsari alokacin farfadiya.
- 8. Jiri da hajijiya.
Yaushe ya kamata a ga likita.
A nemi taimakon gaggawa dazarar anga daya daga cikin wadannan alamomi
- 1. Daukewar numfashi ko fita daga hayyaci bayan angama farfadiyar.
- 2. Jijjiga ko farfadiyar da ta wuce minti 5
- 3. Yin jijjiga ko farfadiya sama da sau daya a lokaci guda.
- 4. Zazzabi me zafi.
- 5. Macen da tai / take farfadiya alhanin tana da juna biyu.
- 6. Masu ciwon siga.
- 7. Wadanda suka ji ciwo ko suka bugu sosai bayan gama farfadiya.
Matsalolin da cutar farfadiya kan haddasa.
- 1. Faduwa, wanda hakan kan iya janyo karaya ko buguwa a kai
- 2. Masu cutar farfadiya wadanda suke shiga ruwa domin iyo ko wasa, akwai yuwar zasu iya nitsewa cikin ruwa idan farfadiya ta kamasu a ciki
- 3. Hadari yayin da suka Fara farfadiyar lokacin tuki.
- 4. Matsala na wajen haihuwa (ga uwa ko yaro)
- 5. Shiga matsalar damuwa (depression), wasu ma kan tunanin kashe kansu (suicide)