Mura / Atishawa, me ke kawota?, alamominta, yadda za'a kare kai, da kuma irin magungunan da yakamata ayi amfani dasu,

Shine me ke kawo Atishawa da Mura?
yin atishawa bawani abune Wanda mutun zai daga hankalinsaba ko yayi tunanin yin hakan alamace na wani babban ciwo ajiki.
atishawa abune mai kyau duk dadai ba dadi yayin da mutun keyi.munayin ta ne domin fitar da majina,kwayoyin cuta da gurbatacciyar iska dakan shiga cikin huhu ta hanci sannan ya iyayiwa huhun lahani.
Meke kawo atishawa da mura
Daga cikin amfanin hanci ajiki shine fitar da majina,kwayoyin cuta da gurbatacciyar iska dake shigowa lokacin numfashi,ta hakan zai hana duk wani abu dazai yimana lahani shiga cikin jikinmu.
Anfiyin mura da atishawane alokacin Rani,hazo ko damina(lokacin da Ake iska sosai)
Abubuwan dake kawo atishawa sunkunshi:
- Shakar kwayoyin cuta kamar su bacteria da viruses ta iska
- Shakar hayaki,kura,yaji,iska mai sanyi ko gurbatacciyar iska haka
- Shakar magunguna kamar su corticosteroids ta hanci
- Masu ciwon atopy ko allergy na gado(wadannan mutanen suna fama da murane akukasan kodayaushe wani sain tare da kaikayin jiki,sannan sunada yiwuwar kamuwa da asthma)
Alamomin mura dake zuwa tare atishawa.
- Fitar majina ta hanji Wanda a farko tsinkakkiyace mai ruwa,daga baya Kuma Takoma mai kauri koriya.
- Tari
- Wahalar numfashi alokacin da majina ta taru a ƙirji
- Ciwon makogaro
- Ciwon kunne a wani sa'in
- Jan ido tare da kaikayi
Illolin da mura ke iya janyowa
- Ciwon nimoniya
- Ciwon sankarau
- Ciwon kunne
- karancin ruwa ajiki
Maganin atishawa.
Amafi lokuta baafiya so a runka Shan magunguna barkatai ba ga mai mura,sabida ko ka Sha magani ko ba kasha ba,mura Bata wuce sati biyu zata tafi da kanta.
Me yakamata kayi?
1.Sirace
Sirace na da matukar amfani sosai wajen magance mura da atishawa idan zaayishi sau biyu haka a Rana.
2.magunguna na kwaya
Zaka iya siyan wadannan magungunan idan murar tayi tsanani musamman idan majinar tayi kauri sosai tanasa ka wahalar numfashi.wadannan magungunan sunkunshi:
- Loratadine
- Fexofenadine
- Cetrizine
- Antibiotics irinsu su Fleming Augmentin.
- Vitamin c
Abubuwan da zasu tàimaka maka wajen magance mura
- Tsaftace gida Yana taimakawa wajen rage kura da gurbatacciyar iska acikin muhalli.
- kare kanka daga yawan shiga hayaki ko kura ta hanyar Saka facemask aduk lokacin dazaka fita daga gida zuwa wani gurin
- mintsinin hanci ko rike hanci kamar yadda kake Yi idan kaji wani abu wari aduk lokacin dakaji atishawar zatafito
- Yawan Shan ruwa akai akai
- Cin kayan itace musamman lemon zagi a kullun Yana matukar taimakawa wajen magance mura
- Shan Shayi mai citta da tafarnuwa Shima na tàimakawa kwarai.