Me ne ne yanar ido? Me ke kawota? Ta yaya zaka iya kare kanka daga ita?

Yanar ido da yadda zaka kare kanka
Yanar Idanu matsala ce dake shafar idanu ta yadda mutum baze na gani da kyau ba.
Wannan ciwo ne dake ci ahankali ahankali
Hakan nafaruwa ne sakamakon yana da ta mamaye cikin Idanu.
A duk shekara a nigeria mutane kusan dubu darine ke kamuwa da wannan ciwo na.
Abubuwan dake kawo wannan matsala
- Shekaru
- Ciwon siga
- Hawan jini
- Matsalolin idanu tundaga haihuwa
- Aikin tiyata cikin Ido
- kiba
- shan giya da shan taba sigari
Alamomin dazakaji in kana da ita
- Gani dishi-dishi ko biyu biyu
- Raguwar gani da dare
- Rashin iya tantance launi na kala
Magani
A asibiti akeyinsa Kuma amafi yawanci tiyata akeyi acire ta.
Cutar yanar Ido tana haddasa matsaloli na Ido dayawa, tundaga kan matsalar gani har zuwa makanta.
Shawarwari
Gawasu daga cikin hanyoyi kariya da shawarwari don kare kai daga wannan cuta.
- Ana yawan zuwa asibiti domin auna Idanu musamman ga wadanda tsufa ya fara kamasu, a kalla sau daya a shekara.
- Kula da yanayin lafiya musamman su hawan jini da ciwon siga. Kada ana bari jini ko siga yana hawa
- Cin abinci da kayan itatuwa dake gina jiki musamman wadanda suke kara karfin gani. Kamar su kifi, karas, lemon zaki da sauransu.
- Kauracewa yan barasa da shan hayakin taba sigari