KULA DALAFIYA: Maganin Kuraje da Tabon Fuska na Halitta

KULA DA LAFIYA: Maganin Kuraje da Tabon Fuska na Halitta
Kuraje da tabon da suke barin a fuska matsala ce da ke damun mutane da yawa, musamman matasa. Duk da kokarin da ake yi na maganinsu, wasu tabo na iya kiyayya su bace, wanda hakan ke iya shafar kwarin gwiwa da bayyanar fuska.
Da yawa sun gwada magungunan kantin sayar da kayayyaki, amma ba kowa ya samu nasara ba. Don haka, mun kawo muku wasu hanyoyin magance tabon fuska ta hanyar amfani da kayan halitta. MUHIMMI: A zabi hanya daya kawai daga cikin wadannan, kada a gauraya su, domin hakan na iya haifar da illa ga fata.
Hanyoyin Magani:
- Dogonyaro da Kurkuma: A tafasa ganyen dogonyaro kadan sannan a hada shi da kurkuma, sai a shafa a fuska. A bar shi na minti 15 kafin a wanke da ruwan dumi.
- Dankalin Turawa: A wanke dankalin turawa, a markada shi sosai sai a shafa a fuska a matsayin mask. Wannan hanya na taimakawa wajen rage kuraje da hana su sake bayyana.
- Tafarnuwa: A daka tafarnuwa sannan a shafa a kan tabo. Ko da yake yana da wari, amma yana da amfani wajen gyara fata da kuma magance tabo.
- Hadakar Karas: Tafarnuwa da Zuma: A gauraya karas da aka sara, tafarnuwa da aka daka, da zuma a matsayin mask na fuska.
Ku gwada wadannan hanyoyin kuma ku tuna cewa hakuri da juriya sune mabuɗin samun nasara. Idan matsalar ta ci gaba, a tuntubi l
ikita.
Join our whatsApp :