Irin Abubuwan da indai kana dasu toh zaka iya samun ciwon hauka

Irin Abubuwan da indai kana dasu toh zaka iya samun ciwon hauka

Abubuwan da indai kana dasu toh zaka iya samun ciwon hauka

Irin abubuwan da indai kana dasu toh zaka iya samun ciwon hauka

Ciwon hauka na daya daga cikin manyan cututtuka da suke shafar kwakwalwa. 

Wannan ciwo yana shafar kwakwalwa ne ta yadda mutum ze na gurbataccen tunani da hargitsi wajen fahimtar rayuwa.

 Wannan na faruwa ne sakamakon gurbacewar wani sashi na kwakwalwa da yake kula da tunani, halayya, walwala da hukunci.

A duniya, cikin mutum 100,000 mutum goma zuwa shabiyar na dauke da ciwon.

A Nijeriya, a kalla mutum kimanin milliyan daya da dugo takwas ne ke fama da wannan cuta.

Maza ko mata duk zasu iya kamuwa da wannan ciwo, amma ciwon yafi yin illa ga maza sosai.

Daga yan shekara shabiyar har zuwa talatin duk kan iya kamuwa.

Mene yake janyo ciwon?

Binciken masana ya nuna babu wani takamaiman abinda ke kawo wannan ciwon. 

Harsashe na bayanai na kwararrun likitocin kwakwalwa da halayya sunyi nuni ga wasu abubuwa da kan iya haddasa cutar.

Daga ciki akwai:

Matsala da ta ke shafar cikin kwakwalwa.

  1. Gado daga iyaye
  2.  Matsanaiciyar damuwa da bacin rai
  3. Rashi, karanci ko yawan wasu sinadarai dake taimakawa kwakwalwa(Misali GABA, DOPAMINE, NORADRENALINE dasauransu.)
  4. Talauci
  5. Matsaloli na aure da iyali ko dangi
  6. Shayeshayen miyagun kwayoyi
  7. Yaran da aka aka sha wahalar cikinsu kafin a haifesu.misali:Idan yakasance mai cikin wata 4-6 tayi zazzabin "rubella" ko "influenza" toh akwai yiwuwar yaran dazata Haifa zai iyayin hauka,yaran da fayarsu tafashe da wuri ko wanda aka dade ana nakudarsu kafin a haifesu suma duk suna da yiwuwar kamuwa da wannan ciwo.
  8. Mutanen dasuka taba buguwa akai ko wadanda ke fama da Cutar farfadiya Suma da yiwuwar Zama mahaukata.
  9. Mutanen dake Zama a birni sunfi saurin kamuwa da ciwon hauka akan Wanda suke Zama a kauye.

Alamomin ciwon.

Yawan gane ganen abubuwa da babu su azahiri(mutun zaina iya ganin mutane,dabbobi,wasu halittu masu ban tsoro kamar ganin mutun da kofaton doki ko Kan jaki da sauransu).

  1. Jin surutai wanda babu wadanda suke surutan azahiri.Mutun zai iya Jin daya daga cikin wadannan:-
  2. Jin wata murya Wanda Babu ita azahiri tana wa mutun maganganu akan komai na rayuwarsa 
  3. Jin muryoyin mutun biyu na tattaunna akan abubuwan dayake yi ko kuwa yarunka jinsu suna muhawara,ko suna masa dariya,wani sa'in su kawo masa tsaigumin wani dayasani ko susa ya aikata wani mummunan laifi.
  4. Jin Kamar ana wa mutun amshin tunaninsa(ma'ana aduk lokacin dayake tunani Sai ya runka Jin wata murya na fadar tunaninsa dakarfi tamkar wanine yake karantawa agaske).

Fuskantar matsaloli na tunani, misali:

  1. jin cewar mutane na iya sanin abun da mutun ke tunani a ransa(thought broadcasting).2-jin cewar tunanin da mutun yake Yi banasa bane,ma'ana wani ne ya ari zuciyarsa yake tunani da ita,dan haka duk abun da zuciyarsa zata saaka masa zai dauka ne tamkar banasa bane na wanine(thought insertion).
  2. Jin cewa rayuwar mutun bashike da iko da itaba,sannan kuma duk abinda yakeyi bashi ya ke aikatawa ba,ma'ana wani ne daban yake sashi yayi (Passivity phenomenon).
  3.  Yawan chanjin yanayi: yawan farinciki ko damuwa.
  4. Jin kamar ana zancen ka ko yi dakai alhalin bahaka bane.
  5. Changin dabia ta mutum: doke doke, ko zage zage, kwaikwayon wani salo dakaga wani, kamar kwaikwayon tafiya, magana da sauransu.
  6. Yin sanbatu da surutan da ba'a fahimtar me ake cewa.
  7. Rashin nuna damuwa ko farinciki (flattening of affect)
  8. Gudun mutane da kauracewa ma’amala da jama’a.
  9. Rashin sanyin komai, kamar kinyin nishadi, magana da sauransu.

Shawarwari.

Yana da kyau a fahimci cewa masu irin wannan ciwo suna bukatar kulawa, kuma wannan kulawar daga kwararrun likitocin kwakwalwa. Tunanin cewa wannan ciwo bana asibiti bane sannan munrunka tunanin wani abu daban ba na mu bane kuma bashi ne mafita ba. Dan haka da zarar an fahimci mutun na fama da daya daga cikin alamomin wannan ciwon to ayi maza a kaishi asibiti. Shawokan ciwon da wuri na taimakawa matuka wajen saurin samun lafiya.