Cututtuka na barci

Barci na daga cikin abubuwan da muke yi domin rage radadi da damuwa ta yau da kullum. Rashin yin barci ko fama da cututtuka da suka danganci barci na da matukar hadari sabida zasu iya sa mutun ya samu damuwa cikin kwakwalwa.
Cutar barci cutace da ta shafi kwakwalwa, wanda me fama da wannan ciwo ze na fama da rashin barci, yin barci fiye da kima, ko kuma barci alokacin da be da ce ba.
Ire iren ciwon barci.
- 1. Insomnia(karancin bacci)
Insomnia na nufin rashin barci.
Alokacin da mutun yake dadewa kafin yafara bacci yayin da ya kwanta ko yake yawan farkawa cikin bacci yana toh Yana fama da wannan ciwo.
Duk kokarin da mutum ze yi dan ganin yayi barci da dare sai kaga abun ya ci tura.
Ana tabbatar da cewa mutun na fama da wannnan ciwo ne alokacin dayakai wajen tsahon wata guda yana fama da ciwon.
Abun dake kawo wannan matsala.
Yawancin abunda ke janyo wannan matsala sunkunshi:
- ciwon damuwa (depression),
- ciwon hauka,
- ciwon fargaba (anxiety disorders)
- Rashin daidaita takamaimai lokacin farkawa da tashi daga bacci.
- ciwon jiki
- cutar sarkewar numfashi ta manya.
- karancin sinadarin iron
- cutar thyroid
- ciwon parkinson
- shaye shayen miyagun kwayoyi
2. Hypersomnia (ciwon yawan bacci)
Duk wanda ke fama da wannan ciwo yana yawan yin bacci fiye da kima,ana tabbatar wa mutun yana da wannan matsalar ne idan yakasance yawuce tsahon wata guda yana fama da wannan matsala.
abubuwan da ke jawo wannan ciwon:
- Ciwon damuwa (depression),
- Rashin takamaiman lokacin kwanciya ko tashi daga bacci(dadewa chatting ko yin game cikin dare),
- Fama da lalura ta dadaddan lokaci.
- Shan magungunan saka barci Kamar "long acting benzodiazepine".
3. Narcolepsy.
Mutanen dake fama da wannan ciwo na yin barci ne in da be kamata ba, wato sukan iya barci a ko ina cikin taro ne ko makamancin haka. Ma'ana barci yakan iya kufce musu a kodayaushe kuma a ko wanne irin yanayi. Sukanyi gyan-gyadi ko da acikin dakin taro ne.
Anasamun wannan matsalar ne alokacin da sinadarin "hypocretin" Wanda yake kula da bacci acikin kwakwalwa yayi yawa.
Alamomin Cutar
- Yawan Jin bacci.
- Gane gane yayin kwanciya bacci.
4.Tafiya yayin bacci.
Tafiya yayin bacci cuta ce ta bacci,anfi samun wannan matsalar a Yara(Yan Shekaru 4-8) da Samari.
Alamomin wannan cuta
- mutun yakan tashi yayi tafiya cikin barci batare da yasani ba(wani sa'in zai ta yawo acikin gida koma yafita waje batare da yasani ba ko Kuma yayi ta kokarin cire Kaya ko sakawa duk cikin magagin bacci)
- idan suka farka alokacin da suke wannan magagin sukan tsorata su firgice wadansu ma suyi ta ife ife.
- yawanci basa tuna wannan magagin tafiyar dasukayi idan suntashi da safe.
5.Yin mugun mafarki da firgata yayin bacci.
Amfi ganin wannan ciwo a yara Yan Shekaru 5 zuwa 6.Mutun yakan iya yi mugun mafarki Wanda zaisa ya firgita sosai.Duk Wanda yake fama da wannan matsala yanada kyau yaje yaga likita domin rubuta Mai magani.
Shawarwari.
Ga masu fama da karancin barci ka da su na yawan barcin rana, sannan suna kwanciya waje maras hayaniya sannan a kashe fitila. Rage damuwa, firgici ko bacin rai kan taimaka sosai wajen shawo kan matsalar. A daina ta'ammali da miyagun kwayoyi, ko magungunan saka barci.
Akiyaye: shawara mafi inganci shine, idan kana/kina fama da daya daga cikin wadannan cututtukan na barci, ayi hanzarin ziyarta likitan kwakwalwa domin magani.