Ciwon gabobi(atiritis) me ke kawoshi? Mene alamomin shi? Me ne maganinshi? Ta yaya za'a iya kare kai?

Wash! gwiwa ta, waii Allah ƙugunahh!
Haka zakaji mutanen da Allah Ya ɗora wannan lalura suna faɗi yayin da suka yi yinƙurin tashi tsaye ko motsawa.
Atiratis: cuta ce wacce take kama dukkanin inda ƙashi da ƙashi suka haɗu kuma wurin yake motsawa ma'ana dai gaɓa. Inda man giris da Allah Ya sanya a gaɓoɓin kan suɗe, sai ƙashi da ƙashi suna gogar juna inda za'a ringa jin zafi da kuma kumburin wurin.
Ita dai wannan cuta tana bibiiyar shekaru ne, ma'ana tafi kama mutanen da suka manyanta daga shekara 40 zuwa sama.
Duk da a cikin kashe kashen cutar atiratis akwai wadda ake kira Jubalin atiratis wacce take cuta ce wacce rashin jituwa ta garkuwar jiki ke haifar da ita kuma yara take kamawa yan kasa da shekaru 16.
Gaɓoɓin da wannan cuta tafi rainawa:
- .Gwiwa
- .Ƙugu
- .Hannuwa( gaɓɓai)
- .Kasan dugadugi
- .Baya
Akwai nau'ukkan wannan cuta da dama dan haka ba za'a iya gane wacce kake ɗauke da ita ba sai kaje asibiti.
Alamomi
- Daga cikin alamominta akwai:
- Ciwon gaɓoɓin( kwankwaso)
- Kasa motsa gaɓoɓin
- Kumburin gaɓoɓi
- Rikewar gabobi musamman in antashi daga bacci da safe
- Ana iya ganin ja-ja a daidai gaɓoɓin da ake jin ciwon
- Zazzaɓi mara zafi
- Tsirowar Kashi a hannu
- Kumburi ko Jan ido
- Ciwon kirji
- Yawan kasala
Dss.
Mi ke kawo shi?
Dama nace maku ciwon gaɓɓai yana da kashe-kashe dayawa to kuma kowanne akwai dalilin da ke kawo shi.
Amma daga ciki dai akwai:
- Gado( idan akwai tarihin mai ɗauke da cutar a cikin dangi)
- Auto immune DX( rashin jituwa tsakanin ƙwayoyin da ke bada kariya a jiki)
- Rashin motsa jiki
- Ayyuka masu tsanani
Yadda za'a magance ta
Idan kana da wannan matsala zaka iya zuwa kaga likita a asibiti ko ka nemi ganin likita Wanda yakware a fannin watoh "rheumatologist" inda zai duba ka sosai.
Likita na iya cewa kayi wannan bincike kamar haka:
1.Hoton gwiwa
Wannan test din zai haska gabar dake ciwo yanuna meke faruwa a cikin gabar
2.Test din jini
Wannan test din zai tàimaka wajen auna wasu sinadarai na garkuwar jiki irinsu rheumatoid factor, antinuclear antibody da sauransu.
3.MRI ko CT scan
Likita zai iya bukata kayi wadannan idan hoton gaba yakasa nuna komai.
Bayan kayi tasa tasa,likita zai doraka akan magani.
Yawanci agaskiya duk cutar da za'a ce maka gado ake, ko kuma yawancin shekaru na kawo ta, to gaskiya ba za'a iya warkewa duka ba.
Amma akwai dubarun da ake yi a asibiti
1.Ana bayar da magunguna masu rage zogi da kumburi irin su inflanil,cocodamol,arthrotec,eproxen da na shafawa irinsu topical Neurogesic cream,bengay da sauransu.wadannan duk zaka iya siya kafara anfani dasu kafin kaje wajen likita Wanda zai rubuta maka na musamman
2.Ana ƙaurace wa wasu nau'in abinci( ya danganta daga wane kalar atiratis ne) kamar Jan nama,gishiri,abinci mai soda da sikari da yawa,barasa da sauransu
3.Ana koyar da motsa jiki na musamman.
Zuwa asibiti shine zai bada damar a baka magani sannan a baka shawarwarin da suka dace daidai da matsalar ka.