Masu riƙe da Takardar Sakandare, Diploma, NCE, HND, BSc, da MSc, an buɗe shafin ɗaukar ma’aikata a Ƙungiyar Agaji ta Save the Children

Masu riƙe da Takardar Sakandare, Diploma, NCE, HND, BSc, da MSc, an buɗe shafin ɗaukar ma’aikata a Ƙungiyar Agaji ta Save the Children
Save the Children tana ɗaya daga cikin manyan Ƙungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya da suka himmatu wajen taimakon yara masu bukata. Ƙungiyar tana gudanar da shirye-shirye a ƙasashe sama da 120 domin ceto yara ƙanana daga yunwa, matsanancin hali, da kuma fafutukar kare hakkinsu, tare da taimaka musu su cimma burinsu.
A Najeriya, Save the Children tana aiki domin rage yawan mutuwar yara, kasancewar ɗaya daga cikin yara biyar a ƙasar na rasuwa kafin ya kai shekaru biyar. Kimanin kashi 40 cikin 100 na yara ba sa zuwa makaranta, kuma suna tilasta yin aiki don su rayu. Haka kuma, kusan yara miliyan biyu sun rasa iyaye ɗaya ko duka biyun sakamakon kamuwa da cutar AIDS.
A halin yanzu, Ƙungiyar Save the Children ta buɗe shafin ɗaukar sabbin ma’aikata a fannoni daban-daban kamar yadda aka jero a ƙasa:
Jerin Ayyukan da Ake Nema
1. Health and Nutrition Officer
2. Livelihoods Officer
3. Livelihoods Officer
4. Child Protection Coordinator
5. Education Officer (ECW)
6. Accountability Assistant (ECW)
7. Child Protection Officer (ECW)
8. Child Protection Information Management System Assistant (ECW)