Abubuwa guda 6 da mai olsa yakamata ya nisanta

Feb 10, 2025 - 06:11
 0
Abubuwa guda 6 da mai olsa yakamata ya nisanta

Abubuwa guda 6 da mai olsa yakamata ya nisanta

Alokacin dakake fama da olsa akwai nauikan abincin da Bai kamata kanaci ba.

Cin su na Kara tsananta ciwon ko ya tayar da olsa din

Alamomin olsa dai sunkunshi:

  • Zafin kirji: shine mafi muhimmancin alama kuma wanda yawancin mutane sukafi zuwa dashi.
  • Zafi ko ciwon wuya da makogaro.
  • Ciwo ko zafin ciki musamman saman cibiya kamar ana hura maka wuta a cikin.
  • Ciwon baya
  • Yawan gyatsa
  • Aman jini awani sa'in musamman intayi kyamari.
  • Bayan gida hade da jini ko yin bayan gida mai kalar baki
  • Kasala da yin Numfashi da kyar awani sa'in

Wadannan abinci sunkunshi:

1.Shan madara

Sabon bincike yanuna cewa; madara nadaga cikin abincin dake tayar da olsa sabida yawan sinadarin 'fat' dake dauke da shi.

Hakazalika shan kindirmo na kara bada damar samarda shi acid din wanda yake qara tsanantar cutar

2.Cin soyayye ko gasasshen Abu

Cin soyayyan abinci nadaga cikin abubuwan da ke tada ko kata tsanantar olsa sabida taimakawar dasuke wajen Kara Samar da sinadarin acid aciki Wanda shine makasudin Samar da ciwon olsa.

3.kauracewa Cin Abu mai yaji

Abinci masu yaji ba abune na mai olsa ba,ko mutun zai na cinsa,sai yarunka ci kadan kadan,yaji na daga cikin abunda ke tada olsa kamar yadda cin Abu mai maiko ko tsami keyi.

4.Giya/Barasa

giya na lalata ciki dakuma duk wani sassa dake taimakawa wajen niqa abinci acikin cikin. Hakan yana kara tsannatar olsa

5.coffee dakuma lemon roba ko kwalba

Shan Coffee da lemo na kwalba na qara tsanantar olsa ta hanyar taimakawa wajen samarda sinadarin acid. 

6.shan tabar shigari

Shan tabar shigari yana haifarda matsaloli dadama wa lafiya. Aciki harda tsananta cutar olsa. 

Kiyaye wadannan nauikan abincin zai tàimaka kwarai wajen magance wannan ciwo na olsa idan aka hada da magunguna da aka bayar asibiti

DR. RABIU RABIU I'm DR. RABIU RABIU, a dedicated and passionate healthcare professional with a strong background in community health. As a licensed practitioner and registered with the Community Health Practitioners Board of Nigeria, my mission is to promote wellness and provide quality care to individuals and communities.