Manyan Illolin Yawan Shan Lemun Kwalba/Roba
Lemun kwalba/roba sun shahara sosai domin kusan kowa na shan su amma da yawa mutane basu san cewa ana alaƙanta yawan shan su da manyan matsalolin rashin lafiya. Ga wasu daga cikin matsalolin da yawan shan su ke haifar wa.

Manyan Illolin Yawan Shan Lemun Kwalba/Roba
Lemun kwalba/roba sun shahara sosai domin kusan kowa na shan su amma da yawa mutane basu san cewa ana alaƙanta yawan shan su da manyan matsalolin rashin lafiya. Ga wasu daga cikin matsalolin da yawan shan su ke haifar wa.
- 1. Yiwuwar Kamuwa Da Ciwon Sukari (Type 2 Diabetes); Yawancin lemun kwalba na ɗauke da sukari sosai wanda ke iya haifar da turjewar sinadarin dake sarrafa sukari (insulin resistance) Wanda hakan na iya gaggauta yiwuwar kamuwa da ciwon sukari.
- 2. Matsalar Ciwon Hakora; Yawancin lemun kwalba sun kasance suna da sukari da nau'in asid wanda sinadarai ne masu iya zagwanyar da hakora da dasashi har ya haifar da kogi/rami a hakora da kuma tada olsa ma wasu.
- 3. Matsalar Ƙashi; An tabbatar da cewa yawan shan lemun kwalba na rage kwarin kashi (osteoporosis) wanda hakan na iya haifar da saurin karaya a ɗan kankanin buguwa ko rauni.
- 4. Matsalar Zuciya; Yawan shan lemun kwalba na iya haifar da ciwon zuciya a sanadiyar sukari mai yawa da yake ɗauke dashi dakan iya ƙara gudun jini a jiki wanda hakan na iya haifar da hawan jini.
- 5. Ciwon Hanta (Non-alcoholic Faty Liver Disease); Ciwon hantar da yawan shan giya/harasa ke haifar wa, ana iya samun wani nau'in shi in mutum ya kasance mai yawan shan lemun kwalba.
- 6. Matsalar Kumburin Ciki; Shan lemun kwalba da yawa na haifar da cushewan ciki lokaci bayan lokaci.
- 7. Ciwon Sabo: Wasu daga cikin Lemun kwalba suna ɗauke da sinadarin CAFFEINE wanda yawan shan shi na haifar da CIWON SABO (Addiction), watau mutum ba zai iya rayuwa ba sai ya sha.
- 8. Cutar Ƙiba; Yawan shan su na haifar da saurin kamuwa da cutar ƙiba (obesity).
- 9. Rage Ƙarfin Aikin Koda
- Wannan matsalolin na aukuwa ne yayin da ake sha da yawa ba bisa ka'ida ba, shan shi ɗan daidai baya haifar da wannan matsalolin. Pharmacist Musa A Bello yace mu kula da lafiyar mu domin kanm
- Forwarded to you:
- Habeeb Bin Muhd
- Public health practitioner