Hanyoyi 4 dazakabi ka magance istimna'i

Hanyoyi 4 dazakabi ka magance istimna'i
Istimnai nadaga cikin matsalolin dake damun matasan mu sosai.yakansa mutun shiga cikin damuwa da zullumi,wani sa'in harta Kai ga abin ya janyowa mutun matsaloli na rashin lafiya sabida damuwa
Akullun Muna karbar tambayoyi dayawa akan yadda za'a magance wannan matsala.
Illolin dayake janyowa
Daga cikin abubuwan dazai iya janyowa sunkunshi:
1.Addiction
Yana zama addiction(ma'ana abune Wanda inkasaba bazaka iya dainawa ba)
2.Hanaka yin abubuwa muhimmi
Daga cikin illolin Aikata wannan Abu shine hanaka yin abubuwa masu muhimmanci kamar zuwa makaranta,kasuwa ko wajen aiki sabida tunanin yadda zaka samu ka Aikata shi.
3.Rage sha'awa
Bincike yanuna Aikata hakan na rage shaawar Yin soyayya koma aure sabida masu Aikata hakan na tunanin zasu iya biyawa kansu bukata batare da sunyi aure ba
4.Mantuwa
mafi yawan mutane dake Aikata wannan Abu sunce suna fama da matsalar yawan mantuwa.amma babu wani bincike na likitanci da ya tabbatar da haka
5.Makanta
Daga cikin matsalolin damuke yawan karba daga masu fama da wannan matsala shine suna samun raguwar Gani.
Shima babu wani bincike da ya tabbatar dahaka.amma mafi yawancin mutane na fama da wannan matsala
6.Rashin iya gamsar da abokin tarayya
Idan mutun na Aikata wannan Abu.akwai yiwuwar zaiyi fama da rashin iya gamsar da abokin tarayya alokacin saduwa
Magani
A hakikanin gaskia babu wani magani da zakasha yahana ka yin wannan Abu,sai dai akwai hanyoyi da zasu tàimaka sosai wajen magance wannan matsala kamar haka:
1.Kadaina yawan zama Kai kadai awaje daya
Bawai dan ance ka yanke mu'amalarka da abokan banza, saikace "nizanyi rayuwata nikadai batareda kowaba". Sam hakan shima badaidai bane. Hasalima shima zama kaikadai acikin daki zaisa kasake tunawa da abubuwanda kake kokarin kauracewa dagasu. Ba'a ta6a rasa abokan arzikiba, saiko Idan baka shirya barin wannan dabi'ar ba.
2.ka/ki Daina boye soyayyar ka/ki ga duk Wanda kake/kike so
Mutane dadama suna kasa furta ko bayyana soyayyarsu zuwaga wadanda suke kauna, saboda wasu dalilai na rayuwa. Ta dalilin haka kuwa saisu kasa jurewa, sannan sukasance masu tunawa da wadanda sukeson harya kaiga suna samun nutsuwane tahanyar aikata wannan mummunar dabi'ar. Yi kokarin bayyana soyayyarka ga duk wacce kaji kanaso ko Wanda kikaji kinaso. A duniya akwai samu akwai kuma rashi.
3.Daina kallan fina finai ko hotunan batsa a social media ko yanar gizo
Idan ka shiryawa barin wannan mummunar dabi'ar, tofa yazama lallai ka hana kanka da kallace-kallace musamman a yanar gizo-gizo. Shawara anan shine kayi kokarin barin kusantar duk wani Abu a yanar gizo mai dauke da wadannan hotuna dakuma video na batsa.
4.Kayi/keyi kokarin yin aure
Amafi lokuta babbar hanya mafi sauki dazaka magance wannan matsalar shine yin aure.idan kana/kina yawan fama da wannan matsala toh ka daure kayi aure.
5.Kadage da addua
Wannan itace hanya mafi muhimmanci dazakabi danganin ka tseratar dakanka saga wannan mummunar dabi'ar. Babu abunda ya gagari MAHALICCINKA. Lallai babushi.