SOMTECH MEDIA - : kiwon lafiya
Yara Meke kawo Nimoniya a yara?
Meke kawo Nimoniya a yara?
Nimoniya cutace datake shafar Huhu. Acikin huhu akwai wasu 'yan jakka da ake kira dasuna "alveoli"inda nanne iska ke zuwa alokacin da muke numfashi. Wadannan alveoli, suna cikene da iska. Alokacin da Kwayar cuta tashiga cikin huhun,takan janyo kumburin wadannan "alveoli" din tare da rage yawan iskar dake ciki, hakanne yakesa yaro daya kamuda nimoniyar yariqa jin zafi yayinda yake nunfashi yakuma hanashi shaqar iskar oxygen ishashshe.
Kungiyar lafiya ta duniya wato WHO, ta bayyana Nimoniya na yara kamar haka " Wata matsalace ga lafiya, wacce take tafeda tari ko nunfashi dakyar-dakyar. Ana iya ganetane ta hanyar bincikar numfashin yaro ko yananan dai-dai ko akasin hakan yayinda aka duba kasan kirjin yaron ko yana fadawa batareda yaron yafice daga hayyacin saba.
Meke kawo wannan ciwo?
Kwayoyin cuta irinsu bakteriya, bairos, fungai ( bacteria, virus, and fungi) sune ke kawo wannan cuta alokacin dasuka shiga cikin Huhu.
Atakaice dai yayinda, daya daga cikin kwayoyin cutar yasamu damar isa zuwa Huhu shike haddasa ta. Wanda sukafi kawowa sune Kwayar cutar bacteria maisuna striptokokkus nimoniya ( streptococcus pneumonia) dakuma Hemopilos influanza taib bi ( Hemophilus influenza type b. [Hib])
Yadda cutar ke yaduwa
Nimoniya tana yaduwa ta hanyoyi dadama:
Kwayar cutar bairos da bakteriya wadanda ake yawan samunsu a hancin yara ko makogwaro sukan isa sushafi Huhun yaron yayinda yaro ya shaqesu
Hakazalika cutar tana yaduwa tahanyar zubarda kaki(majina) lokacin yin tari ko attishawa.
Sanannan takan yadu ta jini musamman lokacin haihuwa.
Ta kan yadu ta hayaqin da yake zagayawa cikin gidaje yayin dafa abinci kodai kona wani abu
Takan yadu a inda babu ishashshen iska misali a daki dan karami ko marasa winduna , yana karawa yaro barazanar kamuwa da nimoniya.Haka zalika cikin taron al'umma.
Alamomin nimoniya a yara
Tari
Nunfashi dasauri-dasauri ko ahankali-ahankali ko Nunfashi dakyar-dakyar
Wani sauti daga kirji kamar ana sace balonbalon
Zazza6i
Ciwon makogwaro
Ciwon kai
Rashin son cin abinci
Dazaran wadannan alamomin sun bayyana ayi gaggawar kai yaro asibiti.
Sauda yawa yara suna rasa ransu akan Nimoniya ne, saboda masu kula dasu ko iyayensu basu iya gane alamomintaba.
Hanyoyin kariya daga Nimoniya
Akwai hanyoyi dadama dazamu kare kanmu da yaranmu daga wannan cutar.
Amma ga muhimman kamar haka:
• Rigakafi
Rigakafi hanyace ingantacciya ta kare yara daga cutar NIMONIYA. Anayin wannan Rigakafin a asibiti bayan sati hudu da haihuwar yara dakuma bayan sati shida sannan kuma bayan sati goma. Yanada kyau yara susami wadannan Rigakafin.
• Ishashshun abinci masu qara lafiya:
Ishashshen abinci masu qara lafiya wa yara, yana farawane daga shayar dasu ruwan nono zalla na tsawon wata shida ( exclusive breastfeeding for the first six months). Yin hakan yana karawa yara karfin garkuwar jiki dakuma kariya daga nimoniya kokuma yahana cutar tsawaita ajikin yara.
• Tsabtar muhalli:
Tsabtar muhalli yana taimakawa wajen bada kariya daga cututtuka dayawa, saboda kana kokarin fitar da wasu kayan dattine dakan iya 6oye kwayoyin cuta.
Domin nimoniya yadace makaucewa taron al'umma misali kauracewa tara yara fiye da hudu ko biyar a daki daya ko wajen biki kodai duk wani wurin taronda nunfashin mutane yana gaurayuwa dana juna, ta yadda dazaran wani yayi tari ko attishawa akwai barazanar kamuwa da cutar. Sannan kuma da kauracewa duk wani mulallinda Hayaqi yake.
Saikuma akara da wadannan hanyoyin
Wanke hannaye da ruwa da sabulu
Sanya takunkumi
Motsa jiki
Ziyartar asibiti akan lokaci
Mungode.
Amfanin Shan lemon zagi guda daya kullun
Amfanin Shan lemon zagi guda daya kullun
Shan lemon zaki na bawo guda daya kacal akullum namatukar taimakawa jiki wajen gudanar da ayyukansa na yau da kullun da magance cututtuka da dama.
Anan zamuyi dan gajeren rubutu akan amfanin sa guda takwas:
1.Kariya daga cutar kansa
lemo yana taimakawa wajen rage wa mutun yiwuwar kamuwa da ciwon Kansa Kowacce iriyace harsahen wani bincike.
Lemon zaki na dauke da wadataccen sinadarin(citrus limonoids),kuma wannan sinadarin na taimakawa wajen hana kamuwa da kansar fata da huhu da nono da ciki da kuma hanji.
2.Kariya daga kamuwa da ciwon koda
Lemo yana taimakawa wajen magance cutar koda da kuma rage hatsarin kamuwa da cutar nan na duwatsun koda(kidney stones).
3.Taimakawa wajen narka abinci
Yana taimakawa sinadaran ciki wajen samun damar narka abinci yadda yakamata ta yadda jiki zai amfana sosai daga abincin.
4.Yana sa fata kyalli da sheki
Yana dauke da sinadarin Vitamin C da "Antioxidant"Wanda suke taimakawa wajen bawa fata kariya daga cututtuka daban daban.
Yana Hana fata yin yaushi tare dasata sheki da kyalli.
5.yana Kara karfin idanu da Bada kariya daga kamuwa da cututtukan ido
Yana taimakawa idanu wajen Samar da kyakkyawan gani saboda yana da sinadarin (carotenoid compound)masu yawa Wadanda ake juyasu su zama (bitamin A),sai su taimaka wajen hana matsalar gani.
6.Kariya daga cututtuka masu hatsari
Yana rage hatsarin kamuwa da cututtuka masu hastari,saboda yana dauke da sinadarin bitamin C da yawa.
7.Kariya daga hawan jini da ciwon siga
Bincike yanuna cewa yawan Shan lemon Zaki kan bada kariya daga kamuwa da wannan cututtuka biyu tare da daidaita hawan jini da siga ajiki.
8.Kara tsawon rayuwa
Lemo na dauke da sinadarin vitamin c da "antioxidants" dayawa.yawan Shan lemo Kan taimaka wajen Kara tsayin rayuwa ta hanyar kare mutun daga kamuwa da cututtuka dayawa!!Yawan shan lemon zaki na bawo na iya mai dan shekara 50 kamar saurayi.
Wash! gwiwa ta, waii Allah ƙugunahh!
Haka zakaji mutanen da Allah Ya ɗora wannan lalura suna faɗi yayin da suka yi yinƙurin tashi tsaye ko motsawa.
Atiratis: cuta ce wacce take kama dukkanin inda ƙashi da ƙashi suka haɗu kuma wurin yake motsawa ma'ana dai gaɓa. Inda man giris da Allah Ya sanya a gaɓoɓin kan suɗe, sai ƙashi da ƙashi suna gogar juna inda za'a ringa jin zafi da kuma kumburin wurin.
Ita dai wannan cuta tana bibiiyar shekaru ne, ma'ana tafi kama mutanen da suka manyanta daga shekara 40 zuwa sama.
Duk da a cikin kashe kashen cutar atiratis akwai wadda ake kira Jubalin atiratis wacce take cuta ce wacce rashin jituwa ta garkuwar jiki ke haifar da ita kuma yara take kamawa yan kasa da shekaru 16.
Gaɓoɓin da wannan cuta tafi rainawa:
.Gwiwa
.Ƙugu
.Hannuwa( gaɓɓai)
.Kasan dugadugi
.Baya
Akwai nau'ukkan wannan cuta da dama dan haka ba za'a iya gane wacce kake ɗauke da ita ba sai kaje asibiti.
Alamomi
Daga cikin alamominta akwai:
Ciwon gaɓoɓin( kwankwaso)
Kasa motsa gaɓoɓin
Kumburin gaɓoɓi
Rikewar gabobi musamman in antashi daga bacci da safe
Ana iya ganin ja-ja a daidai gaɓoɓin da ake jin ciwon
Zazzaɓi mara zafi
Tsirowar Kashi a hannu
Kumburi ko Jan ido
Ciwon kirji
Yawan kasala
Dss.
Mi ke kawo shi?
Dama nace maku ciwon gaɓɓai yana da kashe-kashe dayawa to kuma kowanne akwai dalilin da ke kawo shi.
Amma daga ciki dai akwai:
Gado( idan akwai tarihin mai ɗauke da cutar a cikin dangi)
Auto immune DX( rashin jituwa tsakanin ƙwayoyin da ke bada kariya a jiki)
Rashin motsa jiki
Ayyuka masu tsanani
Yadda za'a magance ta
Idan kana da wannan matsala zaka iya zuwa kaga likita a asibiti ko ka nemi ganin likita Wanda yakware a fannin watoh "rheumatologist" inda zai duba ka sosai.
Likita na iya cewa kayi wannan bincike kamar haka:
1.Hoton gwiwa
Wannan test din zai haska gabar dake ciwo yanuna meke faruwa a cikin gabar
2.Test din jini
Wannan test din zai tàimaka wajen auna wasu sinadarai na garkuwar jiki irinsu rheumatoid factor, antinuclear antibody da sauransu.
3.MRI ko CT scan
Likita zai iya bukata kayi wadannan idan hoton gaba yakasa nuna komai.
Bayan kayi tasa tasa,likita zai doraka akan magani.
Yawanci agaskiya duk cutar da za'a ce maka gado ake, ko kuma yawancin shekaru na kawo ta, to gaskiya ba za'a iya warkewa duka ba.
Amma akwai dubarun da ake yi a asibiti
1.Ana bayar da magunguna masu rage zogi da kumburi irin su inflanil,cocodamol,arthrotec,eproxen da na shafawa irinsu topical Neurogesic cream,bengay da sauransu.wadannan duk zaka iya siya kafara anfani dasu kafin kaje wajen likita Wanda zai rubuta maka na musamman
2.Ana ƙaurace wa wasu nau'in abinci( ya danganta daga wane kalar atiratis ne) kamar Jan nama,gishiri,abinci mai soda da sikari da yawa,barasa da sauransu
3.Ana koyar da motsa jiki na musamman.
Zuwa asibiti shine zai bada damar a baka magani sannan a baka shawarwarin da suka dace daidai da matsalar ka.
Shine me ke kawo Atishawa da Mura?
yin atishawa bawani abune Wanda mutun zai daga hankalinsaba ko yayi tunanin yin hakan alamace na wani babban ciwo ajiki.
atishawa abune mai kyau duk dadai ba dadi yayin da mutun keyi.munayin ta ne domin fitar da majina,kwayoyin cuta da gurbatacciyar iska dakan shiga cikin huhu ta hanci sannan ya iyayiwa huhun lahani.
Meke kawo atishawa da mura
Daga cikin amfanin hanci ajiki shine fitar da majina,kwayoyin cuta da gurbatacciyar iska dake shigowa lokacin numfashi,ta hakan zai hana duk wani abu dazai yimana lahani shiga cikin jikinmu.
Anfiyin mura da atishawane alokacin Rani,hazo ko damina(lokacin da Ake iska sosai)
Abubuwan dake kawo atishawa sunkunshi:
Shakar kwayoyin cuta kamar su bacteria da viruses ta iska
Shakar hayaki,kura,yaji,iska mai sanyi ko gurbatacciyar iska haka
Shakar magunguna kamar su corticosteroids ta hanci
Masu ciwon atopy ko allergy na gado(wadannan mutanen suna fama da murane akukasan kodayaushe wani sain tare da kaikayin jiki,sannan sunada yiwuwar kamuwa da asthma)
Alamomin mura dake zuwa tare atishawa.
Fitar majina ta hanji Wanda a farko tsinkakkiyace mai ruwa,daga baya Kuma Takoma mai kauri koriya.
Tari
Wahalar numfashi alokacin da majina ta taru a ƙirji
Ciwon makogaro
Ciwon kunne a wani sa'in
Jan ido tare da kaikayi
Illolin da mura ke iya janyowa
Ciwon nimoniya
Ciwon sankarau
Ciwon kunne
karancin ruwa ajiki
Maganin atishawa.
Amafi lokuta baafiya so a runka Shan magunguna barkatai ba ga mai mura,sabida ko ka Sha magani ko ba kasha ba,mura Bata wuce sati biyu zata tafi da kanta.
Me yakamata kayi?
1.Sirace
Sirace na da matukar amfani sosai wajen magance mura da atishawa idan zaayishi sau biyu haka a Rana.
2.magunguna na kwaya
Zaka iya siyan wadannan magungunan idan murar tayi tsanani musamman idan majinar tayi kauri sosai tanasa ka wahalar numfashi.wadannan magungunan sunkunshi:
Loratadine
Fexofenadine
Cetrizine
Antibiotics irinsu su Fleming Augmentin.
Vitamin c
Abubuwan da zasu tàimaka maka wajen magance mura
Tsaftace gida Yana taimakawa wajen rage kura da gurbatacciyar iska acikin muhalli.
kare kanka daga yawan shiga hayaki ko kura ta hanyar Saka facemask aduk lokacin dazaka fita daga gida zuwa wani gurin
mintsinin hanci ko rike hanci kamar yadda kake Yi idan kaji wani abu wari aduk lokacin dakaji atishawar zatafito
Yawan Shan ruwa akai akai
Cin kayan itace musamman lemon zagi a kullun Yana matukar taimakawa wajen magance mura
Shan Shayi mai citta da tafarnuwa Shima na tàimakawa kwarai.
Irin Abubuwan da indai kana dasu toh zaka iya samun ciwon hauka
Abubuwan da indai kana dasu toh zaka iya samun ciwon hauka
Irin abubuwan da indai kana dasu toh zaka iya samun ciwon hauka
Ciwon hauka na daya daga cikin manyan cututtuka da suke shafar kwakwalwa.
Wannan ciwo yana shafar kwakwalwa ne ta yadda mutum ze na gurbataccen tunani da hargitsi wajen fahimtar rayuwa.
Wannan na faruwa ne sakamakon gurbacewar wani sashi na kwakwalwa da yake kula da tunani, halayya, walwala da hukunci.
A duniya, cikin mutum 100,000 mutum goma zuwa shabiyar na dauke da ciwon.
A Nijeriya, a kalla mutum kimanin milliyan daya da dugo takwas ne ke fama da wannan cuta.
Maza ko mata duk zasu iya kamuwa da wannan ciwo, amma ciwon yafi yin illa ga maza sosai.
Daga yan shekara shabiyar har zuwa talatin duk kan iya kamuwa.
Mene yake janyo ciwon?
Binciken masana ya nuna babu wani takamaiman abinda ke kawo wannan ciwon.
Harsashe na bayanai na kwararrun likitocin kwakwalwa da halayya sunyi nuni ga wasu abubuwa da kan iya haddasa cutar.
Daga ciki akwai:
Matsala da ta ke shafar cikin kwakwalwa.
Gado daga iyaye
Matsanaiciyar damuwa da bacin rai
Rashi, karanci ko yawan wasu sinadarai dake taimakawa kwakwalwa(Misali GABA, DOPAMINE, NORADRENALINE dasauransu.)
Talauci
Matsaloli na aure da iyali ko dangi
Shayeshayen miyagun kwayoyi
Yaran da aka aka sha wahalar cikinsu kafin a haifesu.misali:Idan yakasance mai cikin wata 4-6 tayi zazzabin "rubella" ko "influenza" toh akwai yiwuwar yaran dazata Haifa zai iyayin hauka,yaran da fayarsu tafashe da wuri ko wanda aka dade ana nakudarsu kafin a haifesu suma duk suna da yiwuwar kamuwa da wannan ciwo.
Mutanen dasuka taba buguwa akai ko wadanda ke fama da Cutar farfadiya Suma da yiwuwar Zama mahaukata.
Mutanen dake Zama a birni sunfi saurin kamuwa da ciwon hauka akan Wanda suke Zama a kauye.
Alamomin ciwon.
Yawan gane ganen abubuwa da babu su azahiri(mutun zaina iya ganin mutane,dabbobi,wasu halittu masu ban tsoro kamar ganin mutun da kofaton doki ko Kan jaki da sauransu).
Jin surutai wanda babu wadanda suke surutan azahiri.Mutun zai iya Jin daya daga cikin wadannan:-
Jin wata murya Wanda Babu ita azahiri tana wa mutun maganganu akan komai na rayuwarsa
Jin muryoyin mutun biyu na tattaunna akan abubuwan dayake yi ko kuwa yarunka jinsu suna muhawara,ko suna masa dariya,wani sa'in su kawo masa tsaigumin wani dayasani ko susa ya aikata wani mummunan laifi.
Jin Kamar ana wa mutun amshin tunaninsa(ma'ana aduk lokacin dayake tunani Sai ya runka Jin wata murya na fadar tunaninsa dakarfi tamkar wanine yake karantawa agaske).
Fuskantar matsaloli na tunani, misali:
jin cewar mutane na iya sanin abun da mutun ke tunani a ransa(thought broadcasting).2-jin cewar tunanin da mutun yake Yi banasa bane,ma'ana wani ne ya ari zuciyarsa yake tunani da ita,dan haka duk abun da zuciyarsa zata saaka masa zai dauka ne tamkar banasa bane na wanine(thought insertion).
Jin cewa rayuwar mutun bashike da iko da itaba,sannan kuma duk abinda yakeyi bashi ya ke aikatawa ba,ma'ana wani ne daban yake sashi yayi (Passivity phenomenon).
Yawan chanjin yanayi: yawan farinciki ko damuwa.
Jin kamar ana zancen ka ko yi dakai alhalin bahaka bane.
Changin dabia ta mutum: doke doke, ko zage zage, kwaikwayon wani salo dakaga wani, kamar kwaikwayon tafiya, magana da sauransu.
Yin sanbatu da surutan da ba'a fahimtar me ake cewa.
Rashin nuna damuwa ko farinciki (flattening of affect)
Gudun mutane da kauracewa ma’amala da jama’a.
Rashin sanyin komai, kamar kinyin nishadi, magana da sauransu.
Shawarwari.
Yana da kyau a fahimci cewa masu irin wannan ciwo suna bukatar kulawa, kuma wannan kulawar daga kwararrun likitocin kwakwalwa. Tunanin cewa wannan ciwo bana asibiti bane sannan munrunka tunanin wani abu daban ba na mu bane kuma bashi ne mafita ba. Dan haka da zarar an fahimci mutun na fama da daya daga cikin alamomin wannan ciwon to ayi maza a kaishi asibiti. Shawokan ciwon da wuri na taimakawa matuka wajen saurin samun lafiya.
Me ke kawo kaikayi / Jan ido?
kaikayin ido ko Jan ido alamu ne na matsaloli dayawa dake shafar ido.sannan abune Wanda zaka iya kare kanka daga shi
Ko meke kawo kaikayi/Jan ido?
Abubuwan dake kawo kaikayin ido nadayawa daga ciki akwai:
1.Yanayi
mafi yawan mutane na fuskantar wannan matsala ne alokacin Rani/ko hunturun sanyi,ko damina,wato a wannan lokacin iska na busawa sosai Kuma tana saurin shiga ido.
2.Shiga cikin gurbatacciyar iska
shiga cikin gurbatacciyar iska kamar hayaki ko turare mai karfi ko man fetir kan iya janyo wannan matsala ta kaikayin ido
3.Sanyi na ido
kwayoyin cuta irin su bakteriya,biros da fungus ke kawo wannan matsala t sanyi na ido,(conjunctivitis,uveilitis, blepharitis).yakan janyo ido yayi ta kaikayi,yayi ja sannan yarunka fitar da kwansa
4.Bushewar ido
abubuwa dayawa ka iya janyo wannan matsala kamar ciwon siga,ciwon rheumatism,Shan magunguna (irinsu na hawan jini,ciwon damuwa, magungunan mura da na kayyade iyali).hakazalika alokacin da mutun ke girma idan sa nakara bushewa.
4.Gajiyar ido.
ido na gajiya alokacin da aka dade ana kallan wani Abu dashi musamman waya, computer,karatu da fitila mara haske ko rashin samun isasshen bacci.alokacin da ido yagaji sai yafara yin ja Yana kaikayi da ciwo.
6.Shigar wani Abu ciki ido
faduwar wani Abu cikin ido kamar kwaro,tsakuwa,yaji da dai sauransu kan janyo ido yayi ja ko yayi ta kaikayi
Shin mene maganin kaikayin ido?
magani a asibiti ake badashi.likita zai iya baka wadannan magunguna:
Magani na digawa a ido
Antihistamines da
Antibiotics inta kama
Abunda zasu taimaka
1.Daddanna ido da ruwan sanyi da tawul alokacin da wannan matsala ta sameka.kasamo ruwan sanyi da tawul Dinka mai tsafta sai ka Saka ciki ruwan sanyin,bayan ka matse shi sai ka daddanna a idon dake ma kaikayi nadan lokaci kadan,hakan nataimakawa kwairai.
2.yawan Wanke hannaye
3.Saka facemask in zaafita waje
4.Kula da tsaftar muhalli da rage kura akai akai.
5.Rage amfani da waya da computer.inkasan kana yawan amfani da wadannan abubuwan zaka iya runka daukar hutun minti 20 bayan ko wanne awa daya dakayi kana amfani dasu.
6.Samun isasshen bacci da hutu
Yana da kyau kaje asibiti kaga likita ko ka nemi ganin kwararran likitan ido watoh Opthalmologist domin samun cikakken kulawa.
Me ne ne yanar ido? Me ke kawota? Ta yaya zaka iya kare kanka daga ita?
Yanar ido da yadda zaka kare kanka
Yanar Idanu matsala ce dake shafar idanu ta yadda mutum baze na gani da kyau ba.
Wannan ciwo ne dake ci ahankali ahankali
Hakan nafaruwa ne sakamakon yana da ta mamaye cikin Idanu.
A duk shekara a nigeria mutane kusan dubu darine ke kamuwa da wannan ciwo na.
Abubuwan dake kawo wannan matsala
Shekaru
Ciwon siga
Hawan jini
Matsalolin idanu tundaga haihuwa
Aikin tiyata cikin Ido
kiba
shan giya da shan taba sigari
Alamomin dazakaji in kana da ita
Gani dishi-dishi ko biyu biyu
Raguwar gani da dare
Rashin iya tantance launi na kala
Magani
A asibiti akeyinsa Kuma amafi yawanci tiyata akeyi acire ta.
Cutar yanar Ido tana haddasa matsaloli na Ido dayawa, tundaga kan matsalar gani har zuwa makanta.
Shawarwari
Gawasu daga cikin hanyoyi kariya da shawarwari don kare kai daga wannan cuta.
Ana yawan zuwa asibiti domin auna Idanu musamman ga wadanda tsufa ya fara kamasu, a kalla sau daya a shekara.
Kula da yanayin lafiya musamman su hawan jini da ciwon siga. Kada ana bari jini ko siga yana hawa
Cin abinci da kayan itatuwa dake gina jiki musamman wadanda suke kara karfin gani. Kamar su kifi, karas, lemon zaki da sauransu.
Kauracewa yan barasa da shan hayakin taba sigari
Yadda abarba ke Gina jiki
Yadda abarba ke Gina jiki
Abarba na daga cikin kayan itatuwa Wanda suke kara lafiya sosai a jikin Dan Adam.
Anan za mu lissafo amfanin Shan abarba guda goma Sha biyar ajiki.
1.Dauke da sinadarai masu Gina jiki
Abarba na dauke da sinadarai masu yawan gaske wanda suke kara lafiya ajikin dan Adam kamar su(kalori,protein, carbs,fiber,bitamin C,manganese, bitaminB6,copper, thiamine, folate da potassium). Wanda suke taimakawa wajen Gina jiki,Kara lafiyar Gani da kaifin kwakwalwa
2.kariya daga cututtuka
Tana dauke da sinadarin 'antioxidant' Wanda yake rage kamuwa da cututtuka daban daban kamar ciwon zuciya,ciwon sukari da kuma Kansa.
3.Narka abinci aciki
Daga cikin amfanin abarba shine taimakawa wajen narka abinci yadda yakamata,yadda jiki zai amfanu sosai dagashi.
4.kara garkuwar jiki
Abarba na bada taimako wajen karfafa garkuwar jiki wanda hakan zai taimaka wajen kare jiki daga shigar cututtuka daban daban.
5.maganin ciwon gabobi
Abarba na taimakawa wajen rage radadin alamomin kumburin gabbai(Arthritis) da ciwon jiki
6.Ciwon baya
Kamar yadda take taimakawa wajen ciwon gabbai hakazalika tana taimakawa wajen rage kumburi da radadin ciwo bayan anyi wa mutum tiyata.
7.Rage teba
Abarba nadaga cikin kayan itacen dake taimakawa wajen rage teba da kiba.idan kana San hakan saika runka ci akai akai
8.Lafiyar kashi
Bincike na likitanci yanuna cewa cin abarba akai akai nataimakawa wajen Kara lafiya da karfin kashi.
9.Haihuwa
Bincike yanuna abarba na taimaka wajen kare mutun daga cututtuka dake shafar haihuwa.idan kana San haihuwa karunka cin abarba akai akai.
Cutar sikila cuta ce ta cikin "jini"wadda ake gadon ta daga wajen iyaye,ta yarda za’a samu karancin jini masu nagarta da za su iya daukar iskar oxygen zuwa sassa na jiki baki daya.
Wannan cuta dai gadon ta akeyi. Yayin da iyaye masu dauke da cutar sikila sukayi aure ma’ana idan mahaifi (SS) da mahaifiya (SS) su kai aure,toh ba makawa akwai tabbacin zasu iya haifar me cutar sikila.
Haka zalika idan mahaifi (AS) da mahaifiya (AS) sukai aure, akwai yuwar za’a iya samun yara masu dauke da cutar sikila. Atakai ce, ana haifar me sikila ne idan daya daga cikin iyayen yana / suna dauke da wannan cuta.
Alamomin ciwon sikila
Alamomin wannan cuta sukan bayyana da wuri. Su kan bayyana ne tun yaro yana wajen wata shida a duniya.
Daga cikin alamomin ta akwai:
1. Yawan Karancin jini ajikin mutum.
Hakan Kan faru ne sabida kwayar halittar jininsu Kan rasa kwari da karfi sannan ranakun su ajiki Kan ragu sosai.
A mutun Mai lafiya Wanda bashi da wannan cuta ta sikila,kwayar halittar jinin sa kanyi kwana 120 kafin su mutu,amma amasu sikila kwanakinsu baya wuce 10-20 suke mutuwa,hakan kansa karancin kwayar halittar jini ajikinsu,tadalilin haka ne suke samun karancin jini gabadaya,wannan dalila ma shiyakesa masu Cutar faama da shawara(jaundice).
Dalili nabiyu da yasa masu Cutar Kan fuskanci karancin jini kuwa shine 'matsalar da ke faruwa a inda jiki ke saamar da jini wato aplastic crisis",hakan Kan faru ne yayin da kwayar Cutar parvovirus tashiga "bone marrow" din.
2. Yawan gajiya da kasala.
Masu sikila kanyi fama da yawan
gajiya da kasala sabida matsalar karancin jini ajikinsu dasuke fama dashi.
3. Ciwon jiki me tsanani ( musamman a cikin kasusuwa da ga‘bo’bi ).
Masu sikila kanyi fama da azababban ciwon jiki sabida toshewar magudanar jini da kwayar halittar jini Mai dauke da sickla keyi!
Ayaayin da aka Samu toshiya a magudanar jini,Sai yakasance isasshen jini baya zuwa sassa daban daban najiki,
kamar(Kashi,gabobi,kirji,kwakwalwa,Koda da sauransu).Aduk lokacin da isasshen jini baya zuwa wani bangare na jiki,hakan Kan haifar da azababban ciwo a wannan bangaren.shiyasa kodayaushe masu wannan cuta kanyi fama da ciwon jiki sosai musamman acikin kasusuwansu da kirjinsu.
4. Kumburin hannaye da kafafuwa.
Hakan nafaruwa ne sabida toshewar Magudanar jini a masu sickla.wannan anfi samunshi a yara kananu.
5. Yawan yin laulayi ( rashin lafiya ).
Masu sikila kanyi fama da yawan laulayi da Rashin lafiya sabida matsalar karancin jini dasuke dashi ajiki.ayayin da jini yayi karanci ajiki,karfin garkuwar jikima Kan ragu,hakan zaibawa kwayoyin cuta damar shigowa cikin jiki su haddasa ciwo.
masu wannan ciwo kanfuskanci matsala a saifar su"spleen",wadda ba karamin taka rawa take ba awajen kare mutun daga cututtuka.
Wannan dalili yasa kodayaushe suke cikin Rashin lafiya.
Dan haka ne likitoci kanyiwa Yara masu Cutar rigaakafi tare da dorasu akan magunguna(antibiotics) da zai karesu daga cututtukan da za su iyayimusu barazana ga rayuwarsu(Kamar nimoniya).
6. Rashin girma / balaga da wuri
A lafiyyayyen mutun aikin kwayar halittar jini ne Kai iska da sinadaran Gina jiki zuwa sassa daban daban najiki,Dan haka alokacin da mutun ke fama da karancin jini a jiki akansamu tawaya wajen Kai wadannan sinadarai sassa daban daban na jikin,hakan kansa masu sickla Rashin girma.
7. Matsalar idanu ( rashin gani da kyau)
Akansamu wannan matsala ne sabida toshewar Magudanar jini dake Kai jini da sinadarai zuwa Ido a masu Cutar sickla.wannan dalili kansa su Samu matsalar gani.
8.Kumburin ciki
Hakan nafaruwa ne sabida kumburin hanta da saifa"spleen" dake faaruwa amasu Cutar.
Abubuwan dake tada ciwon sikila(crises)
Abubuwan dakan iya janyo masu Cutar su Samu "crisis" sunkunshi;
Shiga cikin sanyi
Rashin shan ruwa akai akai
Damuwa
Aikin wahala
Cuta musamman sanyi ko malaria.
Yana da kyau da duk me wannan cuta yayi kokari yakiyaye kansa daga wadannan abubuwan.
Yaushe yakamata kaga likita?
Ziyartar likita yazamanto anayinshi akai akai,sannan alokacin da aka ga daya daga cikin alamomin nan to maza a garzayo asibiti domin tallafin gaggawa.
Daga ciki akwai: zazzabi, tsananin ciwon kashi da gabbai, kumburin hannu da kafa, ciwon ciki, kumburin ciki, dashewar fatar jiki, daukewar magana, ko tsananin ciwon kai, dashewar saman farce, rashin kwari a wani bangare na jiki.
Illolin da ciwon sikila ke janyowa
1. Mutuwar barin jiki
Daga cikin manyan illolin da ciwon sikila ke janyowa shine mutuwar barin jiki.musamman idan ba a kula dashi sosai yadda yakamata
2.Matsaloli a kirji
Ta kan iya haifar da matsala a kirji ( chiwon kirji(acute chest syndrome), nimoniya tare da zazzabi da kuma daukewar numfashi ).
3.Makanta
Cutar sikila takan iya jawo makanta, mutun ya rasa ida nun sa gaba daya.
4. Gyan bon kafa
Ciwon sikila na iya janyo gyanbon kafa da lalacewar kafa Baki daya in ba a kula dashi yadda yakamata
6.Matsala a mata
Ga mata masu juna biyu, takan haddasa hawan jini, bari ko ahaifo yaro bakwai ni.
7.Matsaloli a koda
Cutar sikila kan iya janyo sanyin mafitsara,zubar jini acikin fitsari,ciwon Koda maza, ta kan janyo sandarewar mazakuta ta ki kwanciya, wanda hakan zai iya janyo rashin haihuwa.
8.Matsaloli a Kashi
Cutar sikila Kan iya janyo sanyin Kashi(osteomyelitis) da saurin karayar kashi.
9.Matsaloli a zuciya
Cutar sikila Kan iya janyo cuttuka na zuciya Kamar cardiomyopathy,ishchaemic heart dz,corpulmonale da ciwon zuciya(ccf).
Shawarwari dazasu taimaka
1.Hanya daya da za’a magance yaduwar wannan ciwo shi ne, yin gwaji na cutar sikila kafin ayi aure.
2.Duk mutumin dake dauke da wannan cuta yaakamace shi dayayi kokarin Kare kansa daga yanayi na sanyi ,yawan Tara gajiya, cututtuka, ko Hawa guri Mai tsayi sosai.
3.Yana da kyau agareshi da ya runka Shan ruwa sosai,yazamanto yana zuwa ganin likitaa akai akai tare da Shan magunguna na Karin jini(folic da hydroxyurea),magungunan Kara karfin garkuwar jiki(Kamar vitamin c),hakazalika yana da kyau da ya dage wajen Shan magungunan da zasu Kare shi daga malaria(watoh proguanil) da nimoniya(ta hanyar karban rigaakafi na
pentavalent da pneumococcal vaccines),abun lura anan shine wadannan magungunan suzamanto anashansu akarkashin kulawar likita.
4.Karin jini akai akai(chronic blood transfusion with hbAA blood) bayan kowanne sati shida zaitaimaka sosai wajen bada kariya ga kamuwa da Cutar paralisis(stroke) musamman a Yara.
Yawan yin fitsari alamace da kada kayi wasa da ita
Yawan yin fitsari,alamace da kada kayi wasa da ita
Yawan fitsari alamane na cututtuka dayawa musamman na mafitsara.
Mutun mai lafiya bayayin fitsari sama da sau 6-8 a rana.idan yawuce haka,ko mutun yana tashi sama sau 3 da daddare toh yazama matsala Kuma alamane na rashin lafiya
Yawan Shan ruwa,nescafe ko barasa kan janyo wannan matsala,Kuma hakan bazai zamanto abun damuwa ba,Shan ruwa abune mai kyau ga lafiyarka da jikinka,saidai giya da nescafe Wanda Basu da wani amfani ga lafiya.
Daga cikin abubuwan dake kawo Yawan fitsari sune:
1.Sanyin mafitsara
sanyine dake shafar mafitsara,alokacin daka kamu da wannan sanyi zaka runka fitsari ne sosai ba dare ba Rana, wani sa'in zakanajin zafi lokacin fitsari ko ganin jini acikin fitsarin.
2.Ciwon siga:
ciwon siga na dagacikin cututtukan dake janyo yawan fitsari,mutun na kamuwa da wannan ciwo ne alokacin da siga acikin jikinsa ta hau hawa sosai.bayan yawan fitsari mutun kan fuskanci Jin kishirwa sosai,yawan shan ruwa da rama.ciwon siga nada matukar illa ga jiki,Yana janyo ciwon zuciya,shanyewar barin jiki, cututtuka na magudanar jini,makanta da dai sauransu
3.Juna biyu
yawan fitsari nadaga cikin alamomin juna biyu a mata.Alokacin da kikayi batan wata sannan Kuma kina yawan fitsari toh kifara tunanin ciki
4.Ciwon BPH
kowanne da na miji yana da 'prostrate' acijikinsa wanda yake taimakawa wajen samar wa "sperm cells" sinadaran da suke bukata domin yin aikinsu.
alokacin da shi prostate yafara kumbura,mutun kan fuskanci wannan matsala ta yawan yin fitsari.Amafi yawancin mutane shi wannan prostrate din nafara kumburane alokacin da mutun yawuce shekaru 40.Abubuwa dayawa kan janyo shi Wanda zamuyi bayaninsu a wani rubutun namu.
5.prostatitis
Prostatitis sanyi ne na shi prostrate,yakanzo da zafin fitsari,ciwon dubura bayan yawan fitsari
6.Ciwon shanyewar barin jiki
Ciwon shanyewar barin jiki nadaga cikin abubuwan dake kawo Yawan fitsari,a masu wannan ciwo marar su da duburar su kan saki sukasa rike fitsari ko kashi,Wanda hakan zaisa fitsari ko kashi yarunka fitowa dakansa.
7.Daukewar al'ada ta manyanta
Alokacin da mace tawuce shekaru 50,zata iya fuskantar wannan matsala ta yawan fitsari, watoh alokacin da al'adar ta ta manyanta ta dauke
8.Fibroid
Fibroid ko tsiro acikin mahaifa nadaga cikin abubuwan dake iya kawo Yawan fitsari,yakanzo da azababban ciwon mara da zubar jini sosai.
9.kansar prostrate
Kansar prostate daji ne da prostrate,yakan kama mutun alokacin dayakainahekaru samanda 70,daga cikin alamominsa shine yawan fitsari,yawan Jin matsin fitsari,rashin iya rike fitsari,ciwon baya da dai sauransu.
10.Kansar mara
Kansar mara ko daji na mara daga cikin abubuwan dake kawo Yawan fitsari,mutanen dasukafi kamuwa da wannan matsalar sune masu aiki a kampaninnika na kemicals,ko Wanda suke yawan samun sanyi na fitsara.
13.Magunguna
Shan magunguna irinsu magungunan hawan jini kan janyo wannan matsala ta yawan fitsari
Meyakamata mutun yayi
Idan kana fama da wannan matsala yanada kyau kaje asibiti a gano meke kawo maka wannan matsala da wuri domin magance ta,rashin magance wannan matsala na iya janyo wa mutun wadansu cututtuka daban Wanda maganinsu nada matukar wahala(misali sanyin fitsari na janyo ciwon Koda)
Likita zai iya baka wadannan gwaje gwajen:
1.Gwajin siga
2.Gwajin mafitsara
3.Gwajin ciki
4.Hotan ciki
Magani yadanganta da abunda yake kawoshi Kuma asibiti ake bayarwa bayan likita yamaka tamboyi da gwaje gwaje
Yawan yin fitsari alamace da kada kayi wasa da ita
Yawan yin fitsari,alamace da kada kayi wasa da ita
Yawan fitsari alamane na cututtuka dayawa musamman na mafitsara.
Mutun mai lafiya bayayin fitsari sama da sau 6-8 a rana.idan yawuce haka,ko mutun yana tashi sama sau 3 da daddare toh yazama matsala Kuma alamane na rashin lafiya
Yawan Shan ruwa,nescafe ko barasa kan janyo wannan matsala,Kuma hakan bazai zamanto abun damuwa ba,Shan ruwa abune mai kyau ga lafiyarka da jikinka,saidai giya da nescafe Wanda Basu da wani amfani ga lafiya.
Daga cikin abubuwan dake kawo Yawan fitsari sune:
1.Sanyin mafitsara
sanyine dake shafar mafitsara,alokacin daka kamu da wannan sanyi zaka runka fitsari ne sosai ba dare ba Rana, wani sa'in zakanajin zafi lokacin fitsari ko ganin jini acikin fitsarin.
2.Ciwon siga:
ciwon siga na dagacikin cututtukan dake janyo yawan fitsari,mutun na kamuwa da wannan ciwo ne alokacin da siga acikin jikinsa ta hau hawa sosai.bayan yawan fitsari mutun kan fuskanci Jin kishirwa sosai,yawan shan ruwa da rama.ciwon siga nada matukar illa ga jiki,Yana janyo ciwon zuciya,shanyewar barin jiki, cututtuka na magudanar jini,makanta da dai sauransu
3.Juna biyu
yawan fitsari nadaga cikin alamomin juna biyu a mata.Alokacin da kikayi batan wata sannan Kuma kina yawan fitsari toh kifara tunanin ciki
4.Ciwon BPH
kowanne da na miji yana da 'prostrate' acijikinsa wanda yake taimakawa wajen samar wa "sperm cells" sinadaran da suke bukata domin yin aikinsu.
alokacin da shi prostate yafara kumbura,mutun kan fuskanci wannan matsala ta yawan yin fitsari.Amafi yawancin mutane shi wannan prostrate din nafara kumburane alokacin da mutun yawuce shekaru 40.Abubuwa dayawa kan janyo shi Wanda zamuyi bayaninsu a wani rubutun namu.
5.prostatitis
Prostatitis sanyi ne na shi prostrate,yakanzo da zafin fitsari,ciwon dubura bayan yawan fitsari
6.Ciwon shanyewar barin jiki
Ciwon shanyewar barin jiki nadaga cikin abubuwan dake kawo Yawan fitsari,a masu wannan ciwo marar su da duburar su kan saki sukasa rike fitsari ko kashi,Wanda hakan zaisa fitsari ko kashi yarunka fitowa dakansa.
7.Daukewar al'ada ta manyanta
Alokacin da mace tawuce shekaru 50,zata iya fuskantar wannan matsala ta yawan fitsari, watoh alokacin da al'adar ta ta manyanta ta dauke
8.Fibroid
Fibroid ko tsiro acikin mahaifa nadaga cikin abubuwan dake iya kawo Yawan fitsari,yakanzo da azababban ciwon mara da zubar jini sosai.
9.kansar prostrate
Kansar prostate daji ne da prostrate,yakan kama mutun alokacin dayakainahekaru samanda 70,daga cikin alamominsa shine yawan fitsari,yawan Jin matsin fitsari,rashin iya rike fitsari,ciwon baya da dai sauransu.
10.Kansar mara
Kansar mara ko daji na mara daga cikin abubuwan dake kawo Yawan fitsari,mutanen dasukafi kamuwa da wannan matsalar sune masu aiki a kampaninnika na kemicals,ko Wanda suke yawan samun sanyi na fitsara.
13.Magunguna
Shan magunguna irinsu magungunan hawan jini kan janyo wannan matsala ta yawan fitsari
Meyakamata mutun yayi
Idan kana fama da wannan matsala yanada kyau kaje asibiti a gano meke kawo maka wannan matsala da wuri domin magance ta,rashin magance wannan matsala na iya janyo wa mutun wadansu cututtuka daban Wanda maganinsu nada matukar wahala(misali sanyin fitsari na janyo ciwon Koda)
Likita zai iya baka wadannan gwaje gwajen:
1.Gwajin siga
2.Gwajin mafitsara
3.Gwajin ciki
4.Hotan ciki
Magani yadanganta da abunda yake kawoshi Kuma asibiti ake bayarwa bayan likita yamaka tamboyi da gwaje gwaje
Hanyoyi 5 dazakabi Dan samun lafiyayyan bacci
Rashin samun bacci na da matukar illa ga lafiya,yakan iya janyo cututtuka na jiki Dana kwakwalwa.
Domin samun lafiyyayan bacci,kayi wadannan Abubuwa:
1.Tsaida lokacin bacci da tashi.
Idan kana San samun lafiyyayan bacci,Yana da kyau ka Saka tsayayyan lokacin bacci da tashi akullun.idan kana kwanciya karfe Tara na dare sannan kana tashi 5 na safe,toh yazamanto kullun kanayin haka.
2.Samun bacci na akalla away shida
Akullun ana bukatar kasamu bacci na akalla awa 6,Rashin yin hakan na iyayiwa jikinka illoli daban daban
3.Kashe haske lokacin da zaka kwanta bacci
Kwanciya da haske na iya janyo maka rashin samun wadataccen bacci Wanda zaisa jikinka ya huta kafin safiya,akalla ana so ka kashe wutar dakinka ko kayi nesa da wayar ka awa daya kafin kayi bacci.
4.Kada kasha nescafe ko coffee
Nescafe da coffee na dauke da sinadarin caffeine wanda ke Hana bacci,Dan haka ba abune mai kyau ba inza ka kwanta kasha wadannan abubuwa.
5.Banda motsa jiki
Motsa jiki abune mai kyau ga lafiyar ka,Amma anfiso ayishi alokacin da yadace kamar da safe ko yamma.motsa jiki dad da zaayi bacci bashida wani amfani Kuma zai iya Hana ka samun lafiyyayan bacci.
Cututtuka na barci
Barci na daga cikin abubuwan da muke yi domin rage radadi da damuwa ta yau da kullum. Rashin yin barci ko fama da cututtuka da suka danganci barci na da matukar hadari sabida zasu iya sa mutun ya samu damuwa cikin kwakwalwa.
Cutar barci cutace da ta shafi kwakwalwa, wanda me fama da wannan ciwo ze na fama da rashin barci, yin barci fiye da kima, ko kuma barci alokacin da be da ce ba.
Ire iren ciwon barci.
1. Insomnia(karancin bacci)
Insomnia na nufin rashin barci.
Alokacin da mutun yake dadewa kafin yafara bacci yayin da ya kwanta ko yake yawan farkawa cikin bacci yana toh Yana fama da wannan ciwo.
Duk kokarin da mutum ze yi dan ganin yayi barci da dare sai kaga abun ya ci tura.
Ana tabbatar da cewa mutun na fama da wannnan ciwo ne alokacin dayakai wajen tsahon wata guda yana fama da ciwon.
Abun dake kawo wannan matsala.
Yawancin abunda ke janyo wannan matsala sunkunshi:
ciwon damuwa (depression),
ciwon hauka,
ciwon fargaba (anxiety disorders)
Rashin daidaita takamaimai lokacin farkawa da tashi daga bacci.
ciwon jiki
cutar sarkewar numfashi ta manya.
karancin sinadarin iron
cutar thyroid
ciwon parkinson
shaye shayen miyagun kwayoyi
2. Hypersomnia (ciwon yawan bacci)
Duk wanda ke fama da wannan ciwo yana yawan yin bacci fiye da kima,ana tabbatar wa mutun yana da wannan matsalar ne idan yakasance yawuce tsahon wata guda yana fama da wannan matsala.
abubuwan da ke jawo wannan ciwon:
Ciwon damuwa (depression),
Rashin takamaiman lokacin kwanciya ko tashi daga bacci(dadewa chatting ko yin game cikin dare),
Fama da lalura ta dadaddan lokaci.
Shan magungunan saka barci Kamar "long acting benzodiazepine".
3. Narcolepsy.
Mutanen dake fama da wannan ciwo na yin barci ne in da be kamata ba, wato sukan iya barci a ko ina cikin taro ne ko makamancin haka. Ma'ana barci yakan iya kufce musu a kodayaushe kuma a ko wanne irin yanayi. Sukanyi gyan-gyadi ko da acikin dakin taro ne.
Anasamun wannan matsalar ne alokacin da sinadarin "hypocretin" Wanda yake kula da bacci acikin kwakwalwa yayi yawa.
Alamomin Cutar
Yawan Jin bacci.
Gane gane yayin kwanciya bacci.
4.Tafiya yayin bacci.
Tafiya yayin bacci cuta ce ta bacci,anfi samun wannan matsalar a Yara(Yan Shekaru 4-8) da Samari.
Alamomin wannan cuta
mutun yakan tashi yayi tafiya cikin barci batare da yasani ba(wani sa'in zai ta yawo acikin gida koma yafita waje batare da yasani ba ko Kuma yayi ta kokarin cire Kaya ko sakawa duk cikin magagin bacci)
idan suka farka alokacin da suke wannan magagin sukan tsorata su firgice wadansu ma suyi ta ife ife.
yawanci basa tuna wannan magagin tafiyar dasukayi idan suntashi da safe.
5.Yin mugun mafarki da firgata yayin bacci.
Amfi ganin wannan ciwo a yara Yan Shekaru 5 zuwa 6.Mutun yakan iya yi mugun mafarki Wanda zaisa ya firgita sosai.Duk Wanda yake fama da wannan matsala yanada kyau yaje yaga likita domin rubuta Mai magani.
Shawarwari.
Ga masu fama da karancin barci ka da su na yawan barcin rana, sannan suna kwanciya waje maras hayaniya sannan a kashe fitila. Rage damuwa, firgici ko bacin rai kan taimaka sosai wajen shawo kan matsalar. A daina ta'ammali da miyagun kwayoyi, ko magungunan saka barci.
Akiyaye: shawara mafi inganci shine, idan kana/kina fama da daya daga cikin wadannan cututtukan na barci, ayi hanzarin ziyarta likitan kwakwalwa domin magani.
Abubuwan dazasu sa kakamu da Farfadiya
Abubuwan dazasu sa kakamu da Farfadiya
Cutar farfadiya cutace da ta ke sa mutun jijjiga, tana zuwa tare da yin wasu dabiu na daban da fita daga hayyaci.
abubuwan da ke kawo wannan cuta ta farfadiya su ne kamar haka:
1.Gado
Ana iya samun Cutar farfadiya ta hanyar gadonta daga dangi watoh alokacin da wani acikin iyayen ko dangi yake fama da wannan ciwo
2. Matsalar cikin kwakwalwa.
Matsalolin cikin kwakwalwa kamar su kansa ko tsiro acikin kwakwalwa da cutar shanyewar barin jiki kan iya jawo wannan cuta ta farfadiya.
3. Buguwa a kai
Buguwa a kai sanadiyar hadari ko wani abun kan iya kawo cutar
4. Cututtuka na infection
Cututtuka kamar irinsu sankarau,Kanjamau dasauransu kan iya haifar da wannan cuta.
5. Matsaloli lokacin haihuwa.
Jariran da suka Sha wahala wajen haihuwa,ko suka sha ruwan nakuda,da Wanda basuyi kuka ba lokacin da aka haifesu,ko Wanda sukayi zazzabi, idansu yayi ruwan dorawa ko wata cuta ta shigesu.
Hakazalika wadanda akasamu taruwar jini da ruwa a cikin kwakwalwarsu ko kuma yaro aji masa ciwo a kai yayin fito da shi duk kan iya haddasa wannan cuta.
Alamomin cutar farfadiya.
1. Rikicewa
2. Kafewar idanuwa su kalli sama
3. Jijjiga (musamman kafa da hannu).
4. Fita daga cikin haiyaci.
5. Alamomin firgici da tsoro yayin fara farfadiya
6. Ganin walkiya ko haske yayin far farfadiya.
7. Yin amai, gudawa ko fitsari alokacin farfadiya.
8. Jiri da hajijiya.
Yaushe ya kamata a ga likita.
A nemi taimakon gaggawa dazarar anga daya daga cikin wadannan alamomi
1. Daukewar numfashi ko fita daga hayyaci bayan angama farfadiyar.
2. Jijjiga ko farfadiyar da ta wuce minti 5
3. Yin jijjiga ko farfadiya sama da sau daya a lokaci guda.
4. Zazzabi me zafi.
5. Macen da tai / take farfadiya alhanin tana da juna biyu.
6. Masu ciwon siga.
7. Wadanda suka ji ciwo ko suka bugu sosai bayan gama farfadiya.
Matsalolin da cutar farfadiya kan haddasa.
1. Faduwa, wanda hakan kan iya janyo karaya ko buguwa a kai
2. Masu cutar farfadiya wadanda suke shiga ruwa domin iyo ko wasa, akwai yuwar zasu iya nitsewa cikin ruwa idan farfadiya ta kamasu a ciki
3. Hadari yayin da suka Fara farfadiyar lokacin tuki.
4. Matsala na wajen haihuwa (ga uwa ko yaro)
5. Shiga matsalar damuwa (depression), wasu ma kan tunanin kashe kansu (suicide)
Hanyoyi 6 dazakabi ka kare kanka daga makanta cikin sauki
Hanyoyi 6 dazakabi ka kare kanka daga makanta cikin sauki
Amfanin ido shine karunka Gani dashi,Kuma Gani shine rayuwa,alokacin da aka ce baka ganin komai kashiga yanayi mafi wahala a rayuwarka.
Akwai hanyoyi dazakabi cikin sauki domin kare kanka daga makanta
Yadda zaka kare kanka
1.Karunka cin abinci mai kyau
Cin abubuwa masu kyau na da matukar amfani wajen kare Kai daga makanta,duk da dai rayuwa ta Yi tsada bakowa zai iya siyan wadannan irin kayayyakin abincin ba.akwai Wanda zaka iya samu cikin sauki batare da ka kashe kudi sosai ba kamar
Yawan hada abinci da wake
Cin gyada
Saka Karas acikin abinci
Yawan cin alayyahu da ganyayyaki
Shan lemon Zaki Koda sau daya ne a Rana ko lemon tsami
Cin kwai akai akai Koda kuwa ba kullun ba
2.Rage kallan waya
Allah yakawo mu zamanin da amfani da waya ya zamemana dole,akodayaushe Muna tare da wayarmu a hannu,idan kana yawan amfani da waya ko kompiyuta,Yana da kyau ka runka daukan hutun sakan ashirin bayan kowanne minti ashirin,ko ka runka daukan hutun minti goma Sha biyar bayan kowanne awa biyu dakayi kana amfani da wayarka.
Illar yawan amfani da waya batare da hutu ba sun hada da bushewar ido,Jan ido,kaikayin ido,raguwar karfin ganin ido,ciwon Kai,ciwon wuya da baya da sauransu.
3.Motsa jiki akai akai
Motsa jiki akai akai Koda yar tafiya ce ta minti talatin arana zai tàimaka maka kwarai wajen Kara karfin ganinka ta hanyar kareka daga cututtukan ido dazaka iya samu daga hawan jini,ciwon siga ko kolesterol
4.Gujewa Shan taba
Shan taba nayiwa ido mummunar illa ta hanyar kashe maka jijiyar dake kula da Gani a ido da janyo wash cututtukan ido irinsu cataract.Daina Shan taba alokaci daya nada matukar wahala kwarai da gaske Amma ahakan zakayi kokari kadaina Koda kuwa zaka shiga wani irin yanayi,akullun ka runka tunawa lafiyar jikinka itace dai farko
5.Amfani da tabarau na ido
Amfani da tabarau nataimakawa sosai wajen Bada kariya daga mummunar lahanin d hasken Rana kewa ido,a duk lokacin da zaka fita waje saika dauko tabaranka kasaka.
6.Zuwa ganin likita akai akai
Yana da kyau ka runka zuwa ganin likitan ido akai akai ana duba lafiyar idonka domin kuwa akwai cututtuka musamman irinsu glaucoma da Basu da wata alama dazai nuna kana dauke da ita,amafi yawanci a gwaje gwajen likita a ke gano ta,Dan haka yana da kyau karunka zuwa akai akai ana duba maka lafiyar idanunka a asibiti.
Abubuwa guda 6 da mai olsa yakamata ya nisanta
Abubuwa guda 6 da mai olsa yakamata ya nisanta
Alokacin dakake fama da olsa akwai nauikan abincin da Bai kamata kanaci ba.
Cin su na Kara tsananta ciwon ko ya tayar da olsa din
Alamomin olsa dai sunkunshi:
Zafin kirji: shine mafi muhimmancin alama kuma wanda yawancin mutane sukafi zuwa dashi.
Zafi ko ciwon wuya da makogaro.
Ciwo ko zafin ciki musamman saman cibiya kamar ana hura maka wuta a cikin.
Ciwon baya
Yawan gyatsa
Aman jini awani sa'in musamman intayi kyamari.
Bayan gida hade da jini ko yin bayan gida mai kalar baki
Kasala da yin Numfashi da kyar awani sa'in
Wadannan abinci sunkunshi:
1.Shan madara
Sabon bincike yanuna cewa; madara nadaga cikin abincin dake tayar da olsa sabida yawan sinadarin 'fat' dake dauke da shi.
Hakazalika shan kindirmo na kara bada damar samarda shi acid din wanda yake qara tsanantar cutar
2.Cin soyayye ko gasasshen Abu
Cin soyayyan abinci nadaga cikin abubuwan da ke tada ko kata tsanantar olsa sabida taimakawar dasuke wajen Kara Samar da sinadarin acid aciki Wanda shine makasudin Samar da ciwon olsa.
3.kauracewa Cin Abu mai yaji
Abinci masu yaji ba abune na mai olsa ba,ko mutun zai na cinsa,sai yarunka ci kadan kadan,yaji na daga cikin abunda ke tada olsa kamar yadda cin Abu mai maiko ko tsami keyi.
4.Giya/Barasa
giya na lalata ciki dakuma duk wani sassa dake taimakawa wajen niqa abinci acikin cikin. Hakan yana kara tsannatar olsa
5.coffee dakuma lemon roba ko kwalba
Shan Coffee da lemo na kwalba na qara tsanantar olsa ta hanyar taimakawa wajen samarda sinadarin acid.
6.shan tabar shigari
Shan tabar shigari yana haifarda matsaloli dadama wa lafiya. Aciki harda tsananta cutar olsa.
Kiyaye wadannan nauikan abincin zai tàimaka kwarai wajen magance wannan ciwo na olsa idan aka hada da magunguna da aka bayar asibiti
Hanyoyi 4 dazakabi ka karawa kanka jini cikin sauki
Hanyoyi 4 dazakabi ka karawa kanka jini cikin sauki
Jikinmu na bukatar wadataccen jini domin gudanar da ayyukansa na yau da kullun Daga cikin aikin da jini keyi ajiki shine zagayawa da duk wani sarrafaffen abinci dakuma sauran sinadarai zuwa kowani kwayan halitta dake cikin jiki. Alokacin da jinin jikinmu yazama yayi kasa, to lallai hakan zaisa sassan jikinmu sukasa gudanar da aikinsu yadda yadace.
Akwai abinci dadama dasuke kara yawan jini ajiki yayinda muka kasance masucinsu.
1.Abinci masu dauke da sinadarin iron
Jinin jikinmu yana daukeda sinadarin iron mai tarin yawa. Shiyasa cin abinci dake dauke da sinadarin iron din yake kara yawan jini ajikinmu. Misalansu yahada da;
kifi
Hanta ko Koda
Madara
Fura da nono
Jan nama
Kwai
naman tsuntsaye kamarsu kaji
wake
sauran abinci da ake samosu daka kogi.
2. Abinci masu dauke da sinadarin folic acid
Cin abinci masu dauke da sinadarin folic acid na tàimakawa kwarai wajen Kara jini ajiki.wadannan abincin sunkunshi:
Kwai
Alayyahu
Wake
Lemon Zaki ko tsami
Ayaba
Hanta
Alayyahu
3.Abinci masu dauke da sinadarin vitamin c
timatir
lemon Zaki ko na tsami
Wadannan abinci Sukan taimakawa jiki yasamu hanzari wajen zuko kokuma tsamo sinadarin iron daga cikin abinci. Hakan yana nufin bayan kaci wadancan abincin masu Kara iron, yanada kyau kahada da wadannan masu daukeda sinadarin vitamin c din.
4.Abinci masu dauke da sinadarin vitamin B12
Wadannan abincin suna karawa mutum jini ajiki, tahanyar samarda sabbin jini daga qashi ( bone marrow).
Misalinsu yahada da
Jan nama
naman tsuntsaye (kaji)
Kwai
Alayyahu
Wadannan abubuwa dayawa abinci ne dazaka iya samu cikin sauki.cin abinci masu Kara jini ajiki nada matukar muhimmanci wajen Gina jiki da inganta lafiya.
Gurbacewar ciki bayan cin abinci(food poisoning)
Gurbacewar ciki bayan cin abinci(food poisoning)
Gurbacewar ciki na faruwa sakamakon cin abinci Wanda ke Dauke da kwayoyin chuta ko Kuma cin abinda Wanda ke Dauke da sinadarai Wanda kwayoyin chuta suka samar. Gurbacewar ciki Abu ne Wanda ke illar ta da mutane musamman ma yara, masu ciki, da tsofaffin, wasu lokutan gurbacewar ciki na iya Barazana ga rayuwar mutum.
Alamomin ta sun HaDa da;
Gudawa
amai
ciwon ciki
zaxxabi.
Akwai rashin lafiyoyi da dama wanda ke da irin wannan alamomin. yadda ake Gane ce wannan alamomin sun faru ne sakamakon cin abinci shine.
Faruwar wannan alamomi lokaci kadan bayan Gama cin abinci.
Wasu Wanda suka ci wannan abincin suma susami kalar wannan alamomin.
Shidai abinci Wanda ke Dauke da kwayoyin chuta ba Gane shi ake ta ido ko DanDano ba Dan Haka Abu Mai mahimmanci shi ne a Guji abubuwa Wanda ka iya kawo kwayan cutan cikin abinci.
Yadda zaa kare kai
Ayi kokari wajen wanke duk wani abu da aka San za ai amfani dashi gun cin abincin kamar hannu, kwanuka da sauransu.
Duk abunda za aci atabbatar ya Dahu sosai.
Duk abincin da aka San za aDau lokaci kafin acishi ayi kokari wajen sashi cikin fridge Wanda aka San Yana aiki
Akwai wani abu da alikitance muke chema cross contamination Wanda ke nufin misali ayi amfani da wuka wajen yanka Danyar Doya Sannan ayi amfani da wannan wukar wajen yanka doyar bayan ta Dahu, ana so ya zamto duk abunda akai amfani da shi aDanye bashi za ai amfani dashi ba bayan abun ya Dawu.
Abunda mutum zai yi inya kamu ko wani nashi ya kamu shine, babban abunda ke illatar da mutane shine wannan ruwan da mutum ke rasa ajikin sa sakamakon amai da gudawan, don haka abun da yafi mahimmanci shine duk amai ko Gudawa Guda Daya in mutum yayi ayi kokari ahaDamasa ruwan gishiri da siga abashi yasha yadda zai koshi, Haka za atayi har akai shi zuwa ga asibiti. Daya wa mutane kafin akawo su asibiti sun galabaita wasu ma sun Fi ta daga hayyacin su sakamakon ruwan da suke rasa wa Kuma ba amayr musu dashi ta hanyar ruwan gishiri da sigan.
Cutar Yawan fargaba da Tsoro
Cutar Yawan fargaba da Tsoro
Cutace dake sa mutun yawan fargaba akan abun da zai faru anan gaba.Mutun yakan tsinci kansa acikin matsanancin zullumi da fargaba.
A kalla 40% na masu ganin likitan kwakwalwa suna dauke da cutar. Bincike ya nuna a kalla 50% na yan shekara 11 suna iya samunta wanda 80% na masu shekara 20 zuwa sama suna iya kamuwa da ita.
Anfi ganin wannnan cuta a mata akan maza.
Abun dake kawo ta
Babu takamaimai abinda yake kawo ta sai dai tana sababai wanda suka hada da:
Takurarriyar yarinta
Karancin arziki
Samun me irin cutar a dangi
Ana samun wannan matsalar ne alokacin da sinadaran kwakwalwa irinsu norepinephrine,serotonine,gaba,glutamate suka samu matsala.matsaloli a caudate nucleus,amygdala,da hippocampus kan janyo wannan matsala.
Ire Iren wannan ciwon
1.faduwar gaba.
wannan Yana zuwa acikin kankanin lokaci alokacin da mutum yana cikin bacin rai ko ma yana cikin kwanciyar hankali wani sa'in,mutun zai fuskanci alamomi kamar haka:
bugun zuciya da karfi
yawan gumi
bari da kakkarwa
ciwon kirji ko shakewa
ciwon ciki da amai
jin jiri
jin kamar
jin kamar komai ba gaske bane ko jin kamar mutun ba ajikinsa yakeba.
tsoron mutuwa.
2.Fargaba alokacin da mutun ya shiga taron jama'a.
Mutanen da ke fama da wannan nau'in ciwo na fargaba ne tsoron shiga taron jama'a.
Aduk lokacin da mutun yashiga jamaa yakan rasa samun sukuni da nutsuwa,hakan kansa mutun kin shiga cikin jama'a.
3.fargaba na abubuwan dake muhalli.
wannan yana da alaka da tsananin fargaba ga wasu abubuwa da suke kusa da mutum a muhalli wanda yakan iya ganin su lokaci bayan lokaci.wadannan abubuwan sun hada da dabbobi,jini da sauransu.Mutanen dake fama da wannan nau'in sukan shiga zulummi alokacin da suka ga daya daga cikin wadannan abubuwan.
misali matsanancin tsoro alokacin da mutun yaga kadangare,miciji ko yayin da mutun yahau gada ko bene.
Alamomin sa sun kunshi;
matsanancin tsoro alokacin da mutun yaga wani abu.
shiga cikin zullumi ta yadda wani sa'in mutun yarasa dailin haka
tsoron yakan hanashi gudanar da alamuran rayuwarsa.
4.fargaba da Damuwa sabida abinda mutane zasuce:
Mutun yakan shiga damuwa da fargaba sabida abunda mutane zasu fada idan ya aikata wani abu.wannan zaisa mutum yakiyin abin saboda kar ya jamasa kunya(misali tsoron yin magana a bainar jama'a)
5.Fargaba da tsoro akan duk wasu alamura na rayuwa.
mutanen dake fama da wannnan nau'in kan shiga cikin zullumi akan kusan komai na rayuwarsu kama daga aiki,auratayya,iyali,lafiya da sauransu.
Me yakamata mutun yayi?
Idan kana fama da wannan matsala,kasani cewa ba Kai kadai bane Kuma ana maganin ta a asibiti.
Akwai magunguna na tsoro da Wanda zasu cire maka damuwa da likita zai baka bayan ya tabbatar kana dauke da Wannan ciwo na fargaba.
Abubuwa guda 4 da tafarnuwa keyiwa jikinka idan kayi amfani da ita
Abubuwa guda 4 da tafarnuwa keyiwa jikinka idan kayi amfani da ita
Anan basai munbata lokaci wajen kwatance kwatancen tafurnuwa ba,kusan aba ce sananniya.
Na tabbata bayan karanta wannan Dan gajeran rubutun bazaka/kiso Rana daya tawuce batare da ka/kinyi amfani da itaba sabida dunbun ni'imar da albarkatu dayake tattare da ita.
Amafanin tafarnuwa ajikin Dan Adam
1.Amfaninta gamasu hawan jini.
Sababbin bincike yanuna cewa mutanen da ke cin tafarnuwa kimanin 600mcg zuwa 650mg a rana Kan iya samun daidaiton hawan jininsu Kamar yadda maganin hawan jini zaidaidaita musu shi!.
Hakazalika wandanda suke yawan cin ta akullun kansamu kariya daga kamuwa da hawan jini,harsashen wani bincike.
2.Maganin Mura.
Shin kana yawan fama da mura?bincike yanuna tafarnuwa kantaimaka wajen magance mura sosai.Idan kana fama da mura Fara cin tafarnuwa kafin Shan wani magani.
3.kariya daga kamuwa da ciwon zuciya.
Yawan amfani da tafarnuwa Kan taimaka wajen bada kariya da kamuwa da ciwon zuciya.yakan taimaka wajen rage yawan cholesterol a jiki da daidaita hauhawar jini.
4.kara tsayin rayuwa.
Bincike yanuna cewa mutanen dake yawan cin tafarnuwa sunfi dadewa a duniya idan ka kwatantasu da Wanda basaci.ita dai tafarnuwa na dauke da "antioxidants" dayawa wanda suke taimakawa kwayoyin halittar jiki yaki da wasu abubuwa dakan iya Cutar dasu watoh "free radicals".
Alamomi dake nuna jikinka na fuskantar karancin sinadarai
Alamomi dake nuna jikinka na fuskantar karancin sinadarai
Domin gudanar da aikinsa na yau da kullun yadda yakamata cikin lafiya,jiki na bukatar wasu sinadarai daga abinci dazai yi amfani dasu wajen gudanar da wadannan ayyukan.
Alokacin da baya samun wadannan sinadaran yakan fuskanci wasu matsaloli daka iya janyo wata cuta ko ciwo.
Daga cikin alamomin karancin sinadarai sunkunshi:
1.Alamomi a Gashin kai.
karancin sinadarai kamar su vitamin B12,B complex na iya sa tsistsinkewa da zubar gashi,furfura da wuri da dai wasu matsaloli na gashi.
2.Alamomi a ido
Idan idonka na yawan yin ja,ciwo,kwantsa,ko ganinka na raguwa,toh akwai yiwuwar kana fuskantar karancin sinadarai irin su vitamin A.akwai cututtuka na ido dayawa daka iya kawo maka wadannan alamomin,Dan haka ba karancin sinadarai ne kadai mai Saka wadannan abubuwa ba.
Cin Karas akai akai,kabewa,timatir,kwai,kifi,dankalin turawa,hanta da dai sauransu zai iya magance maka wannan matsala.
3.Alamomi A baki
gyanbon Baki da tsagewar Baki alamomune dake nuna cewa jikinka na fuskantar karancin sinadarai.
Gyanbo ko kurarrajin Baki na iya yiwuwa kana fuskantar karancin sinadarai kamar su vitamin c.
Abubuwan dazasu iya kawo maka wannan matsala bayan karancin sinadarai sunkunshi:Ciwon candidiasis,ciwon siga,ciwon hiv,yawan Shan magunguna na Sha ka fashe.
Zaka iya magance wannan matsala ta hanyar Shan kayan itace masu dauke da sinadarin vitamin c kamar lemon Zaki ko na tsami
4.Dashewar fuska.
Karancin sinadarai ajiki kamar su folic acid da vitamin B12 Wanda Ake amfani dasu wajen Samar da kwayoyin halitta na jini ka iyasa fuskanka ta dashe.dashewar fuska alamane na karancin jini ajiki.
5.Yawan kasala da ciwon jiki.
Hakan na iya nuni da cewa kana fuskantar karancin jini da sinadarai kamar su sodium,potassium,chloride da dai sauransu ajiki.
Zaka iya magance wannan matsala ta hanyar cin abubuwa kamar ayaba,kankana,kwai,Madara,nama,waken suya,shinkafa da dai sauransu.
6.Yawan ciwo ko zafi a kashin jiki
Yawan zafin Kashi na iya yiwuwa jikinka na fuskantar karancin sinadarai na calcium.
Zaka iya magance wannan matsalane ta hanyar cin abinci masu dauke da shi sinadarin kamar su Madara,awara,lemon Zaki,wake,wajen suya,kobewa,kwai da dai sauransu.
7.Raguwar kaifin basira
Alokacin dakake fama da karancin sinadarai,basirarka na iya raguwa.
Abincin dazasu tàimaka maka wajen Kara basira sunkunshi:kwai,kifi,kabewa,coffee,kayan Miya,man kwakwa,lemo,dark chocolate da dai sauransu.
8.Matsaloli na fata
Yaushi,bushewa da rashin kyan fata nada alaka da karancin sinadarai ajiki.
Cin abubuwa kamar kifi,kwai,man kwakwa,man zaitun,lemon Zaki,Karas,green tea duk na tàimakawa wajen gyaran fata.
9.Rashin girma
Rashin girma na daga cikin alamomin karancin sinadarai,alokacin dabakasamun isassun sinadarai da zasu Gina maka jiki toh ba makawa jikinka zai zauna inda yake ba cigaba
Yadda ruwa ke magani da Bada kariya ga wasu cututtuka
Shan ruwa sosai yana da matukar muhimmanci ga lafiyar dan adam,akalla ako wacce Rana yana da kyau mutun yarunka Shan lita uku zuwa hudu.
Anan zamuyi Dan kankanin tsokaci game da amfanin Shan ruwa sosai ajiki.
1.Amfanin sa ga lafiyar koda
Shan ruwa sosai yana rage yawan tsakuwar cikin koda a jikin wadanda daman tuni suke da ita.
Shan ruwa akai akai a Rana Kan kare mutun daga kamuwa da ciwon Koda musamman wadanda suke Zama a garuruwa masu zafi.
2.Amfaninsa ga kwakwalwa
Shan ruwa yana da matukar amfani ga kwakwalwa.yana taimakawa wajen Kara karfin kwakwalwa,nazari da tunani,sannan yakan taimaka wajen rage yiwuwar kamuwa da cututtukan tsufa mussaman cututtukan mantuwa.
3.Maganin ciwon kai
Bincike yanuna cewa yawan Shan ruwa Kan taimaka sosai wajan bada kariya da kuma warkar da ciwon kai.
Amafi lokuta karancin ruwa ajiki shike janyo yawan ciwon Kai da kasala,Shan ruwa akai akai Kan taimaka sosai wajen magance shi.
4. Yana sa shekin fata
Shan ruwa sosai yana gyara launin fata tare da sanyata walwa da walkiya,yakan hana fata bushewa da yin yaushi.
Duk mutumin da kesan fatarsa tarunka sheki sosai toh yakamaceshi da yarunka Shan ruwa sosai
5.Yana taimakawa wajen narka abinci dakyau.
Shan ruwa Kan taimaka wajen saurin narkar da abinci.musamman idan ana Shan shi minti 30 kafin cin abinci,ko da zarar mutun yatashi daga bacci.
6.Kariya da ciwon siga da hawan jini.
Bincike yanuna cewa mutanen dake Shan ruwa sosai suna da karancin kamuwa da ciwon siga da hawan jini idan aka kwatantasu da Wanda basa Sha.
7.Kariya daga ciwon Kansa ko daji
Bincike yatabbatar da cewa Mutanen dake Shan ruwa sosai nada karancin kamuwa da Kowacce iriyar kansa.
Shin kanaso ka kare kanka daga kansa? Toh ka Fara Shan ruwa akai akai.!!
8.Kariya daga ciwon zuciya
Shin kanasan Kare kanka daga ciwon zuciya? toh ka Fara Shan ruwa akai akai.
9.Rage kitse da teba ajiki.
Ga duk mutumin da kesan rage kiba toh yakamaceshi da yarunka yawan Shan ruwa musamman minti 30 kafin cin abinci.
Yanzu fada mana dalilin dayasa bazaka/ki runka Shan ruwa akai akai ba akullun!!!!
Sami Kofi ka debo ruwa kasha abunka,ruwa maganine!!!
Yadda zaka gano cutar dake kawo maka ciwon ciki Saman cibiya
Shin kana fama da ciwon ciki sosai sannan karasa ko me ke kawo maka wannan matsala ?
Ciwon ciki alamane na cututtuka dayawa.sannan wani sa'in yakanbukaci taimakon gaggawa Wanda idan ba adau mataki dawuriba kansa mutun yarasa ransa.
Dan haka idan kana fama da ciwon ciki kowanne iri karkasake kayi Wasa wajen Neman magani.
Yadda zaka Gane wacce cuta ke kawo maka ciwon ciki a Saman cibiya
Idan kana yawan fama da ciwon ciki daga saman cibiya,zai iya yiwuwa kana daya daga cikin wadannan cututtukan kamar:
1.ulsa
Ulsa nadaga cikin cututtukan dake kawo ciwon ciki sosai.mutun zainajin kamar ana busamai wuta a cikin cikinsa.sannan wani sa'in takanzo tare da ciwon baya.
2.Ciwon Gerd
Ciwon Gerd kanzo da ciwo ko zafin kirji.ciwon na tsananta ne alokacin da mutun yakwanta a kishingide, sannan Wani sa'in mutun zainajin Kamar abinci natsaya Mai a makogaro,masu wannan ciwo kan koka da yadda wani bakin su ke wari insunyi magana
3.(kansar ciki) Gastric cancer.
Wannan ciwon anfi ganinsa a masu Shekaru sama da 60,bayan ciwon ciki yakanzo da kumburin ciki,kasala,rashin San cin abinci da rama
4.Ciwon Duwatsun matsarmama.
Wannan ciwo na zuwa da :
Azababban murdawar ciki Wanda idan yafara mutun yakanjishi har zuwa bayan kafadarsa Sannan Idon mutun kan koma ruwan dorawa ko Kore(jaundice)
5.Ciwon kumburin matsarmama
Wannan ciwo Shima yakanzo da ciwon ciki tare da canzawar kalar Ido zuwa ruwan dorawa(jaundice)
6.kumburin saifa
Wannan ciwo kanzo da:
ciwon ciki Wanda mutun kanjishi har zuwa bayan sa.ciwon cikin kanyi sauki alokacin da mutun yazauna
7.Ciwon toshewar magudanar jini ta zuciya
Bayan ciwon ciki, yakanzo da:
Nauyin kirji ko Ciwon kirji sosai,mutun yakanji Kamar ana matse Mai kirji Ciwon kanyi yawo zuwa wuya,kafada da hannaye musamman na hagu,sannan yakan lafa idan mutun ya Dan huta
9.nimoniya
Mutun Mai fama da Nimoniya kanzo da tari,haki da zazzabi da ciwon kirji.
Meyakamata kayi?
Yakamata kaje kaga likita domin ayi cikakken bincike agano matsalar
Binciken da likita zai iyaba kayi Yadanganta da abun da likita ke tunanin shike kawo maka wannan matsalar.
1.upper GI endoscopy
alokacin da likita ketunanin ulsa,kansar makogaro da ciki ne ke kawo maka wannan matsalar.
2.ultrasound scan of gallbladder and biliary ducts
idan likita na zargin acute cholecystitis ko acute cholangitis.
3.ECG
alokacin daa likita ke tunanin matsalar zuciya ke kawoma ciwon cikin.
4.serum amylase da ultrasound scan of pancreas
idan likita na zargin acute pancreatitis.
5.Hotan kirji
domin ganin lafiyar zuciya da huhu.
6.full blood count
domin sanin ko mutun nada karancin jini a jiki.
7.E/UR/CR
Dan ganin lafiyar Koda
Magani yadanganta da Abun da likita yagano.
Illolin dake tattare da yawan cin gasasshen nama
Nama na daga cikin nauin abinci mai gina jiki da Kara lafiya. Yana daga cikin abinci dake dauke da sinadarin protein mai yawa.
Yanada kyau inzaka ci shi ka dafa shi.
Cin soyayye ko gasasshe bashi da wani amfani ga lafiya.
Gasasshen nama na dauke da sinadarai masu cutarwa waɗanda zasu iya ƙara haɗarin kamuwa da cututtukan daji watoh kansa.
Bincike na likitanci yanuna cewa mutanen dake yawan cin abincin da aka gasa ko aka Sarrafa shi da hayaki na iya janyo cututtuka dayawa.
Illolin shin gasasshen mana
Daga cikin illolinsa akwai cututtuka na daji,ciwon siga,shanyewar barin jiki,olsa da dai sauransu.
Ciwon kansar hanji da ciki : Yawan cin gasasshen nama nada alaka ga saurin kamuwa da kansar hanji musamman babban hanji da ciki abunda Bincike ya nuna. Kansar ciki nadaga cikin cututtukan daji dasukafi kashe mutane a duniya.
Ciwon olsa : Daga cikin abubuwan da Ke kawo olsa shine cin abunda aka fada ko aka Babb aka shi da hayaki. Hayaki nadaga cikin abubuwan dake yawan samar da acid acikin ciki. Idan kana da olsa yawan cin Abu mai hayaki na iya tada maka da ita.
Shanyewar barin jiki da ciwon siga: Yawan cin gasasshen Nama na iya janyo wadannan cututtuka na shanyewar barin jiki da ciwon siga da wasu cututtuka ma dayawa.
Yawan Cin Jan nama kadai shima nada nasa illolin,masana sundangantashi da cututtuka na zuciya,shanyewar barin jiki,kansar ‘prostrate’ a maza da dai sauransu.
Yakamata mu runka lura da abubuwan damukeci domin samun zama da jikin mu lafiya
Me ke sa rashin iya rike fitsari?
Wannan alamane na cututtuka dayawa.
Abubuwan dake kawo wannan matsala sunkunshi:
1.Sanyin mafitsara
2.Rashin karfi na tsokar mazaunin mafitsara da mahaifa a mata
3.Zazzagowar mahaifa a mata
4.Yoyon fitsari a mata
5.kumburin 'prostrate' a Maza
ME YAKAMATA KAYI?
Zuwa asibiti shine abun dayafi dacewa.alokacin dakaje asibiti ana iya baka gwaje gwaje kamar haka:
1.urine mcs
2.urinalysis
3.urodynamic studies
4.Ultrasound scan of prostrate
5.PSA
wannan gwaje gwajen zasu taimaka wajen gano asalin meke kawo wannan matsala,Wanda hakan zai tàimaka wajen magance ta.
Magani asibiti akeyi Kuma yadanganta da abun dake kawoshi.
YADDA ZAKA GANE KO KANA DA SANYIN MAFITSARA CIKIN SAUKI
Sanyin mafitsara sanyi ne dake shafar  mafitsara.kwayoyin cuta na bacteria ne ke Kawo wannan cuta.
A hakikanin gaskia wannan cuta anfi samunta a mata da Mutanen da mafitsarar su ta Toshe.
,Yin amfani da robar fitsari ( catheter ),wanke wajen Kashi kafin na fitsari,Saduwa da mutane daban daban duk Kan iya janyo wannan ciwo.
Hakazalikaa ana yawan samun wannan ciwon a matan da al'adar su tadauke,mutanen dake da Matsalar mafitsara tun lokacin haihuwa ( congenital ) da Wadanda ke fama da cututtuka masu karya garkuwar jiki Kamar ciwon kanjamau,siga,tarin fuka da yawan amfani da magunguna Kamar irinsu antibiotics.
YADDA ZAKA GANE KO KANA DASHI:
Idan har kana da wadannan Alamomin toh kana wannan cuta:
1.Yawan fita fitsari musamman da daddare(tashi sama da sau biyu acikin dare)
2.Jin Zafi yayin fitsari
3.Rashin iya rike fitsari idan ya matseka
4.Ganin jini a cikin fitsari
5.Ciwon ciki ko mara
6.Amai da tashin zuciya
7.Zazzabi
8.Ciwon kugu da baya da sauransu.
IllOLLIN DA SANYIN MAFITSARA ZAI IYA JANYO MAKA
1. Ciwon koda : Ciwon Koda nadaga cikin manyan matsalolin da sanyin mafitsara ke kawowa musamman Wanda baisamu isasshen kulawaba.
Yana da kyau idan anga wadannan alamomin ayi gaggawar neman magani.
2. Rubewar wani bangare na koda
3.Duwatsun Koda
4.karancin ruwa da jini a jiki
5.Zazzabi mara tafiya
Da zarar kaji alamomin cutar, a tuntubi likita
MAGANI
Maganin sanyin mafitsara a asibiti akeyinsa.likita zaibaka gwaje gwaje Wanda zasu tàimaka wajen magance wannan matsala cikin sauki kamar haka:
1.Gwajin fitsari na mcs
2.Gwajin fitsari na urinalysis
3.FBC
4.E/U/CR
Likita zai Dora ka akan magunguna na tsawon sati biyu.
Shawarwari dazasu tàimaka maka
1. Yawan shan ruwa akalla Lita 2 ko sama da haka arana
2. Yin bawali kafin kwanciya ko da za rar an sadu da iyali
3. Tsaftar muhalli ( musamman bandaki )
4. Ka da mutum ya na rike Kaashi ko fitsari cikin mara, da zarar anji fitsari a je a yi
5.Wanke wajen fitsari kafin wajen Kaashi
Domin gudanar da aikinsa na yau da kullun yadda yakamata,jiki na bukatar wasu sinadarai daga abinci dazaiyi amfani dasu
Alokacin da baya samun wadannan sinadaran yakan fuskanci wasu matsaloli daka iya janyo wata cuta ko ciwo kamar:
1.Rashin girma da saurin tsufa
2.zubar gashi da saurin furfura
3.karancin jini ajiki
4.Raguwar Gani
5.Raguwar kaifin basira
6.Matsaloli na fata
7.Yawan kasala da ciwon jiki da dai sauransu
Abincin dazasu taimaka
Cin abinci kamar wake,waken suya,shinkafa,dankali,doya da dai sauransu,kwai,nama
Kayan Miya kamar timatir,kubewa,kabewa,citta,tafarnuwa,kuka da dai sauransu
Mai kamar man ja,man zaitun, man kwakwa.
Kayan itace kamar lemon tsaki,cocumber,Karas,ayaba,abarba,mangwaro,dabino da dai sauransu.
Wadannan abubuwa duk zaa iya samu cikin sauki
Mene ne basir a likitance? Me ke kawoshi? Mene maganinshi a likitance?
A duniya kusan hudu na mutanen duniya suna fama da wannan cutar.A Nigeria kusan kaso hamsin nayan kasar suna kamuwa da ita aduk shekara,wanda hakan yana karuwa da yawan shekarun mutum.
????Meke kawo basir?
Babu wani taka mai-man abinda yake kawo basir saidai ana alakanta shi da abubuwa kamar:
1.Rashin yin bayan gida ko yawan rike bayan gida.
2.juna biyu.
3.Masu Shekaru sama da 45.
4.Cin abinci mara sinadarin “fibre”
5.Yawan yunkuri
6.Kiba
7.Tiyata a ciki ko dubura
8.Yawan daukan abu mai nauyi.
9.Masu fama da cututtukan huhu
10.Yawan Tari
11.yawan tsayawa a tsaya
12.Yawan zama waje daya
13.Saduwa ta dubura
????Alamomin basir
Mafi shahara daga ciki sun hada da:
1.Zazzagowar dubura.
2.Fitar jini ta dubura.
3.Zafi a dubura.
5.Kai-kayin dubura.
6.rashin samun gamsasshen saduwa.
7.yin kashi mai tauri ko yawan kashi.
8.Yakan fito wajen dubura alokacin dayakai wani mataki
????Maganin basir
Alokacin da kaji wadannan alamomin na basir Yana da kyau dakaje asibiti adubaka.a asibiti akwai bincike da zaayi kamar haka kafin afara magani.
1.hotunan dubura(colonoscopy,proctoscopy).
2.Gwajin swab mcs
3.Gwajin jini(FB)
Magani yadanganta da girman basir din ko matakin sa kamar haka:
✔Akwai basir mara tsiro wanda baya fitowa wajen dubura.
✔Akwai mai tsiro wanda yake fitowa amma yana komawa dakansa basai ammayar dashi ba
✔Akwai wanda inyafito sai an mayar da shi watoh baya komawa da Kansa
✔Akwai Wanda inyafito baya komawa Koda kuwa an mayar da shi
Daga mataki na daya zuwa na uku :
Maganin mataki na daya zuwa na uku sun hada da:
1. magunguna na kwaya:
Ana Shan magunguna irinsu
Daplon
Nitroglycerin
Antibiotics
Maganin kashe zafi(Nsaids)
Maganin saka kashi laushi(laxatives)
2.Shiga ruwan gishiri:
shiga cikin ruwan gishiri na akullun da safe da yamma na tàimakawa kwarai wajen warkar da basir.zaasamu ruwa mai Dan dumi kadan ba sosai ba sai adebo gishiri cikin hannu azuba acikin ruwan dumin sannan arunka shiga ciki.
idan magani na kwaya da shiga ruwan gishi baiyi aiki ba ana iyayin wadannan abubuwa a asibiti:
1.Rubber Band ligation
2.Laser therapy
3.Electrocoagulation therapy
4.Cryosurgery
Ana yin tiyata ne(stepple hemorrhoidectomy) Idan:
1.wadancan abubuwan da muka lissafo basuyiwa mara lafiya amfani ba,ma'ana Basu warkar masa da basir din ba.
2.Idan basir din yakai mataki na hudu(watoh yafito waje Kuma baya komawa)
????Shawarwari
1.Da zarar mutun yaji kashi toh yana da kyau mutun yaje yayishi.rike kashi kan iya janyo wannan cuta ta basir.
2.Yawan cin abinci masu dauke da sinadir 'fiber' kamar alkama,wake,spageti,dankali,biredi,lemon zagi,piya,ayaba,tuffa,karas da sauransu.
3.Yawan shan ruwa akai akai yana taimakawa matuka
4.Rage daukan abubuwa masu nauyi.
5.ziyarar likita akai akai da bin kaidojin da ya gindaya
Cholesterol sinadari ne dake da amfani ajiki,jiki na amfani dashi wajen Samar da sinadarai masu amfani kamar 'vitamins da hormones',yakan zama matsala ne alokacin da yayi yawa acikin jini.
Yawan Cholesterol ajiki nada matukar illa ga lafiyarka Amma amafi lokuta baya nuna wata alama daza agane yawansa ajiki da wuri har saiyakai ga yiwa mutun illa.
Cholesterol na janyo ciwo?
Ciwon hawan jini,ciwon zuciya,ciwon shanyewar barin jiki da wasu cututtuka na magudanar jini.
Abubuwan dake iya nuna yawansa acikin jini zasu iya kasncewa daya daga cikin wadannan:
1.idan kana da kiba sosai sannan kana da ciwon siga,toh akwai yiwuwar kana dauke da cholesterol sosai ajiki.
2.fitowar manyan kurarraji ajiki masu laushi(xanthomas)
3.Rashin haihuwa a Maza
4.Ciwon kirji,wahalar numfashi.
5.Yawan kasala
6.Rashin warkewar ciwo ko gyanbo da wuri
Tambaya 1: ko meke kawo kaikayin tafin hannu?
Tambaya 1: ko meke kawo kaikayin tafin hannu?
Kaikayin tafin hannu alamane na cututtuka kamar na fata da wasu manyan ciwoka irinsu ciwon siga.
Abubuwan da ke iya janyo maka kaikayin tafin hannu sun kunshi:
1.lokacin sanyi
2.Ciwon eczema na hannu
3.Ciwon siga
4.Taba wani Abu mai illa da hanun(kemical,sabulu ko Omo mai karfi,safar asibiti dadai sauransu)
8.Ciwon jijiya
9.Ciwon fata na psoriasis
Amfani da moisturizer akai akai,Saka kankara a hannu lokacin da ya ke kaikayi,amfani da magani na shafawa watoh "topical steroid" duk kan iya taimakawa wajen magance shi.
Mafi muhimmanci dai shine aje asibiti domin likita ya bincike sosai.
Likitan da ya rubuta:Dr Ibrahim (MBBS)
ALAMOMI 7 DAKE NUNAWA KANA DA YAWAN SIGA AJIKINKA.
ALAMOMI 7 DAKE NUNAWA KANA DA YAWAN SIGA AJIKINKA.
Siga sinadari ne da jiki ke bukatar shi wajen gudanar da ayyukansa na yau da kullun.
Amma idan yayi yawa yakan iya Haifar da matsaloli dayawa kamar ciwon siga,hawan jini,ciwon zuciya,Shanyewar barin jiki,Rashin haihuwa,karuwar yawan cholesterol ajiki, da dai sauransu.
Idan har kana Jin wadannan alamomi toh ba makawa jikinka nafama da hauhawar siga.
Alamomin sunkunshi:
✅1.yawan Jin yunwa da karuwar nauyin jiki.
Idan har kana fama da wannan matsala,zakana Jin yunwa akusan Koda yaushe tare da karuwar nauyin jiki da Tara teba mara amfani.
✅2.Yawan kasala da rashin kuzari
Idan har kanajin yawan kasala da rashin kuzari akusan Koda yaushe,toh ka duba cimar ka,aduk lokacin dakake cin abinci masu dauke da sinadarin siga kawai toh bamakawa zaka fuskanci wannan matsala.
✅3.Yawan fitsari
Yawan fitsari nadaga cikin alamomin ciwon siga,mutun zaina fitsari ba dare ba Rana.
✅4.Rashin warkewar ciwo da wuri
Hauhawar siga ajiki na dukufar da aikin garkuwar jiki Wanda hakan zai janyo rashin warkewar ciwo da wuri.
✅5.Kankancewar gaba da rashin gamsar da abokin saduwa.
Kankancewar gaba da rashin Jin dadin saduwa da abokin tarayya nadaga cikin matsalolin da masu ciwon siga ke fuskanta.
✅6.Bushewar fata da fitowar kurarraji
Yaushi,kurarraji,gyanbon fata nadaga cikin alamomin yawan sinadarin siga aciki.
✅7.Rashin daidaiton hawan jini inkana dashi
Idan har kana fama da hawan jini Wanda baya Jin magani,toh kaduba cimarka.
Yawan siga ajiki na Hana hawan jini ya daidaita Koda kuwa mutun na bin ka'ida na Shan magani
MEYAKAMATA KAYI?
Idan kana fama da wannan matsala yakamata kadage kayi wadannan abubuwa:
1.Cin abinci kamar sau uku a Rana.
2.Motsa jiki akai akai akallah na minti 30
akullun Koda yar tafiya ce a kafa.
3.Rage Shan lemon kwalba Dana roba
4.A runka yawan cin kayan itace
Dr Abdulmalik (MBBS)
Faduwar gaba wani irin yanayi ne daxakaji zuciyar ka ta na buguwa da sauri.
Faduwar gaba wani irin yanayi ne daxakaji zuciyar ka ta na buguwa da sauri.
Faduwar gaba alamane na ciwon zuciya da wasu cututtuka da dama,amma amafi lokuta yakanfaru batare da mutun yana dauke da wata cuta ba.
mutane kan shiga cikin zullumi da damuwa alokacin da sukaji gabansu na faduwa sosai,musamman ma idan sukaji zuciyarsu na bugawa da karfi a kirjinsu,makogaronsu ko a wuyansu,amma amafi lokuta wannan ba matsala bane Kuma yakan tafi dakansa batare da mutun yasha wani maganiba.
Yana da kyau musani ba akodayaushe yake zama matsala ba.
Meke kawo yawan bugun zuciya?
Zaka/ki iya fuskantar wannan matsala ta faduwar gaba idan kana/kina da daya daga cikin wadannan abubuwan da zamu zayyano su akasa:
1.yawan tara gajiya
2.yawan shan Kofi(nescafe),giya ko cin goro
3.yawan yin aiki batare da samun isasshen hutu ba
4.Fama da cututtukan zuciya(bayan faduwar gaba mutun kan fuskanci kumburin kafa,Haki,yawan kasala,rashin San cin abinci da sauransu in har Yana da ciwon zuciya)
5.Macen dake dauke da ciki,ko take jinin al'ada ko lokacin da ta daina jinin al'ada na manyanta(menapause)
6.Karancin jini,ruwa ko siga ajiki.
7.karancin sinadarai masu gina jiki.
8.Fama da ciwon fargaba na kwakwalwa(anxiety disorder)
9.Shan magungunan gargajiya
10.Ciwon thyroid
Likitan da ya rubuta:Dr Abdullahi(MBBS)
Irin ciwon jikin da be kamata ayi wasa dasu ba
IRIN CIWON JIKIN DA BAI KAMATA KAYI WASA DASU BA
Ciwon jiki alamane na ciwuka da yawa,wani sa'in ma har cututtukan da za su iya yin ajalin mutun in ba a dau kwakkwaran mataki da wuri ba.
Ire Iren wadannan ciwukan jikin da Bai kamata kayi wasa da su ba sun kunshi:
✅1.Ciwon kirji mai yawo.
Irin wannan ciwon kirjin alamane na cututtuka na zuciya masu hatsari (kamar su ischemic heart diseases).
Alokacin da kaji kamar ana matse maka kirji ko kamar an Dora maka Abu mai nauyi akan kirjin,sannan bai tsaya iya Nan ba,Yana zuwa har gefen kafadunka da wuya,toh kayi kokarin daukan kwakkwaran mataki akanshi ta hanyar ziyartar likita,likitan ma kwararre.
✅2.Ciwon Kai mai farawa lokaci daya.
Alokacin da kaji kafara ciwon Kai lokaci guda mai matsanancin ciwo da radadi toh kasan cewa wannan alamane dake nuni da fashewar magudanar jini acikin kanka.
Rashin daukan mataki da wuri zai iya sa Taruwar jini acikin kwakwalwa da mutuwa lokaci daya.
✅3.Ciwon hakori.
Alokacin dakake fama da matsanan cin ciwon hakori,Yana da kyau da kaje kaga likitan hakori watoh"dentist" a asibiti domin Neman magani.wasa da irin wannan ciwo ka iya sa ka kamu da ciwon zuciya agaba.
✅4.Mata masu Jin zafi ko ciwo lokacin saduwa.
Wannan alamane na Kansar bakin mahaifa
Musamman inkina fitar da jini bayan saduwar.
✅5.Azababban Ciwon ciki a dan kankanin lokaci.
Wannan alamane na cututtuka masu hadari kamar fashewar hanji,Duwatsun Koda,fashewar appendix,fashewar mahaifa da dai sauransu.rashin daukar mataki da wuri zai iya sa mutun ya rasa rayuwarsa.
✅6.Ciwon kafafu.
Ciwon kafafu musamman tare da kumburi alamane na cutar magudanar jini watoh"DVT" wannan ciwo na da matukar hatsari.
Alokacin dakake fama da ciwon kafa bayan kayi doguwar tafiya,ko bayan anyi maka tiyata,ko bayan kayi doguwar jinya,sannan a mata Kuma inkina Shan maganin tsarin iyali toh afara tunanin wannan ciwo.
Alamomin ciwon zuciya
ALAMOMIN CIWON ZUCIYA
Ciwon zuciya ciwone Wanda kesa zuciya ta kumbura takasa aikin datasaba na tura jini zuwa sassa daban daban na jiki.
Alokacin da mutun yakamu da ciwon zuciya,zai runka Jin wadannan alamomin kamar haka:
1.Hakin dare
2.Hakin rigingine
3.kumburin kafofi biyu
4.yawan kasala
5.Tari
6.ciwon kirji
7.faduwar gaba
Shin kana fama da daya daga cikin wadannan?
Alamomin cututtika na mafitsara
ALAMOMIN CUTUTTUKA NA MAFITSARA
3.ZAFIN FITSARI
Zafin fitsari ko Jin ciwo lokacin yin fitsari alamace dake nuni da cututtuka dayawa musamman ma na mafitsara,mahaifa(a mata) da Koda.
Meke kawoshi
1.Sanyin mafitsara
sanyin mafitsara sanyi ne dake shafar mafitsararka,idan kana dashi,toh zaka runka yawan fita fitsari akoda yaushe musamman da daddare(sau biyu zuwa uku).alamominsa sun hada da:
Yawan fitsari
Tashi da daddare yin fitsari(tashi cikin dare sama da sau biyu)
Jin zafi lokacin yin fitsari
Ganin jini acikin fitsari
Ciwon gefen ciki bayan ciwon mara
mutun na kamuwa da sanyin mafitsara alokacin da aka samu kumburi ko kwayar cuta tashiga cikin mafitsara.
mata sunfi saurin kamuwa da wannan ciwo akan maza.
Hakazalika masu ciki da Wanda al'adar su ta dauke suna da saurin yiwuwar kamuwa da wannan ciwo
2.Sanyin da ake dauka ta hanyar saduwa:
Zaka iya Jin zafi alokacin dakake fitsari idan kana da sanyi wanda ake dauka ta hanyar saduwa.
Daga cikin sanyin da ake dauka ta hanyar saduwa dake kawo zafin fitsari sunkunshi herpes, gonorrhea, da Chlamydia.
Alamomin sa sune:
Jin zafi lokacin saduwa musamman amata
Fitar ruwa ta gaba
Yawan fitsari
Ganin jini acikin fitsari
Kurajen gaba
3.Sanyin prostrate(Prostatitis):
Daga cikin cututtukan dake kawo zafin fitsari akwai prostititis, wato kumburin prostrate,ana samun prostrate ne a maza kadai.Amfanin 'prostate' ajiki shine karawa "sperm cells(maniyyi)" sinadaran dasuke bukata,wanda rashin hakan kan iya janyo "Rashin haihuwa a maza".
Alamomin sa sune:
Fitsarin jini
Ganin jini a cikin maniyyi na maza
Jin zafi lokacin saduwa a Maza
4.Sanyin mara(cystitis):
Cikin abubuwan dake kawo zafin fitsari shine kumburin mara(bladder).
Alamomin kumburi ko sanyin mara sun kunshi :
yawan fita fitsari
ciwon mara musamman idan antaba marar da hannu.
Mutun na kamuwa da wannan ciwon ne alokacin da Kwayar cuta tashiga cikin mara.
5.Sanyin tantanin mafitsara(Urethritis):
urethritis yana nufin sanyi ko kumburin makwaroron fitsari, urethritis na janyo zafin fitsari da yawan Jin San fita yin fitsari.
Mutun na kamuwa da wannan sanyin ne alokacin da Kwayar cuta tashiga cikin tantanin mafitsara
6.Sanyin Epididymis:
Jin zafi lokacin fitsari zai iya kasancewa sabida wannan ciwo, wanda sanyi ne dake shafar mazaunin "sperm cells(maniyyi) acikin marena(epididymitis) yake kawoshi.
Alamomin sa sune:
Ciwon marena
Jin zafi lokacin saduwa a maza
7.Sanyin mahaifa:
sanyin mahaifa watoh "pid" na shafar duk wani bangare na mahaifa tundaga kan bakin mahaifa,cikin mahaifa,hannun mahaifa da Kwan mahaifa.
Alamominsa sunkunshi:
ciwon mara
Kaikayin gaba
Fitar da ruwa ta gaba
jin zafi lokacin saduwa
zafin fitsari
8.Toshewar mafitsara (Obstructive uropathy):
Wannan ciwo ne da yake faruwa alokacin da aka samu wani abu ya toshe magudanar fitsari acikin mafitsara . abubuwan dake kawo wannan matsala suna da yawa.
Alamomin sa sunkunshi:
Rashin iya yin fitsari
Yawan fita fitsari
Rashin iya rike fitsari
Kumburin kafa da fuska
9.Duwatsun koda:
Mutun kan iya fuskantar wahalar yin fitsari idan yana da duwatsun koda.duwatsun Koda wadansu duwatsu ne dake fitowa a Koda daga daskarewar datti da gishiri dake cikin Koda.
Alamomin sa sun kunshi:
Yawan fitsari
Azababban ciwon mara
Ciwo a gefen mara Wanda yake zuwa har cinya
Rashin iyayin fitsari
10.Magunguna:
Shan Magunguna kamar su estrogen, magungunan ciwon damuwa, magunguna na ciwon jiki da dai sauransu kan iya janyo zafin fitsari.
YAUSHE YAKAMATA KAGA LIKITA?
1.idan zafin fitsarin yaki tafiya
2.idan mace nadauke da juna biyu
3.Idan zafin fitsarin yazo tare da zazzabi
4.Idan yazo tare da fitar ruwa daga al'aura
5.Idan fitsarin ya canza kala ya koma ja ko baki ko Kuma fitsarin na wari.
6.Idan zafin fitsarin yazo tare da ciwon ciki
7.Idan dawatsu sun fito acikin fitsarin
MAGANIN ZAFIN FITSARI
Abu mafi muhimmanci shine afara sanin me ke kawomaka wannan matsala,idan har angano inda matslar take toh komai zaizo da sauki.
Za a iya baka wadannan gwaje gwajen a asibiti domin gano meke kawo wannan matsala kamar haka:
1.Test din fitsari
2.Test din jini
3.Hoton mafitsara da hoton mara
4.Test din Koda
Likita zai iya baka "magungunan sanyi"(antibiotics) sabida sanyi,sannan zai iya baka magunguna daza su rage maka radadin ciwon mara.
SHAWARWARI
1 Yawan Shan ruwa na tàimakawa kwarai wajen rage zafin.
2.Rage cin abinci masu tsami sosai,Kofi da barasa
3.Amfani da matakan kariya kamar "condom" lokacin saduwa
4.Rage amfani da sabulu,Omo ko man shafawa masu kamshi sosai .
YAWAN FAMA DA CIWON KAI
Shin kana yawan fama da ciwon Kai na tsawon lokaci mai tafiya ya dawo? Karanta domin sanin wane irin ciwon Kai kake fama dashi
1.Ciwon Kai na tension
Alokacin dakake fama da ciwon Kai na tension,zakaji gabadaya kan naka na ciwo.sannan idan yafara baya lafawa,zaka runka ji kamar ana matse maka Kai.
Amfi ganinsa a mutanen dake Tara gajiya da damuwa ajikinsu.
Ciwon nakaruwa ne ahankali ahankali alokacin dayafara,sannan motsa idanu wa kan ta'azzarashi ma'ana alokacin dakake motsi da idanuwanka ciwon kan nakara tsanani.
2.Ciwon Kai na migraine
Wannan ciwon kan ana jinsa ne a bangare daya na Kai amafi yawancin lokuta,zaka runkaji kamar ana buga maka karrarrawa akai,ko kaji kan na bugawa dakarfi.
Yakanzo da amai.sannan zakaji baka kaunar haske ko zama a inda haske yake.
Alokacin da ciwon kan zaizo maka zakaji canjin yanayi mara dadi.
3.Ciwon Kai na cluster
Wannan ciwon kan yakanzo yatafi,sannan yafi zuwa da daddare tare da ciwon ido na satuttuka da toshewar hanci a bangaren da yake ciwon.
4.Ciwon Kai na cervical root
Idan kana fama da irin wannan ciwon kan,zakanajinsa ne a bayan kanka ko a tsakiyar Kai da gaban goshi.
Yana Kara tsananta ne alokacin da ka motsa wuyanka.
5.Gajiyar ido
Wannan ciwon kan na zuwa ne alokacin da kake karanta wani Abu a littafi,waya ko komfuta,sannan zaka runka Gani dishi dishi.
Ana maganinsa ne alokacin da aka baka tabarau nasakawa.
6.Magunguna
Shan magunguna kowanne iri ne kan iyasa ka ciwon kai.sannan ciwon na tafiyane alokacin daka dakatar da maganin dake kawo maka ciwon kan.
Magani
Magani a asibiti ake badashi musamman irin wannan ciwon kan wanda yake tafiya ya dawo.
Dan haka idan kana fama da irin wannan ciwon kan toh kaje asibiti kaga likita
KUMBURIN MAHAIFAH MAI SAH ZUBAR DA JINI
KUMBURIN MAHAIFA MAI SANYA ZUBAR JINI (ENDOMETRITIS)
Endometritis kumburin bangon mahaifa ne (endometrium) wanda yake haddasa zubar jini daga gaban mace.
Zai iya kasancewa mai tsanani amma baya daukar dogon lokaci (acute). Hakanan zai iya zamowa mai tsanani kuma mai daukar dogon lokaci (chronic).
Mafi yawanci kwayoyin cutar bacteria ne suke kawo shi, musamman wadanda suke kama al'aurar mace bayan ta haihu, ko kuma a lokacin da ake yi mata aikin tiyata a mahaifa ko mara. Bincike ya tabbatar da cewa manyan dalilai masu kawo endometritis sune:
Haihuwa (childbirth): idan kwayoyin cutar bacteria suka shiga cikin mahaifa a lokacin da mace take yin nakudar haihuwa, to, zasu iya haddasa mata matsalar endometritis, musamman idan tayi diguwar nakuda (prolonged labour), ko yagewar jakar ruwan mahaifa (amniotic sac rapture), ko yawan duba mata budewar farjinta (multiple vaginal examination - VE).
Aikin tiyatar cire jariri (caesarian section - CS): macen da akayiwa tiyatar CS sunfi kowa hatsarin kamuwa da endometritis, duk da kasancewar kayan aikin da kuma dakin tiyatar masu matukar tsabta ne. Hakan yana da nasaba da tsanin yawa, naci, da kankantar bacteria din ne.
Ayyukan tiyatar da suka shafi farji da marar mace (gynaecological procedures): wadannan sun kunshi wankin ciki (dilation and evacuation), aikin duba mahaifa (hysteroscopy), daukar wani abu daga cikin mahaifa domin yin awon wata cuta (endometrial biopsy). Kwayoyin cutar bacteria zasu iya shigar mahaifa a lokacin wadannan ayyukan.
Cututtukan da ake dauka a wajen jima'i (sexually transmitted diseases - STDs): wadannan sun kunshi chlamydia, gonorrhea, staphylococcus, da sauransu. Duk suna iya haifar da endometritis idan suka shiga mahaifa.
ALAMUNSA (SYMPTOMS)
Alamun endometritis sune:
Zubar ruwan da mace bata saba gani ba daga gabanta (abnormal vaginal discharge): ruwan zai iya kasancewa mai wari ko karni, sa'annan mai launin ruwan kwai (yellowish) ko ruwan ganye (greenish).
Ciwon mara (pelvic pain): mace mai matsalar endometritis zata rika fuskantar ciwon mara mai tsanani, kodai mai dadewa bai bari ba ko kuma mai zuwa ya tafi.
Zazzabi da jin sanyi (fever and chills): shima zai iya zamowa mai tsanani, sa'annan mai zuwa ya tafi ko mai dadewa.
Jin zafin fitsari ko yawan yin fitsari (dysuria or polyuria): shima zai iya zama mai zuwa ya tafi ko mai dadewa.
Zubar jini mai yawa lokacin al'ada ko rashin tsayayyar al'ada (heavy or irregular menstrual bleeding): shima zai iya zama mai zuwa ya tafi ko kuma mai dadewa.
TASIRINSA A JIKIN MACE (EFFECTS)
Idan ba'a magance endometritis ba, zai iya haifar da:
Rashin haihuwa (infertility): hakan zai faru ne sakamakon raunana da kuma lalata halittun mara na haihuwa.
Taruwar ruwan gunya a cikin mara (pelvic absess): zai iya haifar da gyambo mai tara ruwan gunya a cikin mahaifa. 3. Kumburin dukkan jiki (sepsis): hakan zai iya faruwa ne sakamakon yaduwar kwayoyin cuta a dukkan sassan jiki ta hanyar jijiyoyin jini.
HANYOYIN RIGAKAFI (PREVENTION)
Za'a iya rigakafin kamuwa da endometritis ta hanyar:
Inganta tsabta a lokacin karbar haihuwa, da lokacin yin tiyatar mahaifa a marar mace, domin kaucewa yaduwar kwayoyin cuta
Tsabtace kayan ayyukan tiyata yadda ya kamata. 3. Tabbatar da cewa ma'aurata basu dauke da cututtukan da ake dauka a wajen jima'i.
MAGANI (TREATMENT)
Hanyar magance endometritis ita ce zuwa asibiti domin likita ya yayi aune-aune kuma ya doraki mace akan maganin antibiotics da ya dace. Idan abin ya ta'azzara, to, sai an kwantar da ita. ✍✍️✍️ By Dr MAKINU LABARAN ALIYU